Search
Subscribe
Abin da ke jawo lalacewa ko kangarewar yaro

Abin da ke jawo lalacewa ko kangarewar yaro

Akwai yara da dama ’yan firamare da ba sa cin abinci a gidansu kuma ba a ba su ko sisi haka za su tafi makaranta. Dan abincin da ake ba su a makaranta da shi suka dogara. Idan aka zo ba su abincin kai ka ce nama aka zo ba su, domin za ka ga suna ta murna da farin ciki. Idan wani na musun abin da na fada malaman makaranta na su ba za su musanta ni ba, domin su ganau ne ba jiyau ba.

Idan ka bar danka da yunwa duk wanda ya ba shi abinci ko kudi zai karba ko da kuwa wanda ya bashin cutarsa zai yi. Idan ka bar danka da yunwa idan ya ga kudinka zai iya dauka, in ya ga na wani ma zai iya dauka shi ke nan ya fara dauke-dauke.

Malami na tsakiyar aiki a aji ko malami yana ofis yaro zai shigo a galabaice ya ce cikinsa ko kansa na ciwo. Idan ka tambaye shi cewa ko ya ci abinci a gida kafin ya taho makaranta? Sai ya ce maka a’a. In da za ka ba shi abinci ya ci a wannan lokacin ka kuma tambayarsa yaya batun ciwon cikin ko kan? Cewa zai yi ya daina. Wallahi iyaye ku sani ’ya’ya amana ce Allah Ya ba ku. Kuma irin wannan mummunan kiwon ke sa wadansu ’ya’yan idan sun girma ma ba sa tausayin iyayensu.

Haka za ka ga yaro takalminsa ya tsinke an daure da leda ko zare, rigarsa ta yage an dinke ta kuma ta kuma yagewa an dinke ta. Wadansu yaran littafin rubutu ma bai wuce biyu ko uku suke da shi ba, wani yaron kuwa littafi daya za ka ga yana amfani da shi, duk malamin da ya yi rubutu a ciki zai yi masa. Irin wadannan ’ya’yan don sun kangare ba abin mamaki ba ne.

Gwamnatocin jihohi akwai bukatar a sakar wa masu dafa abinci mara, kuma a sa idanu sosai a harkar ciyarwa a firamare domin akwai macuta a hukumar ko a cikinsu. Yara ’yan firamare akwai bukatar a maida iliminsu kyauta a rika ba su littattafai, fensiri da kayan makaranta kyauta.

Nasiru Kainuwa Hadeja (08100229688)

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin