✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yanzu da fursunoni ke da `yancin kada kuri`a

A makon jiya ne, Kotun Daukaka Kara ta reshen Benin babbar birnin Jihar Edo ta yanke hukuncin cewa, fursunonin Najeriya suna da ’yancin kada kuri’arsu. An…

A makon jiya ne, Kotun Daukaka Kara ta reshen Benin babbar birnin Jihar Edo ta yanke hukuncin cewa, fursunonin Najeriya suna da ’yancin kada kuri’arsu. An zartar da hukuncin ne bayan da wadansu fursunoni biyar suka bukaci kotun  ta taimaka wajen samar wa fursunonin kasar nan ’yancin kada kuri’arsu tare da gamsar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a kan ta tanadar wa duk fursunonin kasar nan rajistar zabe don samun damar kada kuri’a a zaben 2019 mai karatowa.

An dai shigar da bukatar haka a kotun ce tun farkon shekarar 2014, wadda za ta bai wa fursunonin Najeriya damar kada kuri’a a lokacin zabe. Alkalin Kotun Mai shari’a S. Oseji wanda ya jagoranci shari’ar, bai ba Hukumar INEC umarnin hada kai da Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya wajen samar da cibiyoyin zabe a cikin yankunan kasar ba, kamar yadda wadanda suka shigar da karar suka bukata.

A yayin da yake jawabi lauyan da ya tsaya wa fursunonin Mista Aigbokhan wanda kuma Shugaban Kungiyar ‘Initiatibe for Rural Debelopment Information and Legal Adbocacy’ ne ya ce, manufar masu tabbatar da dokar ita ce a rattaba hannu wajen bai wa Hukumar INEC umarnin bude mazabu saboda fursunoni. A cewarsa fursunoni jama’a ne da suka kai yawan wata unguwa, don haka akwai bukatar a bude musu wata cibiyar kada kuri’a, saboda fursunoni na da ’yancin kada kuri’a a lokacin zabe don sanin wadanda za su jagorance su nan gaba.

Wannan hukuncin da kotun ta yi yana tattare da tambayoyin da suka fi amsoshi yawa, musamman a fannin kalubalen samar da kayan zaben da Hukumar INEC za ta yi. Na farko akwai amincewa da umarnin kotu wanda ya hada da rajistar zabe ga fursunoni. Akwai alamar cewa, fursunoni ba su cikin rajistar zabe na hukumar, yayin da a yanzu aka rufe lokacin yin rajistar masu kada kuri’a. Ana bukatar lokaci na fara shirya yin rajistar sababbin masu kada kuri’a a zabe mai karatowa. Da a ce tun lokacin da aka bukaci kaddamar da dokar shekara hudu da suka gabata, da yanzu fursunoni sun fara more wa ’yancin yin zaben.

A muhawarar da aka yi a kan samar wa fursunoni ’yancin zabe ya janyo wa wasu kasashe aikata laifuffuka wajen yin adalci na tsawon lokaci. Abin tambayar a nan shi ne, wane ’yanci ne doka ta tanadar wa fursunonin kasar nan da ke tsare? Irin hakan ya sa duk mai laifin da ke tsare yake  da iyaka a wasu abubuwa har da rashin samun damar kada kuri’a ga wanda yake so, ba kamar yadda kowa yake da ’yancin kada kuri’a ba, saboda dai laifin da fursunonin suka yi har ya kai ga tsare su. An samu bambancin hukuncin doka a tsakanin babbar kotu a shekarar 2014 da hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Benin a sauraren karar da aka yi. A yayin da ake bukatar samar wa fusunoni ’yancin yin zabe Hukumar INEC ba ta da wata hanya ta kada kuri’a ga fursunoni. Wadanda kawai da Hukumar INEC ba ta amince musu da kada kuri’a ba su ne: wanda bai kai shekara 18 da wanda ba dan Najeriya ba, wanda ba su yi rajistar zabe ba da wanda ba su da katin zabe da kuma wadanda sunansu ba ya cikin rajistar zabe.

Wannan hukuncin zai samu gindin zama ne idan har Kotun Koli ta amince a samar wa fursunonin Najeriya ’yancin kada kuri’a, sannan a fara shirye-shiryen yi musu rajista da kuma samar masu da mazabu kusa da gidajen yari ko kuma a rika dauko su zuwa mazabun don kada kuri’arsu. Hakan kuma ba zai yiwu ba kafin zaben 2019, saboda yin hakan wasu matakai ne da za a bi. Yanzu INEC kawai ta fara shirye-shiryen a bayan zaben 2019.

Hanyar da za ta fi amfani ga fursunonin Najeriya ita ce a ilimantar da su a fannoni da dama, a sanya su mai da hankali sosai a kan ilimin. Najeriya tana da gidajen yari 240 yayin da 155 daga cikinsu fursunonin na jiran a yanke musu hukunci, gidajen yari 83 ke da na’urar setilayit. Nan gaba akwai bukatar sake yin shiri a kan yadda fursunonin za su iya kada kuri’a ba tare an hada su da jami’an tsaro ba. Wani abu kuma da yake da muhimmanci shi ne yadda za a fahimtar da fursunoni wanda zai ba su haske a kan ’yan takarar jam’iyyu, idan ba haka ba fursunonin za su kada kuri’arsu a kan kuskure.

Wannan hukuncin da Kotun Daukaka Karar ta yanke zai janyo wa Hukumar INEC karin matsaloli da jami’an hukumar. Bayyana dalilin tsare fursunonin na da matukar muhimmanci wajen kaddamar da ’yancin kada kuri’a a tsarin dokar kasa, yayin da akwai bukatar shiri na musamman don tabbatar da dokar.