✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice… 6

FIFA ta kara wa’adin ranar zaben dan kwallon duniya Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta kara wa’adin lokacin da za a zabi gwarzon dan…

FIFA ta kara wa’adin ranar zaben dan kwallon duniya

Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta kara wa’adin lokacin da za a zabi gwarzon dan kwallon duniya.
Jaridar Daily Mirror ta Ingila ta kalato cewa a da Hukumar FIFA ta rufe zaben ne tun ranar 15 ga watan Nuwamba da muke ciki amma ganin yadda mafi yawa daga cikin wadanda ake sa ran za su kada kuri’ar ba su samu damar yin haka ba ta sa aka kara wa’adin mako biyu.
Masu kada kuri’ar dai su ne masu horarwa daga ko’ina a fadin duniya da shugabannin gidajen jaridu da kuma kyaftin-kyaftin na kulob-kulob da ke sassan duniya.
Da wannan canji da aka samu, wadanda suka kada kuri’a kafin wannan lokaci suna da damar sake ra’ayi a kan wanda suka zaba, don haka an ba su damar sake kada sabuwar kuri’a kafin ranar 29 ga wannan wata da muke ciki.
Alamu sun nuna shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma dan asalin Fotugal, Cristiano Ronaldo ne zai lashe kyautar ta bana.

 

 

Za a fitar da Jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya a ranar 6 ga watan Disamba mai zuwa

A ranar 6 ga watan Disamba ne ake sa ran Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) za ta fitar da jadawalin gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a shekearar 2014.
kasashe 32 ne daga Nahiyoyin duniya ake sa ran za su fafata a gasar.
Za a fara gasar ce a ranar Alhamis 12 ga watan Yunin 2014 kuma ana sa ran kare ta a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2014.
A kasar Afirka, akwai Najeriya da Kwaddebuwa da Kamaru da Ghana da kuma Aljeriya.
A kasashen Turai kuwa akwai manyan kasashe irin su Italiya da Ingila da Jamus da Beljiyam da Faransa da sauransu.
Gasar cin kofin duniya ita ce gasa mafi girma a harkar kwallo a duk fadin duniya.  
kasar Brazil ce mai masaukin baki, kuma ita ce kasar da ta fi lashe kofin har sau biyar a tarihin gasar.
Ana sa ran kasashen Afirka irin su Najeriya za su haskaka a gasar a wannan karon idan aka yi la’akari da yadda suke nuna kwazo a wasannin da su yi a baya.