✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A taimaka: Za a raba ni da ita kuma tun tana karama nake kaunarta

Ana yawan samun matsala a fannin soyayya, musamman ga wadanda ke rainon soyayya. Za ka ga mutum ya yi wa yarinya hidima tun tana karama…

Ana yawan samun matsala a fannin soyayya, musamman ga wadanda ke rainon soyayya. Za ka ga mutum ya yi wa yarinya hidima tun tana karama har ta kammala makaranta; da zarar batun auren ya zo kuma a hana shi. Malam Umar ya samu kansa cikin irin wannan yanayi, shi ya sanya ma ya rubuto cewa:

Umar Garba Gusau, 07063880864:
Assalamu alaikum FDk, shawararka nake nema kan wata abar sona da tun tana karama nake sonta, yanzu kuma samari sun yi mata yawa; iyayenta sun ce kowa ya kyale ta. Ni kuma zuciyata ita kawai take so, don ita kadai na fara so a duniya, ita ma haka. Don Allah koda tes ne, ina neman shawararka.
***
To, Malam Umar, wannan al’amari sai hakuri, domin kuwa shawarar da zan ba ka ita ce, ka mayar da al’amuranka ga Allah, ka ci gaba da addu’ar Allah Ya zaba maku abin da ya fi zama alheri a tsakaninku. – FDk.
***
Daga Sulaiman J. Ahmad BUK, 07032914243:
Fatan alheri gare ka FDk. Duk da cewa ni ba bako ba ne a wannan dandali, sai dai wannan shi ne sakona na farko. FDk, ni ban ga laifin Naseer Mustapha Kano, don ya bayyana abin da ya faru a kansa ba. Shin abin da ya fada ba haka ba ne? Don na ga kamar wasu sun fusata, kuma na san Naseer bai fadi haka da wata manufa ba. Kawai ita dai fahimta fuska ce.
***
Bashar danbala Sauwa:
FDk, Allah Ya kara maka basira. Ina yawan karanta labarinku amma ni ban taba turo nawa sako ba sai yau. Allah Ya kara mana hakuri da masoyanmu maza da mata. Ina rokon Allah Ya kara mana dankon soyayya, ni da masoyiyata Hajara. Wallahi duk wanda Allah Ya ba shi irin budurwata Hajara, ya huce takaicin duniya!
***
Daga Mai Lambar Waya 09098797426:
FDk, barka da kokari. Na kasance mai karatun wannan jarida na tsawon shekara biyar, musamman wannan fili na Dausayin kauna amma ban taba rubuto ko aiko da sako ba sai wannan karon. Akwai wata ’yar uwata da muke matukar son juna, a inda muka yanke shawarar mu sanar da iyayenmmu domin su hada mu aure. Sun amince da fari amma daga baya an dan samu sabani ta bangaren iyayenta, har ma na fara cire raina ga auren yarinyar. Shekara daya da wata takwas ta ki fitar da miji. Da mahaifinta ya matsa sai ta fitar da miji ta gaya masa cewa ni take so ta aura. To, ya amince kuma har an yanka sadaki.
***
Madalla da wannan nasara da aka samu. Muna taya ku addu’ar Allah Ya ba da sa’a a yi auren cikin nasara kuma ya ba ku zaman lafiya da hakuri. – FDk.
***
Yunus YSY, 08037401964:
FDk, ka gaggauta ba ni shawara kafin na yanke hukunci a kan mayaudariyar nan. Wallahi FDk na ki kowa saboda ita, kai a takaice shekararmu uku muna soyayya don aure tun a makaranta, ga shi mun gama har mun fara aiki. To, yanzu na yi mata naganar alkawarinmu wai ita ba wani alkawari a tsakaninmu. Ga shi ita kadai nake so, ni ina Kano, ita Kaduna.
***
Uhhm! Malam Yunusa, ka shafa wa kanka lafiya, domin kuwa duniyar nan fadi gare ta; inda wani ya ki ka da wuni, wani share maka wuri zai yi ka shekara. Don haka ka canja sheka kawai, ka kyale ta. Son maso wani koshin wahala ne! – FDk.
 ***
Isma’il Ibrahim Bauchi:
FDk, gaisuwa gare ka da duk daliban makarantar Dausayin kauna na Najeriya. Ina mika gaisuwa ta gare su da fatan zan samu shiga wannan babbar makaranta mai debe kewa (Dausayin kauna). Na dade ina leke ta tagar Dausayin kauna, daga karshe santin Dausayin ya wurgo ni cikin harabar makarantar. Da fatan ban yi laifi wa shugaban makarantar ba (FDk). Daga karshe, ina maku fatan alheri.
***
Ali Kofaral, 08068212175:
Malam FDk, ina gaishe da duk wani dan uwa na Aminiya. Allah Ya ba da nasara kuma ina gaida duk wani masoyin Manzo (SAW), Allah Ya hada mu da Annabi Muhammadu (SAW). ’Yan uwa, ku biyo mu da amin! Allah Ka ba ni Humaira, alfarmar Annabi (SWA), ku taya ni da addu’a ’yan uwa.
***
Abubakar Masoyin Habiba Auyo, 09031764361:
Don Allah ku sa ni ni ma a cikin fagen FDk. Na yi kira ga iyayen ’yan matanmu ni da abokina Kabiru, a kan irin tsawon lokacin da muka dauka muna soyayya da su, da su tausaya mana mu da ’ya’yan nasu Sadiya da Habiba.
***
Suleiman, 09038391010:
FDk, ni ne na nemi ’yan mata fiye da bakwai da niyyar aure amma sun yaudare ni. Me ya kamata in yi, ko in hakura da nema?
***
Al’amarin rayuwar duniya ai ba a barin nema. Ka ci gaba da kwankwasa kofar, wata rana za ka dace a bude maka. – FDk.
***
Ali Scorpion Maiduguri, 08098307394:
Gaisuwa ga masoyan Dausayin kauna. FDk, ni bako ne a wannan zaure amma ba bakon karanta Aminiya ba. Ina mai matukar son samun yin rajista, kafin in fara turo sakona. A huta lafiya.
***
Saifullahi Ibrahim kiru:
Gaisuwa ga shugaban wannan fili mai albarka da fatan alheri ga sauran ’yan uwana masoya. Allah Ya bar kauna gare ka Sardaunan masoya, Allah Ya kara lafiya, amin.
***
Yakubu Sa’eed Yakubu Gwaram, 07066897465:
Ya ’yan uwa ma’abota soyayya, ina mai kalubalantar Malama Fateemah Zahra’u a kan sharhinta da ta yi a kan mu maza. Gaskiya ban gamsu ba kuma ga mai tambaya zai iya yi a kan su waye mata, in sha Allahu zan yi musu adalci.
***
S. dorayi, 07060736360:
FDk, ina mika sakon gaisuwata ga dukkan ’yan uwa da abokan arziki ma’abota wannan dandali na baje kolin masoya tare da fatan alheri. Ni kam a ganina talaka da attajiri dukkansu babu na yarwa, domin kuwa kowa ya taka rawar gani, amma attajiri ya fi ba da gudunmawa amma abin da ya kamata ta yi shi ne, ta yi shawara da zuciyarta, ta zabi wanda ya fi kwanta mata a rai.