✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice…3

Chelsea za ta sayar da wasu zaratan ’yan kwallonta a watan Janairu Kulob din Chelsea da ke Ingila a shekaranjiya Laraba ya bayar da sananwar…

Chelsea za ta sayar da wasu zaratan ’yan kwallonta a watan Janairu

Kulob din Chelsea da ke Ingila a shekaranjiya Laraba ya bayar da sananwar yunkurinsa na sayar da wasu daga cikin zaratan ’yan kwallonsa a watan Janairun 2014 idan Allah Ya kaimu.
Daga cikin ’yan kwallon da kulob din ke tunanin sayar da su akwai Juan Mata da Demba Ba da Gary Cahill da Kebin De Bruyne da Cesar Azpilicueta da John Obi Mikel da kuma Ryan Bertrand.
Tuni kulob din Napoli da ke Italiya da Atletico Madrid da ke Sifen suka fara tunanin dauke Juan Mata yayin da kulob din Arsenal da ke Ingila ya fara zawarcin Demba Ba a matsayin aro yayin da wasu kulob da dama a Jamus suke kokarin dauke De Bruyne.

Nan gaba za a mayar da kasashen da za su fafata a gasar cin kofin duniya zuwa 40 -Platini

Shugaban Hukumar Shirya Wasan kwallo a Nahiyar Turai (UEFA) Michel Platini ya bayar da shawarar cewa akwai yiwuwar nan gaba kadan kasashe 40 ne za su rika fafatawa a gasar cin kofin duniya maimakon 32.
A shekara mai zuwa ne za a gudanar da gasar cin kofin duniya a Brazil inda kasashe 32 za su fafata.
kasashe 13 ne za su wakilci Nahiyar Turai yayin da biyar suka fito daga Nahiyar Afirka sannan Kudanci da Arewacin Amurka da kuma yankin Asiya suka raba sauran guraben.
Ana sa ran Afirka ta sake samun karin biyu biyu idan aka samu karin.

Kulob din Arsenal ya fara yunkurin dauke dan kwallon Najeriya Kelechi Iheanacho

Kulob din Arsenal da ke Ingila, ya fara tunanin dauke dan kwallon Najeriya Golden Eaglets da yanzu haka yake haskakawa a gasar cin kofin duniya na matasa (U-17) a Dubai mai suna Kelechi Iheanacho.
An shaidi kulob din da yaye matasa idan sun girma ya sayar da su da tsada ga kulob da dama a sassan Nahiyar Turai.
Ya zuwa yanzu Kelechi Iheanacho ya zura kwallaye biyar ga kungiyar kwallon kafa ta Eaglets a gasar cin kofin duniya na matasa da ke gudana a  Dubai.
Iheanacho dai yana buga kwallo ne a kulob din matasa na Taye Academy da ke Owerri ta Jihar Imo