Search
Subscribe
Abdulaziz Yari ya zabi wanda zai gaje shi

Abdulaziz Yari ya zabi wanda zai gaje shi

Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya zabi Kwamishinan Kudin Jihar Zamfara, Mukhat Idris Kogunan Gusau a matsayin wanda zai gaje shi.

Kwanakin baya Aminiya ta ruwaito cewa Mataimakin Gwamnan Ibrahim Wakkala ne zai tsaya takarar gwamnan, sannan shi kuma gwamnan na yanzu zai tsaya takarar sanata, a wata irin yarjejeniya da ake tunanin an kulla tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Yariman Bakura da kuma gwamnan na yanzu Yari.

A tsarin, an ruwaito cewa Wakkala a matsayinsa na hannun daman Sanata Yarima, shi ne zai maye gurbin Gwamna Yari, sannan kuma shi Gwamna Yari yam aye gurbin Sanata Yarima a Majalisar Dattawa.

Amma yanzu kwatsam, sai Daily Nigerian ta ruwaito cewa an samu sauyi a tsarin. Sannan kuma Minsitan Tsaro, Mansur Dan Ali ma ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar gwamnan na Jihar Zamfara.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin