✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yi hattara da irin shukar da aka canza wa halitta – Farfesa Dadari

Aminiya: Wani kamfani mai suna Monsanto na Amurka, wanda yanzu yana gwajin wasu irin shuka na kayayyakin amfanin gona a nan Najeriya. Shin mene ne…

Aminiya: Wani kamfani mai suna Monsanto na Amurka, wanda yanzu yana gwajin wasu irin shuka na kayayyakin amfanin gona a nan Najeriya. Shin mene ne cikakken bayani kan canza halittun irin shuka da wannan kamfani ke yi? 

Farfesa Dadari: Wato shi dai wannan kamfani na Monsanto wanda mallakar kasar Amurka ne ya kware a duniya wajen canja halittun kayayyakin irin shuka na masara da shinkafa da wake da auduga da kasuwancin sayar da irin shuka na kayayyakin amfanin gonar ga manoma a kasashen duniya. Kuma wannan kamfani yana da rassa a kasashen duniya. Idan wannan kamfani ya canjawa irin shuka halitta, ya kanyi mu’amala da gwamnatin kasa, domin ta biya shi diyya. Daga nan gwamnati ta sayi irin shukar da ya canzawa halittar ta sayarwa da talakawa manomanta. 

Misali kasashen Afirka ta Kudu da Sudan da Masar da Burkina Faso da Kenya da Botsuwana duk sun kulla dangantaka da wannan kamfani kan irin shuka na masara da auduga da sauransu da aka canja masu halitta. To, yanzu Nijeriya ma  ta shiga sahu na kulla dangantaka da wannan kamfani,  ma’aikatar binciken nau’in rayuwa da samar da hasken zaman lafiya dake Abuja an bata mallakar bayar da lasisin a shigo da wannan kamfani ayi gwaji kan irin shuka na kayayyakin amfanin gonar da aka canja masu halitta a nan Nijeriya.

Akwai irin shuka na masara da wake, an riga an amince da su. Yanzu ana yin gwajin irin auduga ne, domin a gano shin ya kamata a karbi irin audugar ko ayi watsi da shi. Abin nazari shi ne wannan kamfani yana tallata kayansa ne kan cewa idan aka yi amfani da shi, za a sami bunkasar yawaitar kayayyakin abinci domin jama’ar duniya sun yi yawa. Don haka ana bukatar a ciyar da su ta hanya mafi sauki da dacewa. 

To a bangare daya kuma idan muka dubi sinadaran da ake amfani da su, wajen canja halittun irin shukar amfanin gonar da wannan kamfani yake amfani da su, kamar wake da masara da auduga. Ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi binciki ta gano mene ne illolin wadannan sinadarori da wannan kamfani yake amfani da su wajen canza halittar irin shukar? Domin akwai illoli a cikin irin sinadaran da ake amfani da su, wajen canja irin wadannan halittu wadanda za su yi kamar shekara 10 kafin su fito.  

Aminiya: Kamar wadanne irin illoli wannan irin shuka da aka canja halittarsa ke dauke da su, kuma a wadanne kasashe ne aka gano wadannan illoli? 

Farfesa Dadari: Kamar a kasar Japan sai da aka kai wannan kamfani kotu, a inda aka nemi diyar dala biliyan 2 saboda mutane sama da dubu 2 sun hallaka sakamakon cin abincin da aka samar da irin wannan shuka da aka canja wa halitta da wannan kamfani ya yi. Haka Indiya akwai manoman da suka rika hallaka kansu, domin sun yi asarar audugar da suka noma, saboda audugar da suka noma ta ki yin ‘ya’ya sakamakon amfani da irin. 

Ni kaina na je Barazil a shekara ta 2016, na ga sun shuka irin wannan shuka da aka canja masa hallita na ga wajen da sai da aka yi feshi sau 25 kafin audugar ta yi ‘ya’ya. Alhalin irin audugar da muke shukawa a nan Najeriya sau 3 ko 4 muke yin feshi.  Haka kuma a Barkina Faso a farkon shekarar nan, sun kai wannan kamfani kotu, saboda audugar da suka noma ta mutu sakamakon amfani da suka yi, da irin shuka na wannan kamfani. 

Don haka wannan iri da aka canja masa halitta yana da illoli, domin da farko manomi zai ga kamar yana da alheri, amma shekara ta daya zuwa shekara ta biyu zuwa shekara ta uku, sai abin ya zama wani bala’i. Manomi zai fara ganin bala’i tun daga gonarsa har ya zuwa ga jikinsa sakamakon cin abincin da ya yi na irin wannan shuka da aka canja halittarsa. 

Don haka idan har gwamnatin Najeriya ta yarda za ayi amfani da wannan irin shuka da aka canzawa  halitta to ta sani cewa akwai babban kalubale a gabanta. Don haka muna yi wa gwamnatin Najeriya hanunka mai sanda kan ta yi nazari da bincike kan illolin wannan irin shuka da aka canzawa halitta. 

