✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A sayar da matatun man fetur

A yunkurin da ake yi na farfado da matatun man fetur din kasar nan hudu da suka hada da na Fatakwal da Wari da ta Kaduna,…

A yunkurin da ake yi na farfado da matatun man fetur din kasar nan hudu da suka hada da na Fatakwal da Wari da ta Kaduna, Gwamnatin Tarayya ta sa hannu a kan takardar yarjejeniya tsakaninta da wasu kasashe da suka hada da China da Indiya da Saudiyya da kuma Rasha. Babu makawa hakan ya faru ne saboda rashin katabus da aka yi a baya wajen gyarawa da farfado da matatun man.

An gina matatun man ne domin su biya bukatar da muke da ita na man fetur da dangoginsa amma sai dai wannan bukata ba ta kai gaci ba, domin ta zama wata hanya ta barnatar da dukiyar kasa. Ko da yake Najeriya tana daya daga cikin kasashe 10 mafi arzikin man fetur a duniya, amma har yanzu tana ci gaba da shigo da tataccen mai domin amfanin ’yan kasa a farashi mai tsada. Gwamnati ta yi iyakar kokarinta wajen magance wannan matsala amma har yanzu kwaliyya ba ta biya kudin sabulu ba.

Kulla yarjejeniyar da aka yi da wadancan kasashe hudu, ta sa gwamnati  take sa ran kwalliya za ta biya kudin sabulu lura da yadda a baya gyaran matatun ya ci tura. Saka hannu a yarjejeniyar kadai ba za ta sa a ce an samu nasara a bangaren gyaran matatun ba. Domin akwai wasu matsaloli da suka kamata a yi la’akari da su, wadannan matsaloli sun hada da  shekarun matatun da aikin da aka gina su a kai da kayan gyara da ragowar bukatu da matatu suke da ita kamar garambawul da sauransu.

Sannan ya zama wajibi mu yi la’akari da cewa kamfanoni  daban-daban ne suka gina matatun, wanda hakan yana nuna cewa akwai wasu abubuwa da dole sai wadanda suka gina za su iya warware su. Idan aka kira wadansu  daban da wadanda suka gina matatun domin su gyara su, lallai za a samu matsala. A bangaren yarjejeniya kuma babu daya daga cikin kamfanonin da suka gina wadannan matatu da suka fito  daga kasashen da  aka kulla yarjejeniyar da su. Wannan shi ke nuna cewa kamfanonin da suka fito daga wadancan kasashe da aka kulla yarjejeniya da su, su ne za su yi aikin gyara matatun ba wadancan da suka gina ba, hakan yana nuna za a iya samun tangarda.

Gwamnatocin da suka gabata sun yi ta kokarin bayar da aikin gyaran matatun ga kamfanoni da daidaikun mutane wadanda ba su da kwarewa ta a zo a gani. Wannan sai ya zama wata hanya da makudan kudade suke zirarewa da sunan gyaran matatun. Wannan fage sai ya zama wata saniyar tatsa wadda hakan ya jawo gurguncewar lamari a bangaren gyaran matatun. Haka zalika masu mugun nufi na ganin matataun ba za su gyaru ba domin; su ci gaba da kwashe kudaden da ake warewa don gyaran matatun sannan su ci gaba da samun kwangilar shigo da man fetur cikin kasa da sunan lalacewar matatun.

Sakamakon wadannan matsaloli da suke gudana a wannan bangare, mafi yawan ’yan Najeriya sun yanke tsammanin cewa gwamnati za ta iya gyara wadannan matatu. A lokacin tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ya ba kamfanoni 18 masu zaman kansu lasisin kafa matatu a Najeriya amma kawo yanzu Kamfanin Dangote ne kadai ya kama hanyar cika wannan buri. Daya daga cikin dalilan da suka haddasa rashin shigowar masu zuba jari cikin harkar shi ne batun kayyade farashin mai da ake yi, wanda masu zuba jarin suke yi wa kallon nakasu.

Lura da yadda masu gudanar da  matatun man fetur suke karya doka, ya dace a sake waiwayar sayar da kadarorin gwamnati wadda Shugaba Obasanjo ya fara, daga baya Umaru ’Yar’aduwa ya suke sabo da rashin bin kaida da ake yi. Haka zalika ya kamata a sake waiwayar bangaren iskar gas da man fetur domin bayar da dama ga masu zuba jari a bangaren. Don su zuba jari a matatun da muke da su ko kuma su gina sababbi, watakila wannan ka iya zama wata hanyar ci gaba da Najeriya za ta rika amfana daga albarkatun man fetur da take da su.