✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A samar da gidaje ga ‘yan gudun hijira

A bisa ma’aunin ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, ’yan uwansa da abokansa da mahaifansa, wadanda suke a raye da wadanda suka…

A bisa ma’aunin ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, ’yan uwansa da abokansa da mahaifansa, wadanda suke a raye da wadanda suka rasu, kuma ya baro abincinsa da zai ci, ya baro dabbobinsa da ya dogara da su, ya yi kaura zuwa wani waje, inda bai san inda ya sa gaba ba, wannan shi ne mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta.

A kullum duk inda ka duba za ka ga ’yan gudun hijira ne birjik suna yawon barace-barace cikin kaskanci da takaici, musamman yara kanana wasunsu ma ba su dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abin da za su ci. Wadansu daga cikinsu ko takalmin sakawa ba su da shi haka suke yawo a kasa cikin tagayyara.

Haka idon muka yi la’akari da yadda idan mutum ya saba da wajen zamansa aka ce ya tashi ya bar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya zai ji a ransa? A  baya-bayan nan shekaru biya cikin na uku da suka gabata lokacin da gwamnatin Jihar Zamfara ta rika tayar da mutane da sunan sun tare hanya a saman wasu daga cikin titunan Gusau, duk wadanda wannan lamari ya shafa, ko ka san irin raɗaɗin da suka ji?

Haka a lokacin da gwamnatin Jihar Zamfara ta sallami wadansu daga tasha da sunan samar da tsaro a cikin al’umma, duk wanda wannan lamari ya shafa bai ji daɗi ba, kasancewar akwai dubban jama’a da suke ciyar da iyalansu da ’yan uwansu, wadansu ba su da inda suka dogara koma bayan hada-hadar da suke yi a wajen. Duk wanda lamarin ya shafa a wancan lokacin ba za ka iya auna irin bakin cikin da ya shiga ba.

In ko haka ne! To ina ga waɗanda hare-haren ’yan bindiga ya sa su arcewa daga garuruwansu zuwa inda ba su sani ba?

Misali; a Jihar Borno akwai kungiyoyin sa-kai waɗanda ba mallakar gwamnati ba ne mun ga yaddda suke kokari wajen fafutikar samar wa al’ummar yankinsu mafita, ta hanyar nemo tallafi na musamman daga wasu manyan kungiyoyin ba da agajin gaggawa na duniya, kuma suna ba su haɗin kai da kwarin gwiwar hada karfi-da-karfe don kawo dauki ga al’ummarsu.

A Jihar Borno akwai wurare na musamman da gwamnatin Borno karkashin jagorancin Gwamna Kashim Shettima ta ware domin kula da ’yan gudun hijira. Duk kauyen da tashin hankali ya shafa suna iya zuwa wannan wuri da aka ware dominsu su zauna, su ci gaba da samun tallafi da kula da addu’ar samun zaman lafiya a cikin garuruwansu. Duk wanda yake  bukatar bayar da taimako zai iya zuwa wajen domin bayar da taimakon.

Amma mu Jihar Zamfara har yanzu ’yan gudun hijiranmu sun kasa samun irin wannan gata cikin jama’a, ya kamata a san su ma fa mutane ne kamar kowa, sannan suna bukatar jin daɗin rayuwa kamar kowa, haka ba a son ransu haka ya faru da su ba, tsautsayi ne wanda ba ya wuce ranarsa.

To me ya sa ba za a taimake su ba? Me ya sa ba za a janyo su a jiki ba? Ko shakka babu irin kudaden da gwamnatin Jihar Zamfara take kashewa duk wunin Allah wajen fannin siyasa da an yi amfani da koda rabinsu, wajen tallafa wa ’yan gudun hijira tabbas za su ji dadi, matuƙa duk da damuwar da suke ciki.

Kasancewar yanzu azumi yana matsowa shin ina makomar waɗannan bayin Allah? Ta yaya za su samu abin da za su ci domin samun damar gabatar da ibada cikin sukuni da walwala? Haƙiƙa ya kamata a dubi ’yan gudun hijira da idon rahama a taimaka musu.

Muna kira da babbar murya ga gwamnatin Jihar Zamfara ta dubi girman Allah ta taimaki ’yan gudun hijira da wajen zaman na musamman wato ‘camp’ domin su samu su tsugunna har Allah Ya kawo musu sauki maimakon raɓe-raɓen da suke yi a makarantu ana korarsa. Muna fata da addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya a cikin Jihar Zamfara da Arewa da Najeriya da duniyar Musulmai baki daya.

Ya Allah Ka karo mana arziki mayalwaci a kasar nan.

Nura Muhammad Mai Apple Gusau, dan Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa Reshen Jihar Zamfara,   08133376020