Da Dumi Dumi

Abin da azumi yake nufi a shari’ance – Falalu Dorayi

Fitaccen daraktan fina-finan Hausa, Falalu Dorayi ya ce a shari’ance azumi na nufin kame baki da niyyar bauta wa Allah (SWT), sannan bawa ya kiyaye dukkan abubuwan da suke bata azumi kamar cin abinci ko abin sha ko saduwa da iyali daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Daraktan a cikin wata mukala da ya aiko wa Aminiya ya bayyana cewa a cikin wani hadisi Manzon Allah (SAW) yana fada wa sahabbai cewa “Idan Ramadan ya tsaya to ana daure shaidanu, ana bude kofofin rahama da kofofin aljanna, kuma ana rufe Jahannama.”

Dorayi ya bayyana cewa wannan hadisi shi ne hadisi na 1899 a Sahihul Bukhari.

Daraktan ya ce falalar azumi ta hada da kankare zunubin baya, sannan duk wani aiki na bawa mala’iku ki rubutawa, amma azumi na Allah ne shi ke bada sakamakonsa, inda azumi garkuwar bawa ne daga wuta, sannan azumi yana kara tsoron Allah (SWT).

Daraktan ya kuma bayyana cewa hadisi na 1896 a Sahihul Bukhari ya bayyana cewa: “A Aljanna akwai wata kofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi za su shige ta ranar alkiyama, su kadai za su shige ta. Idan sun shiga sai a kulle ta babu wanda zai sake shiga.”

ADVERTISEMENT

Dorayi ya bukaci duk wani mai azumi ya yawaita karatun Kur’ani da sanin fassararsa, ya yawaita kyauta da sadaka ga mabukata, yawaita nafilfili cikin dare da tuba gurin Allah, ya yawaita zikirai da salati ga Annabi (S.A.W), sannan ya yawaita ciyar da masu azumi domin samun irin ladansu.

Daraktan ya bukaci mutane su rika yin sahur saboda alheri ne da kuma falala ga mai azumi.

Ya ce, “Akwai da damanmu da ba sa yin sahur, kuma sahur alkairi ne da falala ga mai yinsa, domin fadin Ma’aiki (S.A.W) Ya ce: “Ku yi sahur, hakika yin sahur akwai albarka a cikinsa”. (Bukhari 1923), don haka mu tashi ko ruwa da dabino mu saka a baki saboda albarkar da annabi ya fada tana tattare da sahur.”

Ya ce a game da bude baki kuwa masu azumi su yi koyi da Manzon Allah (S.A.W) da ya kasance yana bude baki da danyen dabino kafin ya yi sallah, idan bai samu ba sai ya yi da busasshe, idan har bai samu dabinai ba, sai ya debi ruwa ya sha.

Ya shawarci masu azumi su rika karanta: “Zahabazzama`u Wabtallatil Uruku Wasabatal Ajru Insha`allah”, (kishin ruwa ta tafi jijiyoyi sun jike, lada ya tabbata in Allah Ya yarda.).

A karshe Falalu Dorayi ya bukaci masu azumi su zamo masu hakuri da kai zuciya nesa, su guji gulma ko musu ko hayaniya da za ta haifar da zagi. “Bawa ya zama mai tausayi ga ’yan uwansa wajen saye da sayarwa kada a kara kudin kaya. Bawa ya zamo mai nasiha ga mutane gudun kada su afka abin da zai bata azuminsu.”

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya