✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A taimaki ’yan kasuwar da suka yi gobara a Kasuwar Laranto – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya nemi Gwamnatin Tarayya da ta Jihar…

Sheikh Muhammad Sani Yahaya JingirShugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya nemi Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Filato da masu hannu da shuni su taimaka wa ’yan kasuwar da suka yi asara a gobarar da aka yi a Kasuwar Laranto ’Yan buhu da ke garin Jos, a daren Talatar makon jiya.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje zuwa kasuwar a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ya ce tallafa wa ’yan kasuwar ya zama wajibi ganin irin asarar da suka yi sakamakon gobarar.
Ya ce “A gaskiya hankalina ya yi matukar tashi ganin irin asarar da aka yi a wannan kasuwa, sakamakon wannan gobara, babu shakka wannan gobara ta shafi kowa.”
Sheikh Jingir ya nuna jin dadinsa kan yadda al’ummar Jos Musulmi da Kirista suka hada kansu suka nuna damuwarsu kan wannan gobara kuma suka tsaya suka kashe gobarar tare da fitar da kayayyakin da gobarar ba ta kona ba.
Ya ce wannan hadin kai da kuka nuna ya nuna wa duniya cewa ’yan Najeriya kansu a hade yake. Ya roki Allah Ya mayar musu da asarar da suka yi a gobarar. Kuma ya nemi ’yan kasuwar su kara lura wajen tausaya wa abokan cinikinsu. Ya ce ya kamata duk abin da za su sayar kada su hada abu mai kyau da marar kyau. Kuma su tausaya wa masu karamin jari a cikinsu. Daga nan sai ya tallafa wa ’yan kasuwar da Naira dubu 200.
Tun farko a jawabin shugaban kasuwar Alhaji Muhammad Kabiru Auwal, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 9:00 na dare a ranar Talatar makon jiya. Ya ce gobara ta tashi ne sakamakon kawo wutar lantarki da karfi, inda wutar ta tashi a wani shago da ke kasuwar.
Ya ce al’ummar Jos Musulmi da Kirista sun nuna tausayawarsu ta hanyar taimakawa wajen kwashe kayayyakin runfunan da wutar ba ta kona ba tare da kashe wutar. Ya ce, “A gobarar mun yi asarar rumfuna sama da 200 tare da dukiya ta sama da Naira miliyan 200.”
Alhaji Kabiru Auwal ya ce sun taba fuskantar irin wannan gobara shekara hudu da suka gabata, inda ya ce a lokacin babu wanda ya taimaka musu, amma sun samu taimakon Naira miliyan 20 ta hanyar Sheikh Sani Yahya Jingir.
Ya bukaci gwamnati da sauran masu hali su taimaka musu, kuma ya mika godiyarsu ga Sheikh Jingir kan ziyarar jajen da ya kai musu.