✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rika yi wa gwamnoni da sarakuna gwajin miyagun kwayoyi – Sarki Sanusi

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya bukaci a samar da wata doka da za ta tilasta sarakuna da gwamnoni da sauran masu…

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya bukaci a samar da wata doka da za ta tilasta sarakuna da gwamnoni da sauran masu rike da mukaman siyasa su rika gwajin miyagun kwayoyi.

Sarki Muhammadu Sanusi ya yi wannan kira ne a lokacin bude taron wuni biyu da Majalisar Dattawa ta shirya a birnin Kano kan yadda za a magance matsalar shan miyagun kwayoyi da ke addabar al’umma  a ranar Litinin da ta gabata. 

Sarkin ya ce a shirye yake a yi masa gwajin miyagun kwayoyi a yunkurin da yake yi na ganin an magance matsalar.

Ya ce, “Idan muka fara nuna wannan misali, matasa ’yan baya za su fahimci cewa idan suka yi tu’ammali da miyagun kwayoyi, babu shakka za su takaita damarsu ta zamowa shugabanni. Bai kamata ’yan sanda da sojoji da sauran masu sanya kayan sarki maza da mata su rika shan miyagun kwayoyi ba.” 

Sarkin ya nuna damuwa kan yadda kasar nan take fuskantar babban hadari, inda ya ce, karuwar tu’ammali da miyagun kwayoyi wata alama ce ta gazawa daga bangaren gwamnoninmu.

A cewarsa, matsalar shan miyagun kwayoyi ta shafi kusan dukkan iyali a Arewa. “Gaskiyar lamari shi ne yawancin ’ya’yan masu hali da ke tu’ammali da miyagun kwayoyi sun tashi ne sun gani a gidajensu,” in ji Sarkin na Kano.

Mai martaba Sarki Sanusi II ya yi kira ga mahukunta su dauki matakin gaggawa domin shawo kan matsalar. Ya ce rashin aiwatar da dokokin da aka yi ne ya sa matsalar ke ta’azzara.

Sarki Sanusi ya soki ’yan siyasar kasar nan da cewa suna bai wa matasa kayan maye domin su kare bukatunsu. Ya ce, “Muna yaudarar kanmu ne idan ba mu amince cewa mu ma bangare ne na matsalar ba maganinta ba. Idan babban dan siyasa, misali Gwamna ko Sanata, wanda ke da damar samun ’yan sanda da SSS da za su rika kare shi zai gwammace ’yan bangar siyasa da suke shaye-shaye su kare shi, to me wannan ke nunawa? Mutum nawa kuka sani a tsakanin abokan aikinku da ke biyan ’yan banga albashi, wadanda kuma ke sayen miyagun kwayoyi suna ba su domin su kare su ko su kai hari kan abokan hamayyarsu? Muna ganin gwamnoni suna wucewa da tawagarsu cike da ’yan bangar siyasa da suka yi mankas da kwaya ga makamai a hannunsu, kuma a hakan ne za ku ce kuna yaki da miyagun kwayoyi, to me kuka yaka?”

Ya kawo shawarar cewa yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi ya zamo a sahun gaba na ayyukan da gwamnatin ta sanya a gaba. Ya ce: “Babbar matsalarmu ita ce rashin aiwatar da dokokin da muke da su kana bin da ya shafi harkokin magunguna. Muna da ka’idoji kan wanda ya kamata a bari ya sayar da magunguna da wanda za a sayar masa da magungunan, amma ba mu bin wadannan ka’idoji.”

A farkon watan nan Sarki Sanusi ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki matakin magance matsalar shan miyagun kwayoyi lokacin da Shugaban ya kai ziyara Jihar Kano.

Ya ambato wasu alkaluma da ke cewa ana shan kodin domin yin maye sama da kwalba miliyan uku a kowace rana a jihohin Kano da Jigawa.

Wannan dabi’a ta tu’ammali da kayen maye yanzu ta zama ruwan dare a tsakanin matasa da ’yan mata har da matan aure a Arewa.