Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
A yayin da Kankiyan Katsina ya cika shekara 10 a karaga

A yayin da Kankiyan Katsina ya cika shekara 10 a karaga

Ranar Asabar 28 ga watan Afrilun da ya gabata ta kara shiga cikin muhimman ranakun tarahin gundumar Kankiya kuma Hedkwatar Karamar Hukumar da ke cikin Jihar Katsina. Kasancewar a waccan rana ce `yan asalin gundumar da ma na Karamar Hukumar baki daya da masoya da aminai da masu fatan alheri na kusa da na nesa daga dukkan fadin kasar nan, suka hallara a garin na Kankiya don taya mai girma  Hakimin gundumar kuma Kankiyan Katsina, Alhaji Musa Hassan Sada murnar cika shekaru goma cif-cif, a kan karagar mulkin masarautar da ya gada iyaye da kakanni.

Ko shakka babu, abin a gode wa Allah ne a duk lokacin da aka kai irin wannan lokaci, ana tafiyar da harkokin jama`a, musamman mulkin jama`a irin na sarauta cikin kwanciyar hankali da karuwar jama`a, a kuma masauta mai tsohon tarihi irin ta Kankiya. Masarautar da tarihi ya tabbatar da cewa an kafata tun wajejen karni na 17. Dadin-dadawa, ga shi kuma bayan zama lafiya da jan mutanensa da yake a jika, mai girma Alhaji Musa Hassan Sada, Kankiyan Katsina, yana kuma da abin da zai fadi tare da nuna wa duniya ya yi daga hawansa mulki.

Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya tabbatar wa da Kankiyan Katsina, Alhaji Musa Hassan Sada wannan sarauta a ranar 16 ga watan Mayun  2009, bayan rasuwar kanin mahaifinsa Kankiyan Katsina marigayi Alhaji Audu Kaita a cikin watan Mayun. A baya mahaifinsa Kankiyan Katsina Alhaji Hasssan Sada, shi ya gaji mahaifinsu mariigayi Sada Nadada, wanda shi kuma dan Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ne, kenan Kankiya Musa Hassan Sada gadon sarauta ya yi.

Tarihin rayuwar mai girma Kankiyan Katsina Alhaji Musa Hassan Sada ya tabbatar da cewa an haife shi ne a garin Kaita a 1947, a lokacin kakansa Alhaji Sada Nadada yake Hakimin Kaita kuma Sarkin Sullubawa. A Kaita ya fara karatun allo da na boko, inda bayan ya kammala firamare a 1961, a 1962, ya samu shiga Kwalejin koyon sana`a ta Mashi, inda ya kammala a  1966. Ya samu fita zuwa kasashen waje irin su Birtaniya da Faransa inda ya karo ilimi a kan fannin injiniya. Ya yi aiki da Hukumar Raya Kogunan Hadeja da Jama`are mai hedkwata a Kano. Ya yi ritaya daga ma`aikatar Ayyukan gona ta tarayya a matsayin Darakta a 2007.

Dukkan mutanen Karamar Hukumar Kankiya da ta kunshi gundumomin Kankiya da Rimaye, ko shakka babu za mu dade muna tuna tare da yin addu`o`in alheri ga mai girma Kankiyan Katsina Alhaji Musa Hassan Sada, bisa ga ayyukan alheri da ci gaban da ya kawo ga mutanen Karamar Hukumar baki daya. Alal misali bayan zuwansa kan karagar mulki, tare da taimakon wasu mutanen Karamar Hukumar Kankiya, Kankiyan ya kafa wani kwamiti da ya jagoranta da suka kai ziyara dukkan fadin Karamar Hukumar. Wancan ziyara ita ta bude musu idanu a kan irin mawuyacin halin tabarbarewar da fannin ilimi ya shiga, ilimin da shi ke babbar sana`a ga kusan kowane Bakatsine. Ayarin kuma ya ga irin matsalolin tattalin arziki da na zamantakewa da talakawan Karamar Hukumar suke ciki.

