✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice…

Swansea na neman Fam miliyan 30 a kan Michu Kulob din Arsenal da na Liberpool tilas su biya Fam miliyan 30 muddin suna bukatar dan…

Swansea na neman Fam miliyan 30 a kan Michu

Kulob din Arsenal da na Liberpool tilas su biya Fam miliyan 30 muddin suna bukatar dan kwallon kulob din Swansea Michu, dan kimanin shekara 27 kamar yadda jaridar The Mirror ta Ingila ce ta ruwaito.

Hernandez zai bar Manchester United

dan wasan gaban kulob din Manchester United Jabier Hernandez, mai kimanin shekara 25 ya bayyana kudurinsa na barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana ganin yadda koci Dabid Moyes yake yawan ajiye shi a benchi.  Ya zuwa yanzu ya buga wasanni biyu ne kacal daga cikin wasanni 11 a karkashin kulawar sabon kocin.

Sagna zai bar kulob din Arsenal

Kulob din Arsenal ya fara fafutukar shawo kan dan kwallon bayansa Bacary Sagna, dan kimanin shekara 30 don ganin bai bar kulob din a karshen kakar wasa ta bana ba.  Kwantaragin dan kwallon za ta kare ne a karshen kakar wasa ta bana, kuma dan kwallon ya nuna ba ya da sha’awar sabunta kwantaraginsa a kulob din.

Gareth Bale ya lashe gwarzon dan kwallon kasar Wales

A ranar Litinin da ta wuce ne shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen Gareth Bale ya lashe gwarzon dan kwallon kasar Wales a karo na uku.
Wannan ta sa dan kwallon ya yi kafada da kafada da Mark Hughes da kuma John Hartson, tsofaffin ’yan kwallon da suka taba lashe kyautar har sau uku a tarihinta.
Gareth Bale ne ya lashe kyautar a shekarar 2010 da 2011 da kuma 2012, ma’ana ya lashe kyautar sau uku a jere kenan.
Gareth Bale shi na dan kwallo mafi tsada a duniya a halin yanzu bayan da kulob din Real Madrid ya saye shi daga kulob din Tottenham da ke Ingila a kan Fam miliyan 86 gab da za a fara kakar wasa ta bana.
Ya zuwa wannan lokaci, dan kwallon bai yi wasan kirki a kulob din na Madrid ba saboda raunin da yake fama da shi.