✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ke kawo nasara ga dan kasuwa – Wayya 

Wani matashin dan kasuwa a Jihar Katsina kuma mai gidan kifi na Sauki Fish, Alhaji Babangida Wayya Shinkafi ya ce tsare ginshikan kasuwanci ne zai…

Wani matashin dan kasuwa a Jihar Katsina kuma mai gidan kifi na Sauki Fish, Alhaji Babangida Wayya Shinkafi ya ce tsare ginshikan kasuwanci ne zai kai mutum ga nasara a harkokinsa na kasuwanci.

Alhaji Babangida ya bayyana ginshikan kaswaunci da cewa sun hada da jari da tsare-tsaren kasuwar ita kanta ta hanyar yin komai bisa tsari har zuwa ga yadda za a karbi abokin hulda da sauransu. “Na uku, kudiri. Sai mai yin kasuwanci yana kudiri, wato ya kudirta a ransa cewa jarin Naira dubu 10 yana so ya zama dubu 20 ko 30 zuwa wani dan lokaci. Ka ga mai wannan kudiri ba zai tsaya ya ce sai lokaci kaza zai fito kasuwa ba, ko ya rika wasa in ya zo kasuwar,” inji shi.

Sai rukuni ko ginshiki na hudu a kasuwa shi ne tafiya da zamani. Ya ce idan zamani ya zo da abu to a bi shi. “Misali, yanzu akwai kasuwanci ta hanyar kafafen sadarwa da ake yi. Kana zaune za ka yi, hatta biyan kudin kayan. Kawai sai dai a ce ga kaya ko a zo daukar kaya. Sai hakuri shi ne cikon na biyar. Akwai yiwuwar kai ne ka fara kasuwancin a kan wani abu. Amma sai a wayi gari ku zama ku biyu ko fiye da haka. To kada ka ce zaka yi fushi ka bari, a’a, yi hakuri ka kuma yi tunanin juya akalar irin yadda kake tafiyar da naka zuwa irin yadda ka ga na kusa da kai na yi domin ci gaba,’ inji shi.

Ya ce yin fushi a kasuwa babu inda zai kai dan kasuwa sai koma baya. Ya ce  wadannan su ne ginshikan kasuwanci biyar wadanda muddin babu daya daga cikinsu za a samu tangarda.

Dan kasuwar ya ce, kauce wa wadancan dalilan ne ke sa matasanmu ba su son yin kasuwanci sai aikin gwamnati. “Shin aikin nawa ne, kuma masu bukatarsa nawa? Shi kuwa kasuwancin fa? Kullum karuwa yake. Mai kasuwa bai zuwa fadanci ko bangar siyasa da sauran wasu ayyuka na assha,” inji shi.

Matashin dan kasuwar ya yi kira ga jama’a musamman matasan Arewa su kama harkokin kasuwanci hannu bibbiyu domin tsira da mutuncinsu. Ya ce, dalilin da matasanmu ba su daukar harkar kasuwancin da muhimmanci shi ne, “In ba ka manta ba kusan shekara guda ke nan, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wata magana inda ya ce, akwai ragwanci a tare da wadansu matasanmu. Wannan magana tasa gaskiya ce.

Ragwanci na yin tasiri ga komai a wajen rayuwar wadansu matasanmu na yanzu. Duk abin da mutum zai yi in dai don Allah zai yi shi kuma don ya kare mutuncinsa, to lallai ne ya fuskanci wahala da farko, kuma a ji dadi daga baya. Idan mutum ya ce dadi kawai zai ji to ta yaya zai ji dadin? Kila dan talaka ne, in ma aka bibiya hatta karatun da aka yi sai da ’yan uwa suka tallafa walau da kudin kaza ko akuya. Bayan duk an gama karatun an samu kwalin, sai kuma a ce aiki ake son yi. Amma kuma kafin kai akwai mai shekara 10 da gamawa. Ka ga in babu abin yi sai a rikide a shiga wata harkar daban. Saboda haka, ya zama wajibi ga matasa su yi watsi da komai su rungumi kasuwanci,” inji shi.

Alhaji Wayya ya ci gaba da cewa, bisa ga kididdigar da aka yi a kan manyan masu kudi a duniya, sakamako ya nuna cewa, babu ma’aikacin gwamnati a ciki, dukkansu ’yan kasuwa ne.

Ya ce, “In har ka ga ma’aikacin gwamnati ya zama biloniya, sai ka yi tambayar wane irin aiki yake yi? Amma ko me za a ce dan kasuwa ya zama ta fuskar tara kudi ba a mamaki.”

Wayya ya ce ko a addini an nuna albarka tana nan a cikin kasuwanci da noma da kiwo da fatauci wadanda dukkansu hanyoyi ne na kasuwanci.

“Ba lallai ne sai kana da kudi za ka fara yin kasuwanci ba, gaskiya da rikon amanar mutum suna tsaya masa ya samu jarin kasuwa. In aka duba, kowane dan kasuwa ba shi kadai ya rika yin kasuwancin ba sai da ya hada da wani ko wadansu,tamkar yadda yaro yake tasowa tun daga koyon zama zuwa ga fara tafiya zuwa sauran rayuwa,” inji shi.