Search
Subscribe
A rayuwa: Shiga harkar da babu ruwanka kuskure ne 01

A rayuwa: Shiga harkar da babu ruwanka kuskure ne 01

Ma’abuta karanta shafin Sinadarin Rayuwa, ina yi muku sallama, Assalamu alaikum! Bayan haka, yau kuma da ikon Allah, za mu yi wa kanmu tambihi ne game da wani muhimmin al’amari da muke sanya kawunanmu a cikinsa, ba tare da sanin dinbin asarar da muke tafkawa ba daga yin haka.
Mafi yawan lokuta, mukan kara wa kawunanmu damuwa, musamman wajen tsoma kanmu cikin harkokin da ba namu ba, ko kuma ba su shafe mu ba. Yin haka lallai ba karamar matsala ba ce, kuma ba ta dace da rayuwarmu ba, kuma hakan ba zai taimake mu ba ta kowane hali. Babban alheri ne, ka kauce wa duk wani abu da bai shafe ka ba, kada ka sake ka tsoma kanka cikin wani sha’ani, muddin dai bai shafe ka ba, ko kuma ba a gayyace ka cikinsa ba.
Muna tsoma kanmu cikin abubuwan da ba su shafe mu ba ne saboda wasu dalilai, saboda muna jin cewa lallai a tunaninmu, ba haka ya kamata a gudanar da wannan al’amari ba. Muna jin cewa tunaninmu shi kadai ne tunani mai kyau, hikimarmu ita kadai ce hikima; don haka duk wanda ya aikata wani abu sabanin tunaninmu, sai mu dauka cewa bai yi daidai ba, ko kuma ba zai samu nasara ba. Dalili ke nan ya sanya muke bata lokacinmu wajen kushewa da yin Allah-wadai da wani abu da wasu suka aikata.
Wannan kam yana da babbar illa, domin kuwa muna yin adawa ke nan da tsarin halittar Allah, inda Ya halitta mutane daban-daban, masu tunani da hikimomi daban-daban. Wanda akwai alheri mai yawa cikin bambance-bambancenmu. Yadda Allah Ya halicci mabambantan mutane kuma Ya halitta hikimomi da dabaru iri-iri, wadanda suka sha bamban da na juna, lallai akwai alheri cikin haka.
A lokacin da muka takarkare muna kallon yadda wane ko wance ke gudanar da al’amuransa ko al’amuranta, a lokacin da muka tsaya muna bata lokaci muna kushewa da soka zantuka cikin abin da suke aikatawa, to kuma a lokacin nan muka yi wa kanmu illa, muka hana kanmu aikata wani abin kirki a daidai lokacin. Ke nan mun yi asara goma da goma ke nan. Na farko dai, mun bata lokacinmu. Na biyu kuma mun haramta wa kanmu aikata wani alheri, sannan kuma mun zargi wani kan abin da bai shafe mu ba.
A kowane lokaci, mu ba da himma kan al’amuran da suka dame mu. Kullum muka wayi gari, mu yi nazarai kan wani muhimin abu da ya faru, ko kuma muka ga wani ko wata na aikatawa. Maimakon mu saka kanmu cikinsa, mu yi bincike domin gano fa’ida da muhimmancin abin. Idan za mu iya tsintar wani alfanu ko abin alheri daga gare shi, sai mu dauka mu yi amfani da shi. Idan kuwa muka ga cewa babu amfani cikinsa, sai mu koma kan wani al’amarin mai amfani.
Masu hikimar magana ma sun ce, sa ido sana’ar banza ce, domin ba za ta haifar da alheri ba. Don haka, idan an neme ka shiga cikin wani sha’ani, ka amsa kira cikin al’amrin, tare da aiwatar da iya kokarinka da hikimarka. Amma kada ka kuskura ka yi abin da Hausawa ke kira shiga sharo ba shanu, domin kuwa duk mutumin da ke shiga cikin gayyar sodi, to kuwa ba shi ba muhibba. Ba zai samu nasarar al’amuransa ba, domin kuwa an ce duk wanda ya taka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.
Babban darasin maudu’inmu na yau shi ne, mu maida hankali kan al’amuran da suka shafe mu. Mu kauda kai daga shiga harkar da ba ta shafe mu ba. Ke nan, kada mu rika yin shigar-shugula, watau shiga harkar gayyar sodi, harkar da ba a neme mu da shiga cikinta ba. Mu maida hankali kawai kan al’amuran da suka shafe mu, wadanda za mu iya yin amfani da kwakwalwarmu da karfinmu wajen aiwatarwa. Wannan ne zai taimaka mana, sannan kuma ya taimaka wa na kusa da mu.
Ya kamata mu gane cewa, ita rayuwar nan wata irin shu’uma ce, ba za ka iya taba kure ta ba, sai dai ta kure ka. Ba za ka iya yin komai da komai ba. Don haka, ka dauki abin da kawai za ka iya, wanda ya dace da kai, ya dace da al’ummarka kuma ya dace da kokarinka da tunaninka. Madamar kuwa ka ce sai ka shiga cikin kowane al’amuri, to za ka yi abin da masu hikimar magana ke cewa biyu babu. Domin kuwa za ka rasa wannan sannan ka rasa wancan. Har kullum dai, ka tsaya matsayinka, kada zancen ’yan duniya ya rude ka.
Kada mu manta da darasinmu: Kar ka shiga sha’anin da bai shafe ka ba. Hanyar lafiya, sai a bi ta da shekara! Sai kuma mako na gaba, in Allah Ya kai mu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin