Search
Subscribe
Abdullahi Kagara: Marayan da ya fita da yabo a jami’a kuma ya mallaki kamfanoni

Alhaji Abdullahi Abubakar Abba Kagara

Abdullahi Kagara: Marayan da ya fita da yabo a jami’a kuma ya mallaki kamfanoni

Hausawa sun ce babu maraya sai rago; wannan shi ne abin da rayuwar Alhaji Abdullahi Abubakar Abba, ta nuna.  Matashin mai shekara 34 da aka fi sani da Abdullahi Kagara an haife shi ne a Kagara a Jihar Neja, inda ya yi fadi-tashi a fannin karatu har ya yi digiri na biyu bayan ya kammala na farko da kyakkyawan sakamako mai daraja ta daya (First Class) a Kimiyyar Kwanfuta, a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato. A yanzu ya mallaki kamfanin man fetur da na sufuri mai suna Abba 2 Worldwide Serbice Ltd da kuma kamfanin gine-gine da sadarwa mai suna Alushat Technology Limited:

Wane ne Abdullahi Kagara?

Ni mutumin Kagara ne da ke Jihar Neja, matashi ne dan shekara 34. Na yi firamare a Central Primary School da ke Kagara a Karamar Hukumar Rafi a Jihar Neja, na yi Sakadaren  Ahmadu Attahir da ke garin Kagara, sannan na yi Difloma a Kimiyyar Kwamfuta a Sokoto State Polytechnic. Na yi karatun digiri a Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato a shekarar 2010, sannan na yi digiri na biyu a Alison Unibersity College da ke kasar Ireland.

A bangaren iyali fa?

A bangaren iyali zan iya cewa ni ne iyalin, domin ba wadansu sanannu ba ne, amma dai ina da mace da ’ya’ya biyu, Hafsat da Fatima, sannan mahaifiyata tana raye.

A yanzu za a iya cewa ka samu daukaka tun da kana cikin matasa a Arewaa da ake ji da su, yaya ka yi fadi-tashi a rayuwa har ka kawo wannan matsayi?

To, lallai ni maraya ne, na tashi cikin kuncin maraici, wanda samun irin maraicina ma yana da wahala. An haife ni mahaifina yana raye, amma ya rasu ina da shekara hudu a duniya. Tun daga wancan lokaci na samu kaina cikin tashin hankali, babu abin da za a ci, kudin makaranta da hidimar rayuwa babu, mahaifiyata ba ta da karfi, amma haka cikin ikon Allah ta hanyar fadi-tashi da na rika yi ne, ta hanyar in yi wannan, in yi wancan na samu dogaro da kaina. Domin babu wata karamar sana’a da ban yi ba- kafinta, gyaran takalma, tallar kwarya da dinki  da gadi duk na yi, har Allah Ya sa na kammala firamare ba tare da tallafin kowa ba sai na Allah.

Na shiga sakandare daga JSS1 zuwa SS3 dina ma babu wanda zai ce ya taimake ni da abin da ya kai darajar Naira dubu daya, nike zuwa in yi tallar kuli-kuli ko zobo da sauransu har na kammala sakandare.

Bayan na kammala sakandare kashina ya fara kwari sai na shiga harkar kwadago, inda nake zuwa gonakin mutane in yi noma a biya ni Naira 200. A wancan lokaci ne na bude wurin buga waya lokacin da Kamfanin MTN da GLO suka shigo ke nan. A cikin wannan hali ne na ga ya kamata in koma makaranta, sai na samu gurbin kwas din Difloma a Kimiyyar Kwanfuta a Polytechnic a Sakkwato, sai na sayar da shagon wayata na biya kudin karatu a shekarar farko. A shekara ta biyu kuma babu kudin rajista, sai na ga a matsayina na maraya bai dace in zauna a gida babu abin yi ba, sai na yanke shawarar in shiga gadi.

A Polytechnic da nake a lokacin ne na samu shugaban masu gadi na sanar shi halin da nake ciki, kuma ina so ya taimake ni ya ba ni gadi a makarantar don in samu abin da zan rufa wa kaina asiri. A nan aka dauke ni, ina karatu, ina gadi, har Allah Ya sa na kammala Difloma.

A lokacin da nake Difloma akwai wata baiwar Allah da muke aji daya, jininmu ya hadu sosai, mahaifinta yana da wadata sai ta rika taimakona har ta sama mini gurbin karatun digiri a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato. A nan kuma sai ta saya mini babur roba-roba, sai na ga ban kai lokacin da zan hau ba, sai na sayar da shi na sayi babur kirar Jincheng, na fara yin acaba a Sakkwato. A ciki nake ci, in sha, in biya kudin makaranta. A haka Allah Ya taimake ni na kammala digirina da sakamako mafi daraja (First Class).