A takaice, wannan ziyara, ita ta haifar da mai girma Kankiyan Katsina da taimakon `yan Kwamitinsa irin su Malam Sanusi Imam da Alhaji Dalha Kankiya da Alhaji Ahmed Bala Lankiya da Alhaji Aliyu Musa Dangiwa Sakataren farko na Kugiyar Kwadago ta Kasa wato NLC da Injiniya Muhammad Sani Adamu, da sauransu, suka kafa wata kungiya da aka sa wa suna Kungiyar ci gaban Kankiya, wato (KANKIYA DEBELOPMENT INITIATIBE), a takaice KyDi, kungiyar da ba tare da  bata lokaci ba aka yi mata kundin tsarin mulki sannan kuma aka yi mata rajista da Hukumar yi wa kamfanoni rajista.

Samuwar haka ta sanya a ranar 5 ga watan Mayun 2011, Kankiyan Katsina Alhaji Musa Hassan Sada da takwaransa na Rimaye marigayi Dan Isan Katsina Alhaji Yakubu Kankiya da wadancan mutane da na ambata a sama da sauran `yan Kwamitin Zartarwar kungiya suka kira wani taro a Kankiya a karkashin jagorancin Uban kungiya na farko Alhaji Muhammadu Lawal Kaita, inda aka kaddamar da Asusun neman taimakon Naira miliyan 100. A wajen wancan neman taimako an samu gudummuwar kudi da suka kai Naira miliyan goma da rabi (N10,500,000), amma daga bisani Naira miliyan bakwai suka shiga lalitar kungiya, sauran miliyan uku da rabi har yanzu ana bi-biya.

Da wadancan kudade ne, zuwa yanzu kungiyar KyDi ta fara wasu ayyukan alheri ga mutanen Karamar Hukumar wato na gundumomin Kankiya da Rimaye. Alal misali, a tashin farko an ba da bashi marar ruwa na N500,000, ga matan gundumomin biyu su 50, masu kananan sana`i, inda kowace ta samu Naira dubu goma-goma.

Rahotanni zuwa yanzu sun tabbatar da samun biyan wannan bashi da kashi 98 daga cikin 100.

A shiri na biyu an sake ba mutane 44, har N440,000, shi ma wannan bashi an samu nasarar biyansa da fiye da kashi 77 cikin 100. Baya ga basussuka iri-iri da kungiyar ta bayar ga masu bukata, da suka bunkasa  sana`o’insu daban-daban.

Ta fannin ilimi bayan himmatuwa da kungiyar KyDi, ta yi a kan kara samun shigar dalibai makaratun firamare, ta kuma kebe N500,000, da ta gina ajujuwa bibbiyu a makarantun gwaji na garuruwan Rimaye da Doka. Yin wannan aiki ya sa Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, wato UNICEF, ya shigo zai yi aiki kafada-da-kafada da kungiyar ta KyDi don tallafawa fannin ilimin firamare a yankin.

Akwai dimbin ayyuka kamar na koya wa mata sana`o`in hannu da dukufa wajen wayar da kan jama`a a kan illolin sha da fataucin miyagun kwayoyi da suka zama ruwan dare a kasar nan da batun sa `ya`ya makaranta da abin da zai sa iyaye su kara kula da dawainiyar ilimi da tarbiyyar `ya`yansu. Akwai ma makarantar koyan aikin Ungozoma da kungiyar ta kuduri aniyar kafawa.

Babban makasadin kafa kungiyar KyDi, kamar yadda  Kankiyan Katsina yake nanatawa shi neman samun hadin kan dukkan mutanen Karamar Hukumar Kankiya, don haka ma taken Kungiyar yake “HADIN KAI DON CI GABA.”

Akwai ma nade-naden mikaman sarautun gargajiya daban-daban da Kankiyan Katsina ya yi ga `yan uwansa da makusantan fada da ma sauran talakawan kasarsa, wanda ba a taba yin mai yawa irin sa ba a tarihin masarautar ta Kankiya, kuma duk ba wani abu mai girma Kankiyan Katsina yake son ya cimma ba, illa yadda zai jawo mutanensa kusa da shi, ta yadda za a samu hadin kan kowa, wanda sai da hadin kai za su ci gaba.

A kullum maganar Alhaji Musa Hassan Sada kenan, ko da a wannan biki na cikarsa shekaru 10 abin da ya yi ta nanatawa shi ne Hadin kai! Hadin kai!! Hadin kai!!! Don haka akwai bukatar kowa ya kama masa don a gudu tare a tsira tare. Ina dai sake cewa Allah ja zamanin Kankiyan Katsina Alhaji Musa Hassan Sada a cikin imani da koshin lafiya, amin summa amin.