✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da kasafin kudin Najeriya na badi ya kunsa

A ranar Talatar da ta gaba ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da  kasafin kudin badi na Naira triliyan 10.33 ga Majalisar Dokoki ta…

A ranar Talatar da ta gaba ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da  kasafin kudin badi na Naira triliyan 10.33 ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

Kasafin kudin wanda aka yi wa take da ‘Kasafin tabbatar da ci gaba da samar da aikin yi’ ya dara na bara da kashi 9.7 cikin dari.

An kuma yi kasafin na bana ne a kan hasashen farashin gangan danyen mai a kan Dala 57, inda kuma ake hasashen Najeriya za ta rika fitar da ganga miliyan daya da dubu 860 a kullum. Sannan aka kasafta canjin kudi a kan Naira 305 kan Dalar Amurka daya.

Wannan karon kasafin ya zo cikin sauri, sannan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya ba ministoci mako uku kacal su bayyana a gaban kwamitinsu na Majalisar Dattawa domin kare kasafinsu.

Ga yadda aka raba kudin ga wasu daga cikin ma’aikatu da hukumomi:

  • Majalisar Dokoki – Naira biliyan 125
  • Ma’aikatar Shari’a – Naira biliyan 110
  • Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje – Naira biliyan 262
  • Ma’aikatar Sufuri – Naira biliyan 123
  • Hukumar Ilmi a Matakin Farko (UBEC) – Naira biliyan 112
  • Ma’aikatar Tsaro – Naira biliyan 100
  • Ma’aikatar Aikin Gona – Naira biliyan 83
  • Ma’aikatar Albarkatun Ruwa – Naira biliyan 82
  • Ma’aikatar Ilimi – Naira biliyan 48
  • Ma’aikatar Lafiya – Naira biliyan 46
  • Hukumar Raya Arewa maso Gabas – Naira biliyan 38
  • Ma’aikatar Birnin Tarayya – Naira biliyan 28
  • Ma’aikatar Neja-Delta – Naira biliyan 24
  • Ma’aikatar Wutar Lantarki – Naira biliya 127
  • Ma’aikatar Masana’antu da Zuba Jari – Naira biliyan 40
  • Ma’aikatar Cikin Gida – Naira biliyan 35
  • Shirin tallafi na musamman ga ’yan kasa- Naira biliyan 30