✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice…4

Lukman Haruna ya koka a kan rashin gayyatarsa dan kwallon Najeriya Super Eagles Lukman Haruna ya bayyana rashin jin dadinsa na rashin gayyatarsa da koci…

Lukman Haruna ya koka a kan rashin gayyatarsa

dan kwallon Najeriya Super Eagles Lukman Haruna ya bayyana rashin jin dadinsa na rashin gayyatarsa da koci Stephen Keshi ya yi don karawa da kasar Habasha a wasan neman gurbin zuwa cin kofin duniya da za a yi a garin Kalaba a ranar 16 ga watan nan da muke ciki.
dan wasan tsakiya na Dynamo Kieb, yanzu haka yana haskakawa a gasar rukuni-rukuni na kasar Ukraine ya yi tsammanin za a gayyace shi amma abin mamaki sai koci Keshi yi biris da shi. Stephen Keshi dai ya so ya gayyaci Haruna da dan kwallon kulob din Hull City da ke Ingila Sone Aluko da kuma Gabriel Reuben, sai dai Reuben din kawai ya samu gayyata daga cikinsu.

Jibi Manchester United za ta kara da Arsenal

A jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu kungiyoyin kwallon kafa na Manchester United da kuma na Arsenal na Ingila za su fafata a gasar rukunin Premier.
Za a yi wasan ne a gidan United, kuma wasa ne da daukacin duniya za ta zuba ido don ganin yadda za ta kaya.
A halin yanzu dai kulob din Arsenal ne yake samun tebur da maki 25 daga wasanni 10 yayin da United take ta takwas da maki 17 daga wasanni 10.
Idan United ta samu nasara, za ta zage rarar maki 8 zuwa 5 da kulob din Arsenal ya ba ta yayin da idan Arsenal kuma ta samu nasara ko shakka babu za ta ba United tazarar maki 11.
Ana sa ran za a fara wasan ne da misalin karfe biyar da minti 10 agogon Najeriya.

Na fi kaunar Ronaldo fiye da Cristiano Ronaldo -Kaka

Shahararren dan kwallon AC Milan da ke Italiya ya bayyana cewa a nasa ra’ayin ya gwammace ya zabi Ronaldon Brazil fiye da Cristiano Ronaldo da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Real Madrid.
Ronaldon Brazil a lokacin da yake kwallo ya lashe gwarzon dan kwallon duniya a shekarar 1997 da kuma a 2002. Sannan ya taba lashe kofin duniya sau biyu da kasar Brazil.
Shi kuwa Cristiano Ronaldo sau daya ya taba lashe gwarzon dan kwallon duniya a lokacin da yake buga kwallo a kulob din Manchester United da ke Ingila.