Notice: Undefined index: show_thumbnails in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 199

Notice: Undefined index: show_headline in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 200
Abin da kasafin kudin Najeriya na badi ya kunsa - Aminiya
Aminiya

Abin da kasafin kudin Najeriya na badi ya kunsa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana gabatar da daftarin kasafin kudin badi

A ranar Talatar da ta gaba ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da  kasafin kudin badi na Naira triliyan 10.33 ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

Kasafin kudin wanda aka yi wa take da ‘Kasafin tabbatar da ci gaba da samar da aikin yi’ ya dara na bara da kashi 9.7 cikin dari.

An kuma yi kasafin na bana ne a kan hasashen farashin gangan danyen mai a kan Dala 57, inda kuma ake hasashen Najeriya za ta rika fitar da ganga miliyan daya da dubu 860 a kullum. Sannan aka kasafta canjin kudi a kan Naira 305 kan Dalar Amurka daya.

Wannan karon kasafin ya zo cikin sauri, sannan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya ba ministoci mako uku kacal su bayyana a gaban kwamitinsu na Majalisar Dattawa domin kare kasafinsu.

Ga yadda aka raba kudin ga wasu daga cikin ma’aikatu da hukumomi:

ADVERTISEMENT