✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rika kulawa da kayan gwamnati

Duk kan dan kasa nagari yakan yi wa kasarsa fatar alheri da kuma fatar ganin tana ci gaba a fannoni daban-daban. Irin wadannan ’yan kasar…

Duk kan dan kasa nagari yakan yi wa kasarsa fatar alheri da kuma fatar ganin tana ci gaba a fannoni daban-daban. Irin wadannan ’yan kasar nagari ne suke sadaukar da rayuwarsu haikan wajen bauta wa kasar ta hanyoyi iri-iri. Kuma lura da cewa ba su da wata kasa da ta fi tasu ne ya sa suke maida hankalinsu wajen kula da duk wasu kaya na gwamnati duk da wasunsu ba ma ma’aikatan gwamnatin ba ne. Ba sa lalata kayan gwamnatin kuma ba sa barin wani ko wadansu su bata su. Domin sun san kayan gwamnati  nasu ne tunda jama’a ce gwamnatin ce kuma jama’ar na gwamnati ne. ’Yan kasa da ba nagari
ba, sukan dukufa ne wajen lalata kayan gwamnatin domin su a nasu gajeren tunanin ai kayan gwamnati ba na su ba ne. Saboda haka bari kawai su lalata su domin su yi wa gwamnatin asara a nasu tunanin wanda ni kuma ina hangen ’yan kasa ne suka yi wa asara kuma su ma suna daga cikin ’yan kasar. Wurare da dama gwamnati takan samar da wasu abubuwan inganta rayuwar jama’a, walau gine-gine ko hanyoyi ko wasu muhimman abubuwa domin amfani jama’a, amma sai wadansu batagari su rika wulakanta su suna lalata su. Kuma idan har suka lalata su to gwamnati za ta yi amfani da dukiyar kasa wadda ta ’yan kasa ne wajen gyara abubuwan da suka bata din. Su sake batawa kuma gwamnati ta sake dibar dukiyar kasar ta gyara, ke nan an yi ba a yi ba.
Domin da a ce suna kula da abubuwan da gwamnatin ta samar, sai ta yi amfani da waccan dukiya wajen kara samar da wasu abubuwan da za su taimaki jama’a. Ba ta tsaya a wuri daya ba kullum tana gyara abubuwan da batagari suka barnatar ba.
Da fatan masu aikata irin hakan za su sake tunani su gane cewa dukiyarsu ce suke wulakantarwa.Kuma idan har za su ci gaba da haka, to babu ranar da za su ci gaba. Kuma hakan ba zai taba haifar musu da da mai ido ba!
Don haka ya kamata ’yan kasa nagari su tashi haikan wajen hana batagari lalata kayan gwamnati da suke kusa da su, idan kuma masu barnar sun fi karfinsu, to sai su gaggauta sanar da jami’an tsaro mafiya kusa da su, domin daukar mataki a kansu. Haka ita ma gwamnati ya kamata ta rika yin hukunci mai tsauri ga duk wanda aka samu ya wulakanta kayan gwamnati, domin hukuncin ya zama darasi ga wasu da ke
da niyyar bata kayan gwamnati.
Babu wanda ya gagari gwamnati ta hukunta shi, don haka bai kamata gwamnati ta zura ido wani ko
wadansu batagari su rika barnata kayan gwamnati ta kyale su ba! Domin zura musu ido zai sa su ga kamar sun fi karfin gwamnati ne. Haka kuma wadansu ma su ce tunda wadancan masu bata kayan gwamnati sun gagari gwamnati, to su ma bari su tsunduma a ciki.
Mu ci gaba da zama ’yankasa nagari, domin ci gaban kanmu da kasarmu baki daya.
Haruna Muhammad Katsina
Shugaban kungiyar Muryar Jama’a, Reshen Jihar Katsina.
07039205659,  07057491050.