✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba El-Mustapha ya gargadi mutane kan zabe

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Abba El-Mustapha ya gargadi jama’a cewa su fahimci cewa akwai rayuwa bayan zabe, don haka kada su yarda zabe ya sanya…

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Abba El-Mustapha ya gargadi jama’a cewa su fahimci cewa akwai rayuwa bayan zabe, don haka kada su yarda zabe ya sanya su rika gaba da juna.

Jarumin wanda ake kira da ‘Abba Ruda’ ya yi gargadin ne a shafinsa na Instagram a ranar Lahadin da ta gabata.

Jarumin ya bukaci ’yan Najeriya su rika siyasa mai tsabta da mutunta juna.

Ya ce, “Akwai rayuwa bayan zabe. Kada ka bari harkar siyasa ta hada ka rigima da wani. Ka yi siyasa mai tsabta cikin mutunci da girmama juna.”

Jarumin ya kuma bukaci ’yan Najeriya kada su rika tursasa cewa sai an bi ra’ayoyinsu.

Ya ce, “Ka girmama ra’ayin waninka shi ma ya girmama naka. Ta’addanci da bangar siyasa ba su dace da duk mutum mai hankali ba.”

Abba Ruda ya bukaci kada mutane su bari wani dan siyasa ya yi amfani da su wajen tayar da tarzoma yayin kamfe da lokacin zabe ko kuma bayan zabe.

“Kada ka bari wani dan siyasa ya yi amfani da kai wajen tayar da tarzoma a cikin al’umma. Kada ka yi zaton ’yan siyasa suna amfani da kai ne don ci gaban kasarka, suna amfani da kai ne su mulke ka don jin dadin rayuwarsu. Ubangiji Allah Ya sa mu dace, amin,” inji shi.