✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A shirye muke mu maye gurbin sojoji – ’Yan sanda

Da yake jawabi game da lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeriya, DCP Frank Mba ya ce, ’yan sandan Najeriya a shirye suke wajen tabbatar da…

Da yake jawabi game da lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeriya, DCP Frank Mba ya ce, ’yan sandan Najeriya a shirye suke wajen tabbatar da tsaron cikin gida kamar da dokar kasa ta tanada. “Amma za mu yi nasara ce tare da hadin gwiwar gwamnati da sauran masu ruwa-da-tsaki da mutanen kasa baki daya. Idan aka samu cikakken hadin kan mutane da gwamnati, tabbas ’yan sanda za su yi aikinsu cikin nasara,” inji shi.

Ba mu goyon bayan janye sojoji – Mutanen Borno

A shekarar 2009 ce kungiyar Boko Haram ta fara addabar mutanen Jihar Borno, inda zuwa yanzu rikicin ya jawo asarar dubban rayuka da miliyoyin Naira da kuma raba miliyoyin jama’a da gidajensu.

Bayan shigowar gwamnatin Shugaba Buhari an kara kwato wasu garuruwa daga hannun Boko Haram, kuma aka rika samun nasara a yakin.

Malama Baba Ali Soja wani tsohon soja ne da ya bayyana wa Aminiya cewa idan har gwamnati ta kuskura ta janye sojoji daga fagen fama, to a gaskiya babu abin da za a ce sai “Innalillahi wa inna ilaihi raju’un. Wane shiri aka yi, shin nan da wwata uku za a gama da ’yan kungiyar Boko Haram ne ko kuwa? Domin kowa ya san yadda a nan Jihar Borno sai da ’yan Boko Haram suka kusan kwace kowace karamar hukuma amma a yanzu bayan kowa ya san halin da ake ciki na yau a kai hari a nan, gobe a kai can, sannan rana-tsaka, a ce za a janye sojoji? Yadda na san harkar tsaro da yadda na san sojojinmu, yau shekara fiye da goma, an kasa gamawa da ’yan Boko Haram, abin a duba ne. Ganin rawar da sojojinmu ke takawa a kasashen waje kan wanzar da zaman lafiya ammayanzu Boko Haram a ce sun gagare su. Don haka kamata ya yi gwamnati ta sake shawara, in dai ba so ake a ce sun shigo sun karbe Maiduguri fadar jihar ba.”

Amma Umar Ahmed, wani kwararre a harkar tsaro kuma mamba a Sibiliyan JTf, ya ce shirin Gwamnati Tarayya na janye sojoji ya dace, domin lura da yadda a kullum ake kara samun nasara a wannan yaki. “Kuma mu Sibiliyan JTF a shirye muke kuma kowa ya san irin gudunmawar da muka bayar wajen korar ’yan Boko Haram daga cikin garin Maiduguri. Kazalika ’yan sanda sun ba da tasu gudunmawar wajen yakar Boko Haram. Don haka ina ganin janye sojoji zai taimaka wajen ganin an samu dawwamammen zaman lafiya, ganin yadda kusan su kansu sojoji muna yin aiki ne tare da su, don haka babu wani abin fargaba don an janye sojoji daga wannan shiyya ta Arewa maso Gabas,” inji Umar.

Imam Abubakar Bolori cewa ya yi idan aka janye sojoji su wane ne za su maye gurbinsu domin ci gaba da fada da ’yan Boko Haram? “A yi tunani kafin aiwatar da wannan shiri na fara janye sojoji a wannan lokaci, lura da halin da ake ciki, domin haka babu wani abin da ya kamata mu al’ummar Borno mu yi illa mu ci gaba da yin addu’a, don ita ce kawai za ta kasance mafita a kan lamarin tsaro da kuma Boko Haram.”

Ba mu yi na’am da shirin ba – Sakkwatawa

A Jihar Sakkwato da ke fama da matsalar ’yan bindiga da makwabciyarta ta Zamfara, ba su yi na’am da shirin ba.

A zantawar Aminiya ta yi da wadansu mutane da ke bangaren da abin ya fi ta’azzara, sun koka kan shirin janye sojojin.

Muhammad Lawal daga  Karamar Hukumar Rabah ya ce yankinsu lamarin ya yi sauki sosai zaman lafiya ya fara dawowa. “Za ka ga soja da aka tura aiki amma ya koma yana neman mata, ko maharan sun zo suna ta’adanci wani gefen da babu soja kuma sojan ba su yin komai a kai. “Duk da ina ganin a janye su kawai, amma ta wani gefen kuma komai rashin amfaninsu, zamansu a wurin yana hana wani abu ga ’yan ta’adda. In gwamnati na son magance lamarin ai ta san yadda za ta yi,” inji shi.

A yankunan kananan hukumomin Isa da Sabon Birni, wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Muna fama da ’yan ta’dda sosai. Ko a makon jiya tun karfe 4 na maraice har 8 na dare suna cikin kauyen Tidibale, duk wata dabba da ke kauyen sai da suka tafi da ita. A jiya Talata (Talatar da ta gabata) ma sun zo nan Zango kusa da garin Isa sun kwashe rakuman da ke garin. Yanzu maharan sun canja salo zuwa satar dabbobi da yi wa mata fyade, sun daina daukar mutane a nan. A yankin Bafarawa kamar yanzu hannunsu yake, yadda suka so suke yi. Haka abin yake har a kauyen Burkusuma a Karamar Hukumar Sabon Birni.

Don haka janye sojoji ba dabara ba ce, domin duk da hakan da muke ciki mun san zaman sojoji a wurinmu yana da alfanu sosai don kila da babu su a nan da ’yan ta’addar sun karbe Isa gaba daya,” inji shi

A janye su  daga inda aka samu maslaha ba laifi – Katsinawa

Alhaji Mansir Kankara ya ce, “Ni da idona na gani a talabijin cewa, ana maganar duk wurin da aka samu zaman lafiya ne za a dauke sojojin da ke wajen a maye gurbinsu da ’yan sanda. In kuwa haka ne ina ganin wannan ba wata matsala ba ce. Da ma zaman lafiya ake nema kuma an samu. Sai dai kawai abin da za mu saurara mu ji shi ne shin za a mayar da su barikokinsu ne ko za a kara yawansu a wuraren da ake fama da matsalar tsaro ne.”

Shi kuma Malam Babangida cewa ya yi dauke su na da tasiri matuka kuma a mayar da su bariki. “Misali a lokacin da Boko Haram ke kai miyagun hare-hare ba su shiga wuri sai an janye wurin binciken kan hanya. Hakan ya sa tun a wannan lokacin ana zarginsu da hannu a ciki wajen hada baki da maharan. Sannan ai su maharan kayan sojoji suke sawa wanda abin yake da wahalar bambance su. Mafi yawan lokuta musamman a nan Jihar Katsina muna ji daga wadanda aka kai wa hari ko makwabtansu cewa sojojin na gani ko suna ji maharan na kai harin, amma in an kira su sai su ce ba a ba su umarni ba. To in kuwa har haka ne ina amfanin zamansu a inda suke? Dauke su a bar ’yan sanda zai fi barinsu, domin ko ba komai za a samu saukin kashe musu manyan kudade da ake yi. Sai dai kuma su ’yan sandan a kara wadata su da kayan aiki.”

Shi kuma Garba Abubakar Tankurina cewa ya yi janye sojojin akwai hadari, domin a cewarsa, “In da soja ya gaza ta yaya dan sanda zai iya? In kuwa har wani abu ake so na ci gaba dangane da batun tsaro a kasar nan, to a yi wa manyansu ritaya. Sannan a maido da ’yan banga tare da kara sa ido a tsakanin su kansu sojojin da sauran jami’an tsaro, domin akwai abin mamaki a ce ga abokin gaba a gabana ina kallo amma a ce an harbe ni a baya, to, wa ya harbe ni? Kuma koda ya zama dole sai an dauke su don ganin wajen akwai zaman lafiya, to a bar wadansu a wajen.”

Har yanzu muna bikatar sojoji – Zamfarawa

A Jihar Zamfara, Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Alhaji Abubakar Dauran cewa ya yi har yanzu suna bukatar sojoji, inda ya ce ’yan sanda kadai ba za su iya aikin ba.

Kwamishinan wanda ya yi magana a madadin Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce matsalolin tsaron kasar nan na bukatar hadin gwiwa ne a tsakanin jami’an tsaro da mutane baki daya.

Karin sojojin Arewa maso Gabas ke yi – Gwamnan Adamawa

A Jihar Adamawa, Gwamna Ahmadu Fintiri ya ce yankin Arewa maso Gabas na bukatar karin sojoji ne ba janyewa ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin Kakakinsa, Solomon Kumangar, inda ya ce akwai wasu jihohi da aka tura sojoji da asali ya kamata a ce ’yan sanda aka tura amma ba jihohin Arewa maso Gabas ba, inda a cewarsa nan ne ake fama da asalin matsalar tsaro.

Muna maraba da shirin

– Gwamnatin Filato

A Jihar Filato, Gwamnatin Jihar ta yi maraba da shirin janye sojojin, inda Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Mista Dan Manjang ya ce hakan zai kara sanya natsuwa a zukatan mutanen jihar, cewa an samu zaman lafiya.

“Mu a nan Filato sojoji sun yi kusan shekara 10, don haka ya kamata su koma bariki.”

Kada a yi garajen janye sojoji – Gwamnan Taraba

Gwamnan Jihar Taraba, Mista Darius Ishaku ya ce bai kamata a yi garajen janye sojojin ba, inda ya ce hakan zai jawo koma-baya a harkokin tsaro.

Kakakin Gwamnan, Dan Abu ya ce kasancewar sojojin ya taimaka musamman a rikicin yankin Taraba ta Kudu. Sannan ya ce duk da cewa an samu zaman lafiya, kuma ’yan sanda za su iya ci gaba da aikin, amma bai kamata a janye sojojin ba.