Da Dumi Dumi

A rika daukar tsattsauran mataki kan masu yin fyade – Hajiya Hauwa’u Abubakar

Hajiya Hauwa’u Abubakar ita ce Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Walwala da Jin Dadin Jama’a ta Jihar Sakkwato
Hajiya Hauwa’u Abubakar ita ce Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Walwala da Jin Dadin Jama’a ta Jihar Sakkwato

Hajiya Hauwa’u Abubakar ita ce Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Walwala da Jin Dadin Jama’a ta Jihar Sakkwato. A zantawarta da Aminiya ta yi bayani kan rayuwarta inda ta bukaci a rika daukar tsattsauran mataki kan masu yin fyade:

Tarihina

Sunana Hajiya Hauwa’u Abubakar Muhammad Sakkwato, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Walwala da  Jin DadinJama’a a ta Jihar Sakkwato.  An haife ni a garin Sakkwato a 1963 na yi karatun firamare a Makarantar Tunawa da Turaki  daga nan na wuce Sakandaren Gwamnati (GSS) ta Kwatarkwashi wadda ake kira Unity a yanzu. Can na yi shekara biyar. Bayan na gama na shiga Kwalejin Ilimi ta Sakkwato(COE) na karanta fannin tattalin gida(Home Economics) da na kare sai na tafi   Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na yi digiri cikin shekara hudu, bayan na dawo  na  yi aikin yi wa kasa hidima.

A lokuta daban-daban na yi  karantarwa a makarantu irin su Makarantar Mata ta Nana da kuma ta Arkilla daga baya na sake komawa Jami’ar Ahmadu Bello na yi digiri na biyu a fannin tsara harkokin gudanarwa da na dawo  na zama Shugabar Makarantar Mata ta Rabah daga baya na dawo Kwalejin ’Yan Mata (GGC) daga nan na koma  Makarantar Hafsatu Ahmadu Bello a nan na yi shekara takwas. Ina makarantar ce a lokacin gwamnatin Bafarawa aka yi min Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Al’amuran Mata da Yara, inda na yi shekara hudu.

Lokacin gwamnatin Sanata Wamakko aka dakatar da ni. Da gwamnatin Tambuwal ta zo aka mayar da ni  Shugabar Makarantar Mata ta Bodinga, daga baya aka yi min Babbar Darakta a Bangaren Yawon Shakatawa, yanzu kuma gwamnatin Tambuwal ta mayar da ni Babbar Sakatariyar a Ma’aikatar Walwala da  Jin Dadin Jama’a.

ADVERTISEMENT

Kalubale

Sai dai mu yi wa Allah godiya cikin jin dadi da walwala, abin da ba zan manta ba  dakatar da ni da aka yi na samu damuwa. Mutanen da na yi aiki da su a lokacin sun taimaka min. Amma yanzu abin ya wuce ya zama tarihi. Yanzu dai abubuwa suna tafiya yadda suka kamata a rayuwa, ban da wannan ba ni da wani babban kalubale da zan ce ya yi tarnaki ga sha’anin rayuwata.

Burina

Babban burina a yanzu shi ne in ga na tallafa wa jama’a wadanda ke cikin wani hali har su kai ga nasara. Ina da burin in ga na zama abar koyi ga yara mata da matasa. Haka kuma ina jin dadi yadda na ga wadanda na tarbiyyatar suna zama mutanen da ake alfahari  da su cikin al’umma don haka na cika burina.

Burina a kuruciya

Sai godiyar Allah burin kuruciya ne ya sanya ni cikin wannan fanni.

  Daga hagu Hajiya Hauwa tare dawata  abokiyar aikinta
Daga hagu Hajiya Hauwa tare dawata abokiyar aikinta

Abin da nake son a tuna ni da shi

Bayan ba raina ina son a tuna da ni a matsayin mai son zaman lafiya da kyakkyawar hulda,  ba na mugun nufi ga dan Adam kullum fatata al’amari ya tafi daidai a rayuwa. Hakan zai sanya rayuwa ta yi dadi, don haka in ka yi abu mai kyau kowane lokaci za ka iya samun sakamakon mai kyau.

Wadda nake koyi da ita

Ina koyi da Hajiya Kulu Haruna Kwamishinan Ma’aikatar Kimiyya da Kere-

Kere ta Jihar Sakkwato da Farfesa A’isha Madawaki Kwamishinar Ma’aikatar Walwala da Jin Dadin Jama’a ta Jihar Sakkwato. Tare muka yi ’yan matanci, tana gabana da shekara biyu a makaratarmu ta Kwatarkwashi. Mafi yawan lokaci ina wurinta in ba barci zan yi ba. Duk mai nemana wajenta yake zuwa, abubuwanmu na rayuwa sun zo daya, su ne nake koyi da su.

Iyali

Na yi aure da mijina marigayi Alhaji Abubakar Sakkwato, Allah Ya gafarta masa. Ina da ’ya’ya uku da shi,  Maryam da Sadik da Ahmad.

Tarbiyyar mata matasa

Gaskiya akwai kalubale ba za ka kwatanta inda aka fito ba, akwai miskila yadda muka samu kanmu cikin al’ummar da ta gurbace.  Wasu ta abokai ne wasu kuma rashin sanya idon iyaye ne. Ya kamata iyaye su sanya ido ga abokan ’ya’yansu da yadda abubuwa ke tafiya musamman mata.

Shawara ga mata

Mata su sani lokacin ya yi da za su tashi tsaye su daina jiran abu ya zo musu a banza. Su yi sana’a ba komai ne za ki jira maigidanki ba. Ina kira ga mata mu tashi don dogaro da kanmu.

Shawara ga masu karatu da aure

Ana iya hada karatu da aure. Ni misali ce, kusan duk karatuna da aure na yi shi. Aure bai hana ni komai na rayuwata ba, in kin kasa lokacinki yadda ya kamata ba za ki samun cikas ba.

Abin da za a yi a rage fyade ga mata

A rika sanya hukunci mai tsanani kamar  harbe mutum, duk wanda ya ji wannan zai shiga taitayinsa in yana da niyya ya fasa don wannan abin ya munana cikin al’umma. Kuma a kullum kara yaduwa yake, dole sai an dauki mataki da zai sanya a daina.  Iyaye su rika sanya ido da barin fita cikin tsiraici da inda suke kai- kawo.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya