✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice… 7

Cristiano Ronaldo zai shafe mako uku a benchiShahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo ya samu rauni a cinyarsa ta hagu  a…

Cristiano Ronaldo zai shafe mako uku a benchiShahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo ya samu rauni a cinyarsa ta hagu  a wasan da suka yi da kulob din Almeria a gasar rukunin La-Liga na Sifen a karshen makon jiya da hakan zai shafe kimanin makwanni uku ba tare da ya yi wasa ba.
Ronaldo ne ya fara zura kwallon farko a raga a wasan da kulob din ya doke na Almeria da ci 5-0 a ranar Asabar da ta wuce.
dan wasan ne da kansa ya nemi a canza shi a wasan bayan ya samu rauni.  Tuni kulob din ya tabbatar da raunin da Ronaldo ya ji kuma ya ce ana sa ran dan kwallon zai dawo filin daga ne a ranar 14 ga watan Disamba mai zuwa watau ranar da kulob din zai hadu da na Osasuna a gasar ta La-Liga.
Ronaldo dai yana daga cikin ’yan kwallo uku da za su fafata a gwarzon dan kwallon duniya ta bana. Sauran ’yan kwallon biyu su ne Lionel Messi na FC Barcelona da ke Sifen da kuma Frank Ribery dan kwallon Bayern Munich da ke Jamus.

Ni na fi cancantar lashe Gwarzon dan kwallon Duniya -Ribery

Shaharareen dan kwallon Faransa da kulob din Bayern Munich da ke Jamus, Frank Ribery ya ce ko shakka babu shi ya fi cancantar lashe Gwarzon dan kwallon Duniya (Ballon d’Or) a bana.
“Gaskiya ba na shakkar gwabzawa da kowa a wannan gasa saboda irin namijin kokarin da na yi a kakar wasa ta bana musamman wajen lashe manyan kofuna da kuma taimakawa Faransa hayewa gasar cin kofin duniya”.
“Idan aka kalli yadda na yi kwazo a kakar wasan da ta wuce da kuma ta wannan shekara, bayan na taimaka wajen zura kwallaye da kuma yadda na taimaka aka zura kwallaye a raga ba na shakkar kowa a gasar gwarzon dan kwallon duniya.
dan shekara 30 Ribery ne aka zaba gwarzon dan kwallon Nahiyar Turai a kwanakin baya bayan ya taimaki kulob din Bayern Munich wajen lashe manyan kofuna uku a kakar wasan da ta wuce.

’Yan kwallona sun ba ni kunya -Koci Andre billa-Boas

Kocin kulob din Tottenham da ke Ingila, Andre billa-Boas ya ce ’yan kwallonsa sun kunyata shi bayan sun bari ’yan wasan Manchester City da ke Ingila sun yi musu raga-raga da ci 6-0 a gasar rukunin Premier ta Ingila a ranar Lahadin da ta wuce.
kwallaye biyu da dan kwallon City Sergio Aguero da biyu daga Jesus Nebas da wacce Albaro Negredo da kuma wacce Sandro suka jefa a raga ta sa suka lallasa Tottenham da ci 6-0.
Rabon da a yi wa Tottenham irin wannan wulakanci tun a shekarar 1996 kimanin shekara 17 a lokacin da kulob din Newcastle United ya lallasa na Tottenham a gasar Premier da ci 7-1.
A wannan makon ne kuma ake sa ran kulob din na Tottenham zai hadu da  Manchester United a gasar rukunin Premier na Ingila.