Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Abin da ke haddasa hawa da saukar maniyyata aikin Hajji a Najeriya

Janye hannun gwamnati daga bayar da tallafin musayar Dala lamarin da ya jawo faduwar darajar Naira da tashe-tashen hankula a tsakanin makiyaya da manoma da kuncin talauci da kuma garkuwa da mutane suna daga cikin abubuwan da suke kawo kwan-gaba-kwan-baya wajen zuwa aikin Hajji daga Najeriya a ’yan shekarun nan.

Binciken Aminiya ya gano cewa a shekarar 2017, fiye da mahajjata dubu 70 ne suka sauke farali daga Najeriya inda aka samu raguwar mutum dubu 6 da 691 kan adadin da Saudiyya ta kebe wa kasar nan na mutum dubu 75, yayin da a bara mutum dubu 55, suka sauke farali daga Najeriya. A shekarar 2017 ne aikin Hajj ya fara haduwa da matsaloli da suka shafi jigilar maniyyatan, inda aka rika zazzafar muhawara kan karuwar kudin musaya wadda ta kusa durkusar da rajistar maniyyatan. Sai kuma tilasta biyan Riyal 2000 ga mahajjata da Saudiyya ta bullo da shi a shekara biyar zuwa shida da suka gabata ga duk wanda ya taba yin aikin Hajji a shekara hudu baya.

ADVERTISEMENT

Kididdiga ta nuna cewa fiye da kashi 70 cikin 100 na maniyyatan Najeriya sun taba yin aikin Hajji a shekara biyar baya. Wannan ya sa duk wanda zai maimaita Hajji daga Najeriya sai ya biya Naira miliyan 1 da dubu 700 maimakon Naira miliyan 1 da dubu 400 da sabon zuwa zai biya.

Sannan canjin Dala daya a kan Naira 360  ya taimaka wajen raguwar masu zuwa aikin Hajji daga Najeriya, musamman a wannan lokaci da ake fama da kuncin talauci da kuma rigingimu a tsakanin makiyaya da manoma da kuma tu’annatin masu garkuwa da mutane.

ADVERTISEMENT

Aminiya ta gano cewa ana samun hawa da saukar adadin masu zuwa aikin Hajji a sassan kasar nan, inda kididdiga ta nuna yawan maniyyatan na komawa komawa baya a wasu jihohi yayin da yake hawa da sauka a wasu tun daga shekarar 2016 zuwa bana.

Misali a Jihar Katsina mutum 4, 930 suka je Hajji a 2017 inda suka dawo 2, 750 a 2018 yayin da a bana suka koma 3, 116.  A shekarar 2017 maniyyata 6,713 suka ji Hajji daga Jihar Kaduna inda suka dawo 3,200 a 2018 sai kuma a 2019 suka kai 3, 500. Jihar Legas kuma mutum 2,316 ne suka je Hajji a 2017, a 2018 suka dawo 2,000 sannan a bana suka koma 2, 200.

A Jihar Gombe, maniyyata 2, 405 sukaje Hajji a 2017 suka dawo 1,200 a 2018 sai bana suka cira sama zuwa 1, 465. Sai Jihar Kebbi da mutum 4, 900 suka sauke farali a 2017, a 2018 suka dawo 3,000 sai kuma a 2019 ta suka sake yin kasa zuwa  2, 143. Ita kuwa Jihar Kano da a 2017 mutum 5, 500 suka je Hajji a 2018 sun dawo 2, 810 sai kuma bana suka cira sama zuwa 3, 170.

Jihar Bauchi mutum 3, 500 suka je Hajji a 2017, inda suka yiwo kasa zuwa 1, 602 a 2018, a bana kuma sun karu zuwa 1, 985. Sai Jihar Oyo mai mahajjata 1, 100 a 2017, a 2018, kuma suka yiwo kasa zuwa 911 sannan a bana tana suka koma 900. Jihar Ogun mai alhazai 1,000 a 2017, a 2018 sun koma 957 sai kuma bana suka sake kasa zuwa 724.

Jihar Osun mahajjata 962 suka sauke farali a 2017 sai kuma 2018 suka yi kasa zuwa 599, a bana kuma sun kara sama zuwa 670. Jihar Adamawa mutum 2,600 suka je Hajji a 2017, sai a 2018 1,661 sannan bana 1, 692. Mahajjata 2,004 ne suka halarci aikin Hajji daga Jihar Kwara a 2017, sai 2018, aka samu 1,500, a bana kuma 2,062.

Jihar Neja mutum 4,225 suka je Hajji a 2017 sai 2018, 3, 022 sannan a bana, 3,200. Jihar Sakkwato a 2017 mutum 4,859 suka je Hajji yayin da a 2018 suka koma 2, 837 sai bana suka sake yinkasa zuwa  1,500. Jihar Borno a 2018 mahajjata 1,650 suka sauke farali a bana kuma 1,637.

