Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

A sayar da Kamfanin Karafa na Ajaokuta – Masana

Masu masana’antu da kwararru sun ce sayar da kamfanin karafa na  Ajaokuta zai haifar da da mai ido ga gwamnati, maimakon tafiyar da harkokinsa  da gwamnatin take yi.

Da suke zantawa da manema labarai a mabambantan lokuta, sun ce tafiyar da kasuwanci da gwamnati kan yi ba a cika samun riba ba, face cin hanci da rashawa da kuma barnatar da dukiya.

ADVERTISEMENT

Saboda haka sun shawarci gwamnati ta sayar da hannun jarin kamfanin ta hanyar da ta dace domin kauce wa yin kitso da kwarkwata.

Wani kwararre kuma dan kasuwa Dokta Bincent Nwani, ya ce bai kamata a ce gwamnati ce take gudanar da kasuwancin kamfani ba.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “Kamfanin Karafa na Ajaokuta yana bukatar a tafiyar da shi ta hanyar kasuwanci ba wai ya zama ma’aikata daga cikin ma’aikatun gwamnati ba ko wata kungiya wacce take ba don riba ba. Kamfanin yana bukatar a mayar da shi hannun ’yan kasuwa masu zaman kansu domin samun cikakkiyar gudanarwa. Kamfanonin karafa na duniya kamar su Japan da sauransu ba gwamnati ce take gudanar da su ba, suna hannun ’yan kasuwa masu zaman kansu ne kuma suna aiki yadda ya kamata da gagarumar nasara.”

Nwani, ya nanata cewa kamfanonin sarrafa karafa su ne kashin bayan ci gaban kowacce kasa a duniya.

“Idan har aka tafiyar da Kamfanin Karafan na Ajaokuta ta hanyar da ta dace, zai samar wa kamfanonin cikin gida cikakkun kayan aiki, sannan zai samar da issasun kudaden musaya da ake batarwa wajen sayo kayayyaki daga waje. Kuma zai samar da karin aikin yi da bunkasa tattalin arziki,” inji shi.

Wani kwararre kuma Farfesa a Jami’ar Tarraya da ke Uyo, Leo Ukpong, ya ce cin gashin kai  zai sa kamfanin ya samu damar tafiyar da harkokin sa ba tare da tarnaki ba kuma cikin nasara.

Ya ce, “Kasuwancin da gwamnati take gudanarwa yana dauke da tarihin cin hanci da rashawa da kuma rashin ci gaba da aiki, idan wata gwamnatin ta tafi wacce ta zo ba za ta dora daga inda tsohuwar gwamnati ta tsaya ba, sai ka ga sabon shugaba ya dauko nasa sabon aikin. Bukatar karfe a duniya ta karu matukar gaske, wannan zai ja hankalin duk wani mai son zuba jari a harkar karfa.”

Shugaban Kungiyar Masu Masana’antu ta Kasa, Mansur Ahmed, ya ce yana da matukar alfanu a ce harkar karafa tana cin gashin kanta domin idan kasuwancin ya dawo hanun ’yan kasuwa zai jawo hankalin masu zuba jari na kasashen duniya.

Ya nanata cewa masu zuba jari su ne wadanda suka dace su tafiyar da harkar karafa a Najeriya domin su mai da ita harka ta samun riba.

Ya cewa koda gwamnati za ta sa hannu a cikin harkar to dole masu zuba jari suna da ’yancin gudanar da kamfanin ba tare da tsangwama ba, domin masu zuba jarin suna da yawa da ya kamata a ba su dama.

Mansur Ahmad ya ce, yana fatan haka ta kasance cikin gaggawa domin ana tsananin bukatar karafa a Najeriya domin ci gaba cikin hanzari.

Tun farko, Shugaban Kungiyar Masu Amfani da Karafa ta Kasa, Farfesa Benjamin Adewuyi, ya bukaci Shugaba Buhari ya kammala aikin masana’antar karafan da ya rage kafin wa’adin mulkinsa na biyu.

Adewuyi wanda ya fadi haka  a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce ya kamata Shugaba Buhari ya tabbatar ya kammala aikin Ajaokuta, ya fara aiki kafin wa’adinsa ya kare domin bunkasa tattalin arziki.

Ya ce idan aikin ya kammala za a samar da makamai da albarusai  da motoci da sauran abubuwa masu yawan gaske, kayan da ake shigowa da su kuma kamfanin zai samar da su cikin kasa.

Ya ce “Kamfanin Karafa na Ajaokuta yana da karfin da zai samar da motoci da makamai ga sojoji da kuma samar da dimbin ayyukan yi ga ’yan kasa kuma ya bunkasa tattalin arziki. Muna yaudarar kanmu ne kawai cewa muna kera mota a cikin gida. Ba za mu taba yin motoci ba ba tare da Kamfanin Ajakuta yana aiki ba. Muna da matasa masu hazaka da za su iya duk wani kokari na ci gaba sai da kawai babu kayan aiki, Shugaba Buhari ya sake ziyartar Kamfanin Ajaokuta sannan ya aza harsashin karasa aikinsa.