✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ke kawo matsala a Kannywood – Fatima Maina

Fatima Muhammad Maina da ke zaune a Kaduna, jarumar fina-finai ce kuma marubuciya wadda ta shahara wajen rubuta fina-finai da daukar nauyinsu a Masana’antar Kannywood.…

Fatima Muhammad Maina da ke zaune a Kaduna, jarumar fina-finai ce kuma marubuciya wadda ta shahara wajen rubuta fina-finai da daukar nauyinsu a Masana’antar Kannywood. Aminiya ta tattaunawa da ita, inda ta bayyana yadda ta shiga masana’antar da kuma abin da ke kawo wa masana’antar matsala:

Yaushe kika fara fitowa a cikin fina-finan Hausa kuma sun kai kamar nawa?

Gaskiya ba zan iya cewa ga yawan fina-finan da na yi ba a halin yanzu. Duk da cewa ban jima a cikin harkar ba, amma zan iya cewa na yi akalla shekara biyar ko sama da haka. Sannan akwai wasu daga cikin fina-finan da ni na rubuta kuma na fito a ciki kamar fim din Zafin Kishi wanda ni ce na rubuta shi kuma na fito a ciki a matsayin jaruma. Sai fim din Dan Baiwa shi ma ni ce na rubuta kuma na fito a matsayin jaruma sai kuma Safina wanda na fito a matsayin likita. Amma mafi yawan fina-finan da na fi fitowa a ciki su ne masu dogon zango wadanda ake kira da Ingilishi da Season Film.

Kin ce kina rubuta fina-finai, akalla fim nawa kika rubuta kawo yanzu?

Akalla na rubuta fim sun kai 10 wadanda suka hada da Zafin Kishi da Dan Baiwa da Hargitsin Rayuwa da Marar Tallafi da sauransu.

A tsawon lokacin da kike shiryawa da fitowa a fim, wane darakta kika fi jin dadin aiki da shi?

To ni dai ba zan ce ga wanda na fi jin dadin aiki da shi ba, domin duk wanda aiki ya hada ni da shi  ina jin dadin aikin a gaskiya.

Kawo yanzu wadanne nasarori kika samu a wannan harka?

Mun gode wa Allah domin na samu rufin asiri a ciki sosai, sai dai godiya kawai.

Wadanne kalubale kike fuskanta a wannan harka da kuma ita kanta Kannywood?

Babbar matsalar da ta addabe mu ita ce ta rashin hadin kai. Abin da muke bukata shi ne hadin kai a tsakanin ’yan Kannywood. Sai kuma hadin kai tsakanin ’yan Kudu da na Arewa wato Kannywood da Nollywood. Domin idan babu hadin kai babu inda za a samu nasarar da ake bukata. Don haka dole sai mun hada kai idan muna so mu samu ci gaba.

Ana cewa kasuwar fina-finai tana durkushewa yaya kike ganin al’amarin?

A gaskiya wanda ba ya ciki ba zai fahimci hakikanin abin da ke faruwa ba. Kamar ni yawancin fina-finaina masu dogon zango nake yi, ba kamar wanda aka fi shiryawa a Kannywood ba. Mu namu muna da hanyoyin da muke samun riba a ciki.

Shin kina da wani kira zuwa ga gwamnati a kan wannan harka taku?

Ina kiran Gwamnatin Tarayya ta yi koyi da kasar Indiya kan yadda take tallafa wa masu shirin fina-finai na can. Mu ma ya kamata gwamnati ta tallafa mana a cikin wannan harka. Amma wadansu sun dauki wannan sana’a tamu kamar sana’a ce da ba ta dace ba, musamman a nan Arewa inda ake mana kallon ’yan iska kuma ba haka abin yake ba.

Gwamnatin Tarayya ta yi wani shiri don tallafa wa masu shirya fina-finai shin kina ganin shirin zai yi tasiri?

Gaskiya abu daya muke bukata idan muna son wannan shiri ya yi tasiri; shi ne hadin kai a tsakaninmu. Idan muka hada kai shirin zai amfane mu idan kuma babu hadin kai, to, abin ba zai yi tasiri ba, kuma ba za mu ci gajiyarsa ba.

Sai kuma kirana ga gwamnati ta sassauta matakan da ta gindaya wajen bayar da wannan tallafi domin gaskiya sun yi tsauri da yawa. Muna bukatar a sassauta.

Kina ganin yawan fada da ake samu a gidaje da  a wani lokaci kan kai ga kisan kai da sauransu yana da alaka da kallon fina-finan Hausa?

A gaskiya ban yarda cewa kallon fina-finanmu yana jawo rikicin ma’aurata ba, sai dai mu ce laifin iyaye ne domin mafi yawa su ne suke yi wa ’ya’yansu auren dole. Amma idan har mace tana son mijinta babu yadda za a yi ta kashe shi. Don haka iyaye su dage da tarbiyyar ’ya’yansu.