 

Matsalar ta shafi duniya

Masu zuwa aikin Hajji dai suna raguwa a duk fadin duniya cikin shekara 10 da suka gabata, kamar yadda wani rahoto na Saudi Gazette ya nuna a watan Satumban 2016. Jaridar ta ce a shekarar 2007, fiye da maniyyata miliyan 1 da dubu 700 daga kasashen waje da mahajjata dubu 746 da 511 ’yan kasar ne suka yi aikin Hajji, hakan na bnuna adadin mutum miliyan 2 da dubu 400 ke nan. Amma a shekarar 2012, fiye da mutum miliyan 3 ne suka yi aikin Hajjin, wanda shi ne mafi yawa a shekara 10.

A shekarar 2016, mutum miliyan 1 da dubu 325 da 372 da kasashen waje da ’yan kasar dubu 537 da 537 suka yi aikin Hajji, jimilla miliyan 1 da dubu 862 da 909, kuma wannan ne mafi karanci a shekara 10 da suka gabata.

Kididdigar ta nuna raguwar masu zuwa aikin Hajjin ta shafi kasashe 165 kuma ga dukkan alamu matsalar tana ci gaba a haka.

Misali kasar Indonesiya wadda ita ce ta fi yawan Musulmi a duniya kuma ta fi samun kujerun Hajji a shekara 10 da suka gabata, a 2016 ta tura mahajjata dubu 220 da 200, adadi mafi girma a shekara 10, sai dai ita ma ta hadu da faduwar darajar kudinta na Rupiah a shekarar 2011 zuwa 2015. A lokacin an rika canja Dala 1 da Rupiah dubu 19 da 395 da digo 75, wannan ya sa masu zuwa Hajji daga kasar suka ragu zuwa dubu 199 da 85 a shekarar 2011, suka dawo dubu 192 da 29 a  shekarar 2012. Sannan a shekarar 2013 suka sake yin kasa zuwa dubu 154 da 55, sai shekarar 2015 suka koma dubu 154 da 46.

 

Dalilin da ya sa maniyyata suka fi son tafiya Hajji ta kamfanoni

A duk lokacin da tafiya aikin Hajji ya kusanto Gwamnatin Tarayya da na jihohi na fito da sababbin tsare-tsare don kyautata rayuwar maniyyata, sai dai maniyyata da dama sun fi son yin tafiya wannan ibada ta Hajji ta hannun kamfanoni masu zaman kansu.

Binciken Aminiya ya gano cewa mafi yawan alhazan suna yin haka ne saboda ba su son dadewa a kasar Saudiyya, yayin da wadansu kuma ke yin haka don gudun wulakanci da rashin klua da bata lokaci.

Alhaji Abbas Tijjani ya shaida wa Aminiya cewa yawancin alhazan da ke tafiya Hajji ta hannun kamfanoni masu zaman kansu ’yan kasuwa ne, “Kin san yawanci ’yan kasuwa ne, don haka muka fi so mu yi kwanakin da ba su wuce mako uku a Saudiyya ba, kuma hakan ne tsarin kamfanoni masu zaman kansu. Amma gwamnati tana bayar da sama da kwana 40. Sai a ga mutum yana da harkokinsa amma ba ya da ikon ya taho gida sai ya yi wadancan kwanaki. Wani abu kuma shi ne yawan dadewar Alhaji a can shi ne adadin kashe kudin da zai yi. Domin kullum sai mutum ya ci abinci da kudinsa,” inji shi.

Ya ce wani dalili da maniyyata suka fi mu’amala da kamfanoni masu zaman kansu shi ne, yadda Alhaji ke da ’yancin rike fasfo da tikitinsa a hannunsa, duk lokacin da ya yi niyyar tafiya gida zai iya tafiyarsa ba tare da fuskantar wata matsala ba.

“Idan mutum ya so tafiya gida yana da damar ya yi tafiyarsa ba sai ya jira wadannan kwanakin da aka diba masa ba. Illa iyaka ya sayi sabon tikiti ya taho abinsa. Amma wanda ya je ta bangaren gwamnati ba ya da wannan dama,” inji shi.

Wani binciken Aminiya ya gano cewa yanzu haka kudin kujerar Hajji ta hannun kamfanoni masu zaman kansu ya fi na gwamnati araha da wasu abubuwa na kyautatawa.

Alhaji Hafizu Umar ya shaida wa Aminiya cewa, “A yanzu tafiya aikin Hajji ta kamfanoni masu zaman kansu ya fi araha a kan na gwamnati. Kuma ya fi samun kulawa da kyautatawa. Misali, masaukin da ake ajiye alhazai a Makka da Madina na kamfanoni masu zaman kansu sun fi kyau da tsabta, sannan suna kusa da masallatan Harami. Har ila yau ko a zaman Mina, shemar alhazan kamfanoni masu zaman kansu ta fi kyau da tsabta haka abincin da ake raba wa alhazai. Na tafi aikin ta bangarorin biyu, ba sau daya ba sau biyu ba.”

