Da Dumi Dumi

A shirye nake in kai Kano Pillars zuwa Nes Lebul – Surajo Yahaya

Alhaji Surajo Sh’uaibu Yahaya
Alhaji Surajo Sh’uaibu Yahaya

Sabon Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars, Alhaji Surajo Shu’aibu Yahaya, ya ce yana da burin mayar da kungiyar ta zama daya daga cikin kungiyoyin  da za yi fice a Nahiyar Afirka

Ko za ka gabatar mana da kanka?

A takaice, an haife ni a 1966, a garin Gama na Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano. Na yi firamare da sakandare a garin da aka haife ni. Na kuma shiga Jami’ar Bayero ta Kano, inda na yi digiri a fannin halayyar dan Adam. Ina kuma da  diploma a fagen gudanar da mulki. Lokacin da nake dalibi na kasance mai taka leda sosai. Na buga gasar matasa ta kwallon kafa ta YSFON na ’yan kasa da shekara 13 da 19 har da 21. Bayan na kammala wasanni a matakin YSFON, na taka leda wa kungiyoyin kwallon kafa na garina, Gama, wato Gama Tornadoes da Gawuna Jubentus da Dangi Babes. Sai dai da na shiga jami’a, na daina taka leda da wadannan kungiyoyi; inda na mayar da hankali kacokan ga kungiyar kwallon kafa ta jami’ar. Baya ga sha’awata ga  kwallon kafa, ni sanannen dan siyasa ne a Kano, musamman ma a garinmu, Gama. Na tsunduma a harkokin siyasa gadan-gadan tun a 1982 a karkashin Jam’iyyar NPN. Wani dan siyasa, mai suna Isma’ila Mai Biskit ne ya shigar da ni siyasa. Ya nada ni a matsayin Shugaban Matasa a unguwarmu, yayin wata ziyara da ya kawo makarantarmu; inda ya ce lallai ni zakakurin matashi ne, wanda zamaninsa yake ja. Na nemi takarar kujerar dan Majalisar Tarayya a karamar hukumarmu, amma sai jam’iyyarmu ta ce mu kyale wanda ke kai ya ci gaba da jan zarensa. Lallai ni dan siyasa ne; sai dai sha’anin siyasar bai hana ni mayar da hankali kan kwallo ba, saboda ina da sha’awar wasanni musamman kwallon kafa.

Akwai abin sha’awa tare da tarihinka; sai dai mutane da dama sun yi mamaki, bayan da aka yi shelar kai ne Shugaban Kungiyar Kano Pillars……?

Saboda ba su da masaniya game da sabgata ta kwallon kafa. Ni mai bibiyar al’amuran Kano Pillars ne tun shekarar da aka kafa ta. Kuma ni magoyin bayan kungiyar Racca Robers ce, ina halartar motsa jikinsu, a lokacin da ba na motsa jiki a kungiyata. Bayan zabubbukan da suka gabata inda muka yi nasara sai Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ji yana son tafiya da ni, saboda siyasata ta tara jama’a ce. Na yi ta tsammanin a nada ni kwamishina; amma sai Gwamna Ganduje ya yanke shawarar nada ni Shugaban Kungiyar Kano Pillars, sakamakon yadda ya san dama can ni magoyi bayanta ne. Don haka, ga wadanda suka san ni a fagen tamaula, nadin nawa ba zai zo musu da mamaki ba.

ADVERTISEMENT

Ke nan yanzu za a iya cewa kana samun gAggan masu ruwa-da-tsaki a fagen kwallon kafa a Jihar Kano suna saka maka albarka?

Ai kamar yadda na gaya maka, Ibrahim Galadima tamkar uba yake a wajena. Ni mutum ne da ake matukar girmamawa. Ina kuma girmama mutane; kuma ina daukar darussa daga gare su. Ko da yake, Alhaji Ibrahim Galadima, ba ya Kano lokacin da aka nada ni shagabancin, sai dai ya aiko mini da sakon taya murna. Kuma dukkan tsoffafin shugabannin kungiyar sun mara mini baya. Ina ganawa da su keke-da-keke, don tuntubarsu tare da neman shawarwari daga gare su. A shirye nake kullum in karbi kuskure kuma in gyara inda suka ga na karkace.

Mene ne babban hankoronka ga Kano Pillars?

Takena shi ne kai Kano Pillars zuwa matakin Nes Lebul. Na jaddada wa kowa a kungiyar cewa ni mai da’a ne; ina kuma son mai da’a. A mako na biyu a ofis, na kafa kwamitin da zai yi bincike kan halayyar magoya bayan kungiyar. Kuma wanda yake jagorantar kwamitin, shi ne Farfesa Musa Garba mutum ne mai ilimi, wanda ya san harkar. Suna aikin gano mene ne dalilin da ke haifar da magoya bayan Kano Pillars ke nuna halayyar da ba tagari ba, ko dai a lokacin da aka yi nasara a kanmu ko muka yi nasarar. Kuma na gaya musu cewa, Kano Pillars ta lokacina za ta kasance wacce ta yi zarra cikin tsara a Nahiyar Afirka gaba daya; ba kawai a Najeriya ba.

Wane kokari kake yi wajen mayar da Kano Pillars ta rage dogaro da gwamnati?

Mun kwana da sanin ya kamata a mayar da Kano Pillars, kungiyar da ba ta dogaro da gwamnati kacokan, wajen samun kudade. Muna sa ran Pillars ta zama tana rabi-da-rabi wajen samun kudadenta ko ma kashi 70 daga gare ta kashi 30 kuma ya zo daga gwamnati. Mun tuntubi wasu kamfanoni masu daukar nauyi; kuma zuwa yanzu mun samu kyakkwawar fahimta da su.

Yaya za ka kwatanta goyon bayan da kuke samu daga Gwamnan Jihar Kano?

A gaskiya Gwamna yana abu mai kyau sakamakon sha’awar da yake da ita ga kwallon kafa da kuma irin kwarin gwiwar da yake da ita a kaina. Ya tuntubi masana sosai a kan ko zan iya aikin sai suka gwada masa, eh lallai zan iya.

Me kake yi na daban da zai karfafa gwiwar ’yan wasa da jagororin Kano Pillars?

Ina bayar da muhimmancin gaske ga harkar jin dadinsu, kuma ina kusa da su sosai. Muna zama a otel guda da su kuma mu ci abinci tare sa’annan mu tafi tare da su. Abokaina ne, kasancewata tsohon mai taka leda, wani lokacin mukan yi atisaye tare da su.

Share