Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Abdullahi Sule kadai ne ya cancanci ya gaje ni – Gwamna Al-Makura

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya ce dan takarar Gwamnan Jihar a Jam’iyyar APC ,Alhaji Abdullahi Sule ne kadai ya cancanci ya gajeshi a matsayin Gwamnan Jihar a zaben da ke tafe.

Gwamnan ya bayyana haka ne a jawabinsa wajen gangamin yakin neman zaben Alhaji Abdullahi Sule da sauran ’yan takarar jam’iyyar a Shiyyar Nasarawa ta Kudu da aka gudanar a garin Karu.

ADVERTISEMENT

Ya yaba wa wakilan Jam’iyyar APC a jihar dangane da hangan nesa da suka yi na zaben Alhaji Abudullahi Sule a matsayin dan takarar jam’iyyar a kujerar Gwamnan Jihar, idan aka yi la’akari da kwarewarsa da kuma sanin ya kamata.

Ya ce abin da ya rage yanzu kawai shi ne al’ummar jihar baki daya su fito kwansu da kwarkwata su zabe shi, domin ba shi damar dorawa daga inda shi ya tsaya, “A yau mun kasance a nan ne don mu nemi goyon bayanku, don ku fito ku zabi dan takararmu na Jam’iyyar APC a jihar nan Abdullahi Sule, don ina tabbatar muku cewa a shirye yake ya dora daga inda na tsaya. Kuma ina so in bayyana muku cewa kasancewar shiyrarku din nan ne ta fi amfana da ayyukan ci gaba da na gudanar a jihar nan a matsayin Gwamna. Kuma a yayin da yau nake shirin barin gadon mulki, babban abin da za ku saka min da shi kawai shi ne ku zabi Abdullahi Sule don a cikin ’yan takarar kujerar Gwamnan jihar nan a yanzu shi ne ya fi cancanta ya maye gurbina. Shi ya sa kuka ga na fito da kaina ana yin wannan yakin neman zabe da ni. Haka su ma sauran ’yan takarar jam’iyyarmu mai tausayin talakawa a shiyyar nan da jiharmu baki daya ina kiranku da ku fito ku zabe su don ba su damar ci gaba da samar muku da romon dimokuradiyya a jihar nan baki daya,” inji shi.

ADVERTISEMENT

A lokacin da yake jawabi, dan takarar Gwamnan Alhaji Abdullahi Sule ya ce ba shakka idan al’ummar jihar suka ba shi damar zama Gwamna a zabe da ke tafe, zai yi koyi ne da salon mulkin ubangidansa Gwamna Umaru Tanko Al-Makura musamman wajen gudanar da ayyukan ci gaba da za su ci gaba da canja rayuwar al’ummar jihar baki daya.