✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yau za a ci gaba sauraran karar Shema da EFCC ta shigar

A yau Litinin ne ake ci gaba da sauraran karar da ake yi wa tsohon Gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shema  tsakanin gwamnatin jiha da gwamnatin…

A yau Litinin ne ake ci gaba da sauraran karar da ake yi wa tsohon Gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shema  tsakanin gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya a babbar kotun jihar Katsina.

Kotun dai na tuhumar Shema ne akan zambar kudade da suka kai adadin naira biliyan 17.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta Najeriya, EFCC ce ta kai tsohon Gwamna Shema tare da wasu mutum uku da suka hada da: Sani Makana da Ibrahim Yankaba da Lawal Safana zuwa babbar kotun akan laifin karkatar da kudin da suka kai naira biliyan 11 na kananan hukumomin jihar.