✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abdulmuminu Kofa ya rasa kujerarsa a zaben cike gurbin Kano

Dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Datti Yako ya lashe zaben cike gurbi na Dan Majalisa mai wakiltar mazabun Kiru da Bebeji a jihar…

Dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Datti Yako ya lashe zaben cike gurbi na Dan Majalisa mai wakiltar mazabun Kiru da Bebeji a jihar Kano, inda ya doke abokin karawarsa Abdulmumin Jubril Kofa da ya tsaya takarar a jam’iyyar APC.

Da yake sanar da sakamakon zaben, jami’in hukumar zaben na mazabun Kiru da Bebeji, Farfesa Abdullahi Arabi ya shaida cewa, Datti Yako ya sami kuri’a dubu 48 da dari 6 da 1 inda ya doke Abdulmumin Jibrin Kofa, na jam’iyyar APC inda ya samu kuri’a dubu 13 da dari 5 da bakwai.