Daga nan me ya faru?

Bayan na kammala digirina a shekarar 2010 sai na je hidimar kasa a shekarar 2011, nan ma sai Allah Ya hada ni da wata mata, inda bayan ta ji tarihin rayuwata sai ta ce za ta sama mini aiki. Shi ne na fara aiki da Bankin Eco, inda aka kai ni Kano, daga nan aka mayar da ni Katsina, na yi aikin banki na shekara daya ne.

Matar da kuka hadu a Sakkwato ko soyayya ce ta hada ku?

Ba soyayya ba ce, mutunci muke, abokiyar karatu ce. Ita kuma mata ta biyun da ta sama mini aiki a kafar sada zumunta ta 2go muka hadu da ita, muna cikin sada zumunci na fada mata ni dan hidimar kasa ne, ita ma ta ce ai tana hidimar kasa, inda a karshe muka gane muna hidimar kasa a Jihar Delta ne gaba dayanmu.

Bayan nan sai me?

Bayan na yi aikin banki saboda ni mutum ne mai son lura da mutane, ina kuma zaman lafiya da abokai, to daga nan ta hanyar aikin banki sai na hadu da masoya na fara harkar canji, na fara da canjin kudin Sefa na Nijar, ina kuma yi wa masu sayar da motoci fito (clearing) har Allah Ya sa idona ya fara budewa a kasuwanci. Na ga ya kamata in ajiye aikin banki in dogara da kaina. Domin na hango cewa a aikin bankin ba zan iya samun abin da nake so ba.

Bayan ka ajiye bankin me koma?

Bayan na fara digirina na biyu ta Intanet (online) sai na fara kasuwanci, inda a shekarar 2012 na bude kamfanina mai suna Abba 2 World Serbice, sannan na shiga harkar man fetur, daga nan na bude kamfanin gine-gine da kwangiloli mai suna Alyusat Technology Limited.

A yanzu ma’aikatan kamfanoninka sun kai nawa?

A kamfanina mai suna Abba 2 Worldwide Serbice ina da ma’aikata 16, sai Alyushat Technology mai ma’aikata takwas, sai dayan mai suna World Wide International Serbice, wanda na hadaka ne mai ma’aikata 21, ni nake biyansu albashi, sannan akwai direbobi 15 da kuma yaran motocinsu, su ba su cikin masu zaman ofis ke nan, sannan akwai daruruwan leburori da sai aikin gine-gine ya taso nake nemansu

Ga shi ka kai ga wannan nasara ta mallakar kamfanoni bayan ka tashi cikin maraici, wane kira kake da shi ga marayu da sauran matasa?

A kowane hali dan Adam ba zai kira kansa maraya ba, idan ka ga maraya to rago ne. Tabbas ni ne shaida a kan haka, domin na tashi ba ni da mahaifi, amma ba zan kira kaina maraya ba a yanzu, don haka ina kira ga matasa Musulmi ko Kirista, komai za su yi da farko su rika sa Allah, su tsayar da gaskiya, domin tana kai mutum matakin nasara. Kuma duk abin da za su yi idan mahaifiyarsu tana raye su taimake ta, duk wahalar da na sha ban yi kasa a gwiwa ba na taimaka mata sosai. Duk abin da zan samo haka za mu ci tare, ko ma garin kwaki ne.

Sannan kada mutum yana matashi ya kashe zuciyarsa, su tashi tsaye su nemi sana’a babu abin da ba za su zama ba, in da rai da rabo. Matasa su rika nazari, sannan su kyautata al’amuransu, su kuma guji sanya kai a cikin halayen banza. Misali da a ce na sa kaina a cikin shaye-shaye ko bin mata da ban kai matakin da nake a kai ba. Na kama mutuncina, na dage wajen karatuna.

Ga shi ka bude wata kungiya ta tallafa wa matasa me ya sa haka?

Na bude kungiyar da ke tallafa wa marayu da marasa galihu, mai suna Orphans Around the World don in taimaki al’umma, saboda na san halin da marayu da marasa galihu suke ciki, saboda ni ma na taba kasancewa a halin da suke ciki.

Shawararka ga sauran jama’a fa?

A kullum ina so mutane su tsayar da gaskiya, su guji shaye-shaye, saboda shaye-shaye na rusa rayuwar mutum, sannan duk wanda suka hadu da shi to su kyautata mu’amala da kuma tsayar da gaskiya. Jama’a su zamanto masu amana da neman na kai, kada mutane su ji kunyar yin karamar sana’a. Jama’a da dama suna sha’awata amma babu karamar sana’ar da ban yi ba, gaskiya matasa su tashi su nemi na kansu. Kada su ce sun kammala digiri ba za su yi karamar sana’a ba.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin