✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rage yawan ’yan majalisa maimakon jam’iyyu – Maizabura

Shugaban Jam’iyyar NDLP, ta Kasa Alhaji Umar Muhammad Maizabura ya ce yawan wakilan  Majalisar Dokoki ta Kasa ya kamata a rage maimamon yawan jam’iyyun siyasa,…

Shugaban Jam’iyyar NDLP, ta Kasa Alhaji Umar Muhammad Maizabura ya ce yawan wakilan  Majalisar Dokoki ta Kasa ya kamata a rage maimamon yawan jam’iyyun siyasa, inda ya ce hakan zai tabbatar da habaka da ingantuwar tattalin arziki, ta yadda zai iya kaiwa ga talaka kai-tsaye.

Alhaji Umar Muhammad Maizabura, ya ce “Babu shakka idan aka yi la’akari da yawan ’yan Majalisar Wakilai sama da 300 da na Majalisar Dattawa109 da kowanensu ake biyansa albashi da alawus-alawus da wasu kudade masu yawa, tare da saya musu motocin alfarma, a daidai lokacin da talakawa ke kwana da yunwa ko kwana a waje, akwai bukatar a duba wannan lamarin ta hanyar rage yawan  ’yan majalisar ta yadda kowace jiha ta samu sanata daya.”

Ya ce “Su ma ’yan Majalisar Wakilai su zama daidai a kowace jiha don a rage kashe kudade, a samu zarafin da za a yi wa talakawa aiki a samar musu da ingantattun hanyoyi da magunguna a asibitoci da ingantaccen ruwan sha da wutar lantarki da inganta noma da ilimi da bunkasa kananan masana’antu ta yadda za a samar wa matasa aikin yi. To amma a ce kowane dan majalisa yana daukar albashi da alawus-alawus sama da Naira miliyan goma sha a kowane wata wannan bai dace ba.”

Ya ce “Da a rage yawan jam’iyyun siyasa da wadansu ke magana gara a rage yawan ’yan majalisa don yawan jam’iyyun ba ya da alaka da tattalin arzikin kasa. Domin ka ga ba wani mai ba mu albashi muna yi ne kawai don ra’ayin kanmu ba don a ba mu wani abu ba. Amma ’yan majalisar nan su ne masu kwashe kudin kasar nan ba gaira ba wani dalili, kuma zai iya kasancewa wani dan majalisar ba zai taba iya gbatar da wani kudiri don ci gaban al’ummar yankinsa ba har ya sauka, illa kawai yana cin kudi ne kawai,” inji shi.