Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

A yi nazari kan matsalolin da ke tare da zaben raba-gardama

Ganin yadda ake yawan samun tashe-tashen hankula da kuma yin magudi a lokutan zabubbuka a kasar nan musamman a zaben gwamnonin da aka yi a ranar Asabar 9 ga watan Maris ne ya sa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sake gudanar da zaben raba-gardama a wasu jihohi 6 na kasar nan.

Jihohin sun hada da Kano da Sakkwato da Bauchi da Filato da Adamawa da kuma Benuwai. Yadda  aka samu tsaiko wajen isar wasu kayayyakin zabe a wasu mazabu da yadda na’urar tantance katin zabe ta ki aiki a wasu mazabu na daga cikin dalilan da suka sa Hukumar INEC ta sake yin zaben raba-gardama a irin wadannan wurare.

ADVERTISEMENT

A zaben sanatoci da na ’yan Majalisar Wakilai ma an samu matsalolin da suka sa aka gudanar da zaben raba-gardama a wasu sassan kasar nan.

Sashe na 26 da na 53 na Dokar Zabe ya nuna ana sake gudanar da zaben raba-gardama ne a duk lokacin da aka lura yawan kuri’un da ba a kada ba saboda wasu matsaloli zai iya canja sakamakon da aka fitar.  Ke nan idan ’yan takara biyu ko uku da ke sahun gaba aka lura yawan kuri’un da ba a kada ba za su iya sa wani daga ciki ya samu nasara, to ya zama wajibi a gudanar da zaben raba-gardama.

ADVERTISEMENT

A bisa irin wannan dalili ne ya sa Hukumar INEC ta gudanar da zaben raba-gardama a jihohi 6 in ban da Jihar Adamawa a ranar 23 ga watan Maris din bana. Sai a ranar Alhamis 28 ga Maris ne aka gudanar da na Jihar Adamawa.  Hakan ya faru ne saboda yadda Jam’iyyar MRDD ta shigar da kara inda ta kalubalanci sahihancin zaben ganin yadda Hukumar INEC ta yi kuskuren cire alamar jam’iyyar a takardun kada kuri’a.  Daga baya ne kotu ta yi watsi da karar da jam’iyyar ta shigar bayan ta lura jam’iyyar ma ba ta da dan takarar Gwamna don haka ba ta ga dalilin da zai sa  ta kai kara ba.

Kawo yanzu an kammala zaben raba-gardama a dukan jihohi 6 da aka gudanar.  Sai dai a yayin da aka tabbatar an yi zaben lami lafiya a jihohin Filato da Binuwai, rahotanni sun ce an samu tashin hankali a yayin zaben raba-gardamar a Jihar Kano.  Masu sanya ido game da yadda zaben ya gudana a gida da waje sun nuna yadda aka rika amfani da ’yan bangar siyasa wajen yin magudi da coge a yayin zaben a Jihar Kano.  Wannan ya sa ratar kuri’a dubu 26 da dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP ya bayar tunda farko suka bi ruwa bayan an sake zaben raba-gardama inda jam’iyyar APC ta samu galaba.  Daga nan ne Jam’iyyar APC ta samu nasara bayan ta samu kuri’u mafi rinjaye. A Jihar Sakkwato ma an yi gumurzu a yayin gudanar da zaben na raba-gardama, inda da kyar Jam’iyyar PDP ta samu nasara da tazarar kuri’u 341.  Wannan shi ne mafi karancin tazara da wata jam’iyya ta bayar a yayin zaben na bana a duk fadin kasar nan.

Sannan an samu canjin gwamnati a jihohin Bauchi da Adamawa.  A zaben gwamnoni da aka yi a ranar 9 ga watan Maris, 2019, gwamnonin da ke kan mulki ne suke baya, kuma bayan an sake gudanar da zaben raba-gardama sai suka fadi a zaben.

Kodayake ana gudanar da zaben raba-gardama ne don ganin an shawo kan wasu daga cikin matsalolin da ke tattare da gudanar da zabe, a daya bangaren kuma gudanar da zaben raba-gardamar yana tattare da irin nasa matsalolin.  Alal misali Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi zargin ’yan takarar gwamnoninta ne suke kan gaba a jihohi biyar daga cikin 6 da Hukumar INEC ta ce zaben bai kammalu ba. Sannan wasu jam’iyyu kan yi amfani da damar wajen ganin an soke da kuma sake zabe a duk jihohi ko wuraren da suke ganin za su fadi zabe, da hakan ke sa su nemi a sake gudanar da zaben raba-gardama.  Sannan akwai zargin yadda shugabannin da ke kan mulki suke amfani da wadansu batagari a Hukumar INEC ko jami’an tsaro wajen yin magudi a lokacin da ake gudanar da zaben raba-gardamar.

Matsalolin da ke sanyawa ana sake yin zaben raba-gardama sun hada da rashin isar kayayyakin zabe da wuri da yadda masu kada kuri’a suke kin yarda a yi amfani da na’urar tantance katin zabe da kuma yadda ake amfani da ’yan bangar siyasa wajen kawo cikas a yayin gudanar da zaben da kuma yadda wadansu ke sace akwatunan zabe da sace ko kona sakamakon zabe da sauransu.

Jami’ar Hukumar INEC da ta lura da jihohin Neja da Kaduna da Filato da Babban Birnin Tarayya, Abuja a zabubbukan da aka kammala kwanan nan Misis Antonia Okoosee-Sumbine ta ce sake gudanar da zaben raba-gardama ba laifi ba ne, amma laifin shi ne yadda wadansu batagari suke amfani da damar wajen tayar da hankali da yin magudi don ganin sun samu nasara ko ta wace hanya.

Ta ce ganin yadda ake yawan samun matsaloli kama daga sace akwatunan zabe da cin mutuncin jami’an da ke lura da zaben ko masu kada kuri’a da tashe-tashen hankula da kuma kashe-kashe a wasu wurare, ya kamata Hukumar INEC da jami’an tsaro su dauki darasi don a shawo kan al’amarin a nan gaba. Muna kira ga Hukumar INEC da ta sake nazari game da dalilan da suke sanyawa a sake gudanar da zaben raba-gardamar.  Wadansu bata-gari suna amfani da damar ce da zarar sun lura sun kama hanyar faduwa zabe, sai su kawo cikas don ganin an soke zaben ko kuma an sake gudanar da zaben raba-gardama.

Don haka Hukumar INEC ta sake nazari game da dokar da ta sa ake gudanar zaben raba-gardama don a kauce wa damar da wadansu ke amfani da ita wajen lashe zabe ko ta halin ka-ka.