Kuma wata matsala a Najeriya ita ce, sai ka ga mutanenmu suna zuwa suna shigo da wasu irin shuka daga kasashen makota, suna amfani da su. Irin wannan kuskure za a iya kawo mana wani abu wanda zamu zo muna dana sani. Saboda haka muna kira ga manoma su rika amfani da irin shukar da muke da su a Najeriya, wadanda cibiyoyin binciken aikin gona na jami’o’inmu suka yi bincike a kansu.

Aminiya: To me zaka ce kan zargin da wasu ke yi, cewa yawancin cutukan da ake fama da su a kasar nan sakamakon cin abincin amfanin gonar da aka yi wa feshi da kuma takin zamani? 

Farfesa Dadari: Wadannan maganganu da mutane suke yi gaskiya ne. Domin hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ce a koma amfani da takin gargajiya da magungunan da aka yi da itatuwa wadanda za su rika kashe kwari wajen yin noma a duniya. Domin su ba su da illa, amma takin zamani duwatsun da ake amfani da su wajen yinsa, suna taruwa su yiwa mutum illa. Suna kawo ciwon hawan jini da ciwon suga suna sanya mata su rika zubar jini da barin ciki da dai sauran cututtuka. Duk ana danganta wadannan cututtuka da suke damun mutane da irin abincin da mutane suke ci. Saboda amfani da irin wadannan sinadarori da ake amfani da su wajen yin magungunan fashi da takin zamani. 

Ka ga yanzu Chana sun koma amfani da sinadarorin tsirai saboda ba su da illa ga dan adam. Sun daina amfani da irin wadannan sinadarai masu daskarewa a jikin dan adam wajen yin aikin nomansu. 

Yanzu a Ingila da sauran manyan kasashen duniya amfanin gonar da aka noma, da takin juji ya fi amfanin gonar da aka yi da takin zamani tsada. Saboda sun ce amfanin gonar da aka yi da takin juji ba shi da illa ga dan adam. 

Yadda zaka san cewa muna da matsala a Najeriya shi ne feshin maganin da ake yi. Idan ka je kasuwanni zaka ga yadda ake sayar da wadannan magunguna a fili kusa da mai tuyar kosai ko mai tsire iska na diba. Idan mutum ya ci wannan abinci ta ya ya zai sami lafiya? An ce idan mutum zai yi feshi ya sanya riga ya rufe bakinsa ya sanya gilas. Idan ya gama ya sha gwangwanin madara don ya rage karfin maganin. Saboda haka mutane su yi taka tsantsan da irin wadannan kayayyakin feshin magungunan ciyawa da takin zamani a wajen noman da suke yi. Don  haka muna kira ga gwamnati da masu hanu da shuni a kasar nan, su karfafa ma’aikatu da cibiyoyin binciken aikin noma na kasar nan, ta hanyar ba su kudade. Domin a cigaba da bincike tare da samar da sinadaran da ba su da illa ga harkokin noma a kasar nan.

Aminiya: A makon da ya gabata an bude wani babban kamfanin kaji mai suna Olam a Jihar Kaduna. Wace irin gudunmawa ka ke ganin wannan kamfani zai bayar wajen bunkasa harkokin noma a kasar nan? 

Farfesa Dadari: Wato wannan kamfani na Olam ya dade a Najeriya kuma wannan kamfani wanda hedikwatarsa take a kasar Koriya, yana da rassa da dama a duniya. Babu shakka wannan kamfani zai baiwa dubban matasan Najeriya aikin yi. Kuma wannan kamfani zai sayi kayayyakin amfanin gona kamar masara da waken soya. A takaice wannan kamfani zai iya saye kusan dukkan masarar da aka noma bana a Najeriya.

Aminiya: A halin yanzu amfanin gonar da manoma suka noma ya fara shiga kasuwanni, inda farashinsu ya fadi. Anan wane kira ko jan hankali zaka yi ga manoman kasar nan game da wannan al’amari?

Farfesa Dadari:  Wannan samun abinci da aka yi wata babbar nasara ce, domin mu da ma bukatarmu ita ce abinci ya samu ya yawaita a kasar nan. Idan abinci ya yawaita zamu iya dauka mu kaiwa makotanmu mu sayar da daraja. Ada ai ba mu da abinci a kasar nan, don haka ake daukar kudaden Najeriya ana sayo abincin, amma yanzu zamu rike kudinmu kuma mu sami kudaden waje ta hanyar samun wannan abinci da aka yi a bana. Don haka wannan abinci da aka noma a bana, zai kawowa Najeriya dimbin kudade daga waje. Don haka a bana za a sami koshi a kasar nan kuma za a sami kudaden waje ta hanyar wannan abinci da aka noma. 

Yanzu mutanen da suke ihun cewa Najeriya an shiga yunwa, za su yi shiru. Don haka muna fatar gwamnati za ta tanadi yadda za a fitar da rarar wannan abinci da aka noma, zuwa kasashen waje. Kuma muna kira ga manoma kada su ji tsaro sakamakon faduwar fashin kayayyakin abinci, komai zai gyaru ya yi kyau in Allah Ya yarda.