Game da sauye-sauyen da ake samu a harkar gudanar da aikin Hajji, Alhaji Sani Salisu Danbaba wanda ya kwashe sama da shekara 20 yana zuwa aikin Hajji, kuma yanzu haka yake can, ya shaida wa Aminiya cewa a bana Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta bullo da sabon shiri na kula da lafiyar mahajjata, inda ta hade abin a wuri daya maimakon yadda yake a shekarun baya. “A da za ki samu kowace jiha tana da cibiyar kula da lafiya da take ajiye ma’ikatan lafiya a masaukai biyu ko uku daga cikin masaukanta, inda za ta kula da lafiyar mahajjatan jiharta. Amma a bana sai Hukumar NAHCON ta hade abin wuri daya ta hade likitocin. Ma’ana, dukkan alhazan Najeriya wuri daya za su je don kula da lafiyarsu. Hakan ya kawo matsala sosai ga mahajjata, domin a yanzu haka ba ki ga dogon layin da marasa lafiya ke yi a wajen ba. Kwana biyu da suka wuce na raka wadansu makwabtana da ba su da lafiya wurin, tun safe ba su ga likita ba har yamma. Kin ga wannan sauyi ne amma ya zo da matsala ga mahajjata,” inji shi.

Wani da ya kwashe shekara sama da 30 yana zuwa Aikin Hajji kuma yanzu yake kasar Saudiyya, Alhaji Yahaya Ibrahim ya ce akwai sauyin da ya gani a aikin Hajjin bana game da harkar abincin da ake raba wa mahajjata.“A bana gaskiya mu alhazan Jihar Kano mun ga sauye-sauye ta bangaren abincin da ake raba wa mahajjata. A yanzu wai sai ki ga an dauko burodi da kunu an ba mu. Sai mutum ya rasa yadda zai yi ya ci saboda ni dai iya rayuwata ban taba ganin inda aka sha kunu da burodi a hade ba,” inji shi.

Ita kuwa Hajiya Umma Sani ta ce ta dauki shekaru ba ta je aikin Hajji ba sai a bara, don haka ta ga sauye-sauye a tsarin tafiyar da aikin da suka burge ta. “Na dade ban je aikin Hajji ba sai a bara, don haka da na je na ga sauye-sauye masu yawa. Misali, shi kansa a bangaren kasar an samar da sauye-sauye na sababbin gine-gine, inda aka rushe tsofaffin masaukai musamman a titin Shari Sittin. Haka a zaman alhazai na Mina a shekarun baya tabarmi ake shimfidawa a shemomin Najeriya amma yanzu abubuwa sun ci gaba ga kafet ga katifu har da barguna. Haka tsarin yadda ake fita Mina ya canja, a da kowa na fita a ranar 8 ga Zul-Hajji amma yanzu ana fara jigilar alhazai zuwa Mina tun daga ranar 7 ga wata.”

Wani da ya shafe shekaru yana zuwa aikin Hajji da Umara, Alhaji Hayatuddin Muhammad, ya danganta bin jirgin yawo maimakon na gwamnati mai sauki da maniyyata ke yi a kan wadata da gudun wulakanci.

Hayatuddin ya ce maniyyatan da suka saba tafiya Hajji sun gwammace su bi jirgin yawo don samun karin kulawa da gudun wulakanci a lokacin tafiya da dawowa.

Ya yi zargin cewa sau da dama akan samu akasi tun daga tafiya, inda ake barin maniyyata zube a sansanin alhazai da ke jihohi ko wurin saukar jirgi na tsawon lokaci, sabanin yadda aka tsara tafiyar. Y ace sannan idan aka je Kasa Mai tsarki sai a kai su masaukan da ke nesa da Harami. Ya ce duk da kudin guzuri Dala dubu 1 (kimanin Naira dubu 350) da Hukumar Hajji bai wa mahajjata tare da yi musu tanadin masauki da sauran hidimomi daga cikin Naira miliyan 1 da rabi da suka biya, maniyyata masu wadata sun gwammace su bi jirgin yawo da ke karbar adadin wannan kudi ba tare da ba su kudin guzuri ba, saboda yadda suke yi musu tanadin masauki mai kyau da ke kusa da Harami

Ya ce mahajjatan kamfanonin na da zabin su ci rin abincin da su ke so, baya ga gudanar da aikin hajjinsu cikin mako biyu kacal, sabanin na gwamnati da ake shafe kwana 40 a wani zubin kafin a dawo da mahajjaci.

A fuskar raguwar yawan mahajjatan Najeriya daga shekarun baya-bayan nan, tsohon mahajjacin ya ce matsalar tawayar tattalin arziki a  Najeriya ya sa adadin mahajjatan kasar ke ci gaba da raguwa, inda ta kai mahajjatan bana ba su wuce dubu 60 ba a bangaren hukuma kamfanoni. Ya ce idan a ka yi la’akari da karuwar jama’ar kasar nan a yanzu, adadin mahajjatanta na iya kaiwa dubu 200 ta misali da shekarun baya da al’ummarta ba su kai hakan ba, amma adadin ya fi na kowace kasa yawa, inda ya haura dubu 100.