✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Zamantakewar Soyayya: Shin Wace Ce Mace Tagari?

Masu salon Magana suna cewa, kowa yana son mai kyau sai dai idan bai samu ba. Burin kowane namiji shi ne ya samu mace tagari.…

Masu salon Magana suna cewa, kowa yana son mai kyau sai dai idan bai samu ba. Burin kowane namiji shi ne ya samu mace tagari. Sai dai ga dukkan alamu wasu bas u san ma wace ce mace tagari ba. Idan ba ka san yanayi da halayen mace tagari ba, saurari abin nda Sunusi musa zai gaya maka a nan:

Sunusi Musa Ciyaman Kano 08020800420:
Mace tagari, ita ce wacce ta mallaki wadannan halaye guda goma sha daya, kamar haka: 1-Idan mijinta ya kale ta zai ji farin ciki ya lullube shi. 2-Ita ce wacce take gaggawa wajen cika umurnin mijinta. 3-Ita ce wacce take matukar kiyaye duk abin da zai bata wa mijinta rai. 4-Ita ce wacce take dagewa wajen bautar Ubangijinta. 5-Ita ce wacce ba ta wasa da duk wani hakki na mijinta. 6-Ita ce wacce duk lokacin da mijinta ya yi fushi, ba ta samun kwanciyar hankali har sai ta yardar da shi. 7-Ita ce wacce take kiyaye duk wani sirrin mijinta. 8-Ita ce wacce idan mijinta ba ya nan take kiyaye mutuncin kanta, da kuma dukiyar da ya bari a gida. 9-Ita ce wacce take kulawa da tarbiyyar mijinta da ’ya’yansa koda ba ita ce ta haife su ba. 10-Ita ce wacce take matukar girmama iyayen mijinta, kamar yadda take girmama nata iyayen kuma take kyautata wa ’yan uwansa ba tare da tsangwama ba. 11-Ita ce wacce take zama da makwabtanta da kishiyoyinta cikin tsoron Allah da kyautatawa, ko da su suna munana mata.
***
Wai-wai-wai! Garin dadi na nesa wai angulu ta leka masai! Duk macen da ta mallaki wadannan halaye, babu shakka ta mallaki halayen ’yan Aljanna. Allah Ka sanya mu kasance nagari a halayya da dabi’a, mazanmu da matanmu. Amin. – FDk.
***
Ibrahim Kabara, 08188966748:
Wai me ya sa wasu ’yan matan ko zawarawa ke tsananin kamuwa da son mutumin da ba su taba gani ba da ido? Ta waya kawai suke magana?
***
Dalili daya ne, wato abin da Hausawa ke kira da hangen Dala ba shiga birni ba! A wannan batun kuma, ba mata kadai abin yake shafa ba, domin kuwa karfe daya ba ya amo. Kamar yadda ake samun wasu mata na fadawa cikin irin wannan yanayi, haka ake samun wasu mazan ma suna afkawa. Wasu ana dacewa har a kai ga aure, wasu kuwa abin rikidewa yake ga zamba da yaudara. Allah Ya kiyaye. – FDk.
***
Baban Huzaifa, 08180391941:
FDk na Aminiya, ina mika sakon gaisuwata gare ku, sannan ina son wannan fili na Dausayin kauna, domin samun haske wajen gudanar da soyayya a tsakanin ’yan mata da samari. Na gode.
***
Mu ma mun gode sosai, Baban Huzaifa. – FDK
***
Fatima Musa Abubakar Zariya, 08145675122:
Ina muku fatan alheri da fatan kuna lafiya. To, a gaskiya ya kamata maza su daina cutar mata kuma mata su ma su daina cutar maza saboda kada su shiga irin halin da na shiga. Saboda na bata da wani saurayi wanda ya taba cutata. Da fatan kun gane kuma ina rokonku da ku yi mini addu’ar samun saurayi nagari.
***
Haka dai ya kamata a rika yi, kowa ya kula da kansa, kada ya cuci wani kuma kada ya amince a cuce shi. Malama Fatima, maimakon ki roki addu’ar samun saurayi nagari, ai kamata ya yi ki ce mijin aure nagari ko? To Allah Ya ba ki miji nagari, mu kuwa mu zo Zazzau mu sha biki. – FDk.
***
Husna Abutah Katsina, 09038386296:
FDk, ni Husna na fada tarkon soyayyar Habib ta dalilin Aminiya, a filin Dausayin kauna. Yanzu haka mun kwashe shekara uku ba mu taba ganin juna ba. Yana Kano, ina Katsina. Muna gaisawa a Social Media amma bai taba sanya hotunansa ba bare ya turo mini. A haka nake soyayya da shi kuma wallahi ina matukar kaunarsa. ’Yan uwana, ina mafita?
***
Haba malama, shekara uku ana abu daya? To, Allah Ya kyauta, domin ina guje maki kada ki fada komar yahoo-yahoo! Ni dai ina ganin abin da kike ciki shi ne Makauniyar Soyayya, idan ba haka ba, ina Kano, ina Katsina? Idan dai soyayyar gaskiya ce ai kuwa ya dace a ce cikin shekara uku ya gana da gidanku! Ruwa a cokali dai ya ishi mai hankali wanka! – FDk.
***
Ibrahim Makurdi, 08069276386:
FDk, bayan tafiyar Fati, na yi kokarin ta dawo amma ta furta mini cewa ina shiga rayuwarta. Daga nan sai Ummulkhairi ta zo ta share mini hawaye amma kuma sai ga Fati ta ce mini wai za ta bata soyayyarmu da Ummi. Mece ce mafita FDk?
***
Mafita daya ce, ka rike soyayyarka da karfi da gaskiya da Ummi. Idan ka yi haka, babu makircin da Fati za ta iya yi don raba ku, tun da dai ita ta ce ba ta yi, to kuma ina ruwanta da wadda ta ce ta ji kuma ta gani? – FDk.
***
Samir Lawal Yeldu, 08060379772:  
FDk, ina mika sakon gaisuwata ga duk wanda ke cikin wannna dandali na Dausayin kauna. Ni dai bako ne a wannna dandali, na turo sakon gaisuwa ne kamin makon jibi ni ma na ce wani abu.
***
Madalla Malam Samir, muna yi maka lale marhabin da shigowa kuma Allah Ya sa mu dace, amin. – FDk.