Da Dumi Dumi

A wannan wata kotu za ta yanke hukunci kan shari’ar Buhari da Atiku

Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta shirya don yanke hukunci kan shari’ar da ke tsakanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da babban mai kalubalanta zabnesa Atiku Abubakar na PDP a cikin watan nan na Satumba.

Ana sa ran alkalan kotun su yanke hukuncin a cikin wannan wata kamar yadda sashi 134 (1) zuwa (3) na dokar zabe ya yi tanadin cewa za a shigar da kara, a kuma tattauna a kotu a yanke hukunci cikin kwana 180 da gudanar da zabe. An sanya wannan sashin cikin dokar zabe ne saboda gudun kada a dauki dogon lokaci da zai haifar da jinkiri kafin raba gardama a tsakanin ’yan siyasa. A cewar majiyarmu, “Ko shakka babu za a yanke hukunci kan karar da Alhaji Atiku Abubakar ya shigar kan zaben ranar 23 ga Fabrairun bana. Kotun ba za ta iya wuce ranar ba, wajen yanke hukuncin saboda haka dokar, kasa ta yi tanadi, don kwana 180 ne da doka ta tanada a yanke hukunci.”

A makon jiya, Kotun Kolin ta kori bukatar Jam’iyyar PDP da dan takararta ta a ba su damar duba shafin rumbun bayanai na Hukumar INEC.

 

ADVERTISEMENT
Share