Da Dumi Dumi

Abba Sarki Sharada: Dan gwagwarmayar nakasassu ya kwanta dama

A ranar Lahadin da ta gabata ce Allah Ya yi wa dan gwagwamayar nan mai fafutukar tabbatar da cewa nakasassu sun samu ana damawa da su a Jihar Kano da ma fadin kasar nan rasuwa.

Aminiya ta kalato cewa Marigayi Abba Sarki ya samu lalura sakamakon gwajin maganin cutar sankarau da Kamfanin Pfizer ya yi a kan wasu marasa lafiya da ke fama da lalurar sankarau wanda ya janyo yara da yawa suka rasu, wasu kuma suka samu lalurar nakasa.

Abba ya rasu sakamakon tashin farat daya da cutar Asma ta yi masa a daidai lokacin da suke dawowa daga ziyarar wani danu wansu da ya angwance.

Kafin rasuwarsa Abba ya yi ta fadi-tashi wajen ganin an tabbatar da dokar kariya ga nakasassu, musamman dokar da Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya sanya wa hannu a ranar 4 ga watan Disambar bara.

A hirarrakin da marigayin ya yi a baya, ya bayyana cewa ya jajirce wajen ganin an samar da dokar nakasassu ne domin yin duba da yadda dokar za ta zame gata ta hanyar sama musu dukkanin hakokokinsu da ba su samu wanda suka hada da samun ilimi kyauta da batun ba su guraben ayyuka a ma’aikatun gwamnati da hukumomi da sauransu.

ADVERTISEMENT

A watahira da Abban ya yi a kan bikin Ranar Nakasassu ta Duniya, ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda Gwamnatin Tarayya da  na jihohi suka gaza aiwatar da dokar.

Hajiya Asma’u Usman ita ce mahaifiyar marigayi Abba. Ta shaida wa Aminiya cewa ta yi rashin da mai kula da ita, mai zumunci. “Babu shakka Abba yaro ne mai son ’yan uwansa da kokarin yin zumunci. Kin ga a halin da yake amma duk inda wani abu na ’yan uwa ya taso, Abba yana kokari sai ya ga ya halarta. Shi mutum ne mai son zaman lafiya tun yana yaro ba shi da abokin fada.”

Ita ma wataabokiyaraikin Abba a kungiyarsa ta Kanawa Educational Forum, Malama Nafisa Ibrahim ta bayyana marigayi Abba a matsyain mutumin da ba ya gajiyawa akan abin da ya sa gaba.

Shi ma Shugaban Gamayyar Kungiyar Nakasassu ta kasa reshen Jihar Kano Injiniya Musa Muhammad Shaga ya bayyana cewa marigayin ya yi kokari wajen ganin an samar musu da dokar a Jihar Kano don haka nakasassu ba za su taba mantawa da marigayn ba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya