✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba da Ganduje: Yadda ta kaya a zaman farko a Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta yi zaman farko kan karar da PDP da dan takararta na Gwamnan Jihar Kano Abba Yusuf suka daukaka zuwa gabanta suna…

Kotun Daukaka Kara ta yi zaman farko kan karar da PDP da dan takararta na Gwamnan Jihar Kano Abba Yusuf suka daukaka zuwa gabanta suna kalubalantar zaben Gwamna Abdullahi Ganduje.

A Ranar 2 ga Oktoba ne Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano ta tabbatar wa  Gwamna Abdullahi Ganduje nasarar da ya samu, amma Jam’iyyar PDP da Abba Yusuf suka daukaka kara kan ba su gamsu da hukuncin da kotun farko ba.

Kotun Daukaka Karar da ke Kaduna ta ce za ta yanke hukunci a kan karar.

Bayan kammala sauraron kowanne bangare, kotun, mai alkalai biyar a karkashin jagorancin Mai shari’a, Tijjani Abubakar, ta ce za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci. Jam’iyyar PDP da Abba sun samu wakilcin ayarin lauyoyinsu a karkashin jagorancin Adegboyega Awomolo (SAN), sai Joseph Dawudu (SAN) ya wakilci Hukumar INEC), yayin da Offiong Offiong (SAN) da Aled Iziyon (SAN) suke wakiltar jam’iyyar APC.