✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice… 5

Messi zai shafe wata biyu ba tare da buga kwallo ba Shahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen Lionel Messi zai kwashe akalla makonni…

Messi zai shafe wata biyu ba tare da buga kwallo ba

Shahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen Lionel Messi zai kwashe akalla makonni takwas yana jinya ba tare da yin kwallo ba saboda raunin da ya samu a cinyarsa ta hagu.

Messi, dan kimanin shekara 26 ya samu rauni ne a wasan da kulob dinsa ya yi da na Real Betis a gasar La-Liga ta Sifen a karshen makon jiya.
FC Barcelona ce ta samu nasara a wasan da ci 4 da 1.
A daidai minti na 21 ne Andre Iniesta ya canza Messi a wasan bayan ya samu raunin.
Tuni mahukunta kulob din FC Barcelona suka tabbatar da wannan labari.

dan Najeriya zai yi alkalanci a gasar Club World Cup

Peter Edibi, alkalin wasa dan Najeriya yana daga cikin wadanda za su yi alkalanci a gasar Club World Cup da za ta gudana a kasar Maroko.
Wannan shi ne karon farko da wani alkalin wasa da ya fito daga Najeriya zai yi alkalanci a irin wannan gasa.
Gasar za ta gudana ne a tsakanin ranakun 11 zuwa 21 ga watan Disamban 2013 a kasar Maroko.
kungiyoyin kwallon kafa guda shida ne ake sa ran za su fafata da suka hada da kulob din Bayern Munich da ke Jamus da Al Ahly da ke Masar da Atletico Mineiro daga Brazil da kulob din Monterrey da ke Meziko da Auckland City daga New Zealand da kuma mai masaukin baki Raja Casablanca da ke Maroko.
Duk kulob din da ya lashe kofin zai samu kyautar Dala miliyan ashirin kwatankwacin Naira Biliyan 3 da miliyan 200.

Watakila Hernandez ya koma Arsenal a watan Janairu

Kulob din Arsenal da ke Ingila ya fara shirye-shiryen dauke dan wasan gaban kulob din Manchester United da ke Ingila a watan Janairun badi idan Allah Ya kaimu.
Kulob din ya ce ya lura dan wasan gabansa Olibier Giroud yana iya samun matsala a lokacin da kakar wasa ta yi nisa, kuma hakan na iya jefa kulob din cikin matsala don haka ya yanke shawarar dauke Jabier Hernandez daga kulob din Manchester United.
Kocin Arsenal, Arsene Wenger a baya ya so ya dauke dan kwallon gaba a kulob din Liberpool Luis Suarez amma hakarsa ta ba cimma ruwa ba.
Sannan an ruwaito kocin ya fara zawarcin matasan ’yan kwallon Brazil biyu da suka fafata a gasar cin kofin duniya na matasa da ya gudana a Dubai kwanan nan watau Boschilla da kuma Nathan.