✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da muke bukata daga Buhari da gwamnoni

Masu iya magana suna cewa duk wadanda suke cikin ni’ima ko inuwa wadansu ne suka tsaya musu a rana. Kuma idan zafin ranar ya gallabe…

Masu iya magana suna cewa duk wadanda suke cikin ni’ima ko inuwa wadansu ne suka tsaya musu a rana. Kuma idan zafin ranar ya gallabe su suka kauce sai kowa ya ga wadancan mutane a rana. Hakika kamar yadda na fadi a wani rubutu da na yi a watan Afrilun bana an samu kura-kurai a zubin gwamnatin Buhari ta farko, kuma na dora alhakin hakan a kan muguwar barnar da gwamnatin ta iske a kasar nan da kuma yadda ba a tsoma wadanda suka san siyasa a cikinta ba, inda aka ba da fiffiko ga wadanda ake ganin kwararru ne wadanda galibi suka kasa aiwatar da ayyukan da aka dora musu.

Na ce rashin sanya ’yan siyasa na gidi a gwamnatin ya taimaka ’yan siyasar da suka hadu wajen kafa Jam’iyyar APC suka rika zame kafar gwamnatin Buhari, yayin da wadanda ya nada da yake ganin nasa ne saboda rashin sanin siyasar suka daburce suka kasa fidda gwamnatin daga matsalolin da ta samu kanta a ciki. Wannan ya sa gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza cimma kudirorinta kamar yadda jama’a suka sa rai, har ta kai yau akwai ’yan Najeriya da suke fata Jam’iyyar PDP ta dawo gadon mulki, duk da muguwar barnar da ta tafka a shekara 16 na mulkinta.

Halin da ake ciki ya sa mutane sun manta a zamanin PDP ne aka fi kassara tattalin arzikin kasar nan da sunan tsame hannun gwamnati daga harkokin kasuwanci inda a mahaifata Jihar Kano cikin shekara hudu na farkon mulkin Cif Obasanjo aka rufe masana’antu sama da 200. Kada a yi batun kamfanonin da gwamnatin PDP ta yi gwanjonsu a tsakanin ’ya’yanta wadanda akasarinsu sai da suka ci bashi a bankuna suka iya tsayawa takarar mukaman da suka kai su gadon mulki a wancan lokaci.

Kuma sayar da wadannan masana’antu da rufe su ne ya fara dora kasar nan a kan turbar rashin aikin yi da kara talautar da talakawa. Sai kuma gwamnatin ta PDP ta kwace iko da ’yancin kananan hukumomi ta mayar hannun gwamnonin jihohi wanda hakan ya dada jawo mugun talauci a yankunan karkara.

Wadannan abubuwa biyu ne ummul haba’isin talaucin da ya kara jefa masu raunin imani da rashin tausayi suka fara aikata wasu miyagun ayyuka kamar rikice-rikicen kabilanci da sace-sacen shanu da Boko Haram da satar mutane don tsafi da satar mutane ana neman kudin fansa da sauran miyagun ayyuka.

Na fadi abubuwa da dama a wancan rubutu inda na bayar da shawara ga gwamnatin Buhari cewa a wannan karo ya kamata gwamnatoci a matakai daban-daban su samar da wasu hanyoyi ko wata gidauniyar kula da talaka da marasa karfi domin ceto rayuwar mutanen da suke cikin tsananin bukata a daukacin kananan hukumomin kasar nan 774, musamman a wuraren da suka fi fama da annoba.

Na ce baya ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, manyan kamfanoni da masana’antun da ke Najeriya tun daga Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) da kamfanonin sadarwa da na gine-gine gidaje da hanyoyi da bankuna da sauran masana’antu a sanya kowanne ya rika bayar da akalla kashi biyu cikin 100 na dukiyar da ya mallaka ko kashi 5 cikin 100 na ribar da ya samu a shekara a zuba a asusun kula da marasa karfin.

Masu hakar mai da sufurinsa da daidaikun masu dukiya su kuma su rika bayar da akalla kashi daya cikin 40 na adadin abin da suka mallaka duk shekara ga wannan asusu. Gwamnati ta yi amfani da kudin wajen sayen kayen amfani gona da na masarufi ta raba a wadace kuma kyauta ga masu tsananin bukata na tsawon wata shida zuwa shekara daya. Kuma a shigo da magunguna masu inganci a wadace, a zuba su a asibitoci su ishi marasa lafiya marasa karfi na tsawon shekara a rika raba su kyauta, bayan shekara kuma a fara sayarwa a kan rabin kudinsu, har sai komai ya daidaita, kowa ya dawo cikin hayyacinsa.

Na bayar da wadancan shawarwari ne saboda gina dan Adam ya fi gina hanya, ya fi gina komai, domin komai din saboda dan Adam ake yin sa. Ubangiji da Ya halicci duniya da abin da ke cikinta Ya halitta ta ce don jin dadin dan Adam ba don ya kalle ta yana cikin kunci ba.

Don haka  wajibi ne wannan gwamnati ta yi wa komai garambawul ta yadda kowane mutum zai tsira da ransa da dukiyarsa da mutuncinsa da imaninsa, ta ceto al’umma daga kuncin da suke ciki. Koda za a kashe kashi 90 cikin 100 na duk dukiyar kasa ce wajen ceto al’umma daga kunci riba ce gare ta. A yi watsi da shawarwarin cibiyoyin Jari-Hujja da suke sa gwamnatoci suna jefa mutane cikin ukuba, wato irin su IMF da Bankin Duniya da suke cewa gwamnatocin kasashe masu tasowa su daina bayar da tallafi ga jama’a kan kiwon lafiya da ilimi da man fetur da sauran muhimman kayayyakin bukatun rayuwa. Domin ran dan Adam yana gaba da duk wani kayan jin dadi da za a tanada masa, kuma rashin ceto rayuwarsa muguwar asarar ce a duniya da Lahira. Saboda hakan na kara haifar da miyagu a cikin jama’a, ya sanya masu raunin zuciya ko imani su rasa imanin, marasa imani zuciyarsu ta dada kekashewa su yi ta aikata barna da fasadi, kowa ya rika cewa wayyo Allah!

Alhamdulillahi damina ta yi kyau a shekarun nan an samu abinci. To amma, kada a manta ba kowa ne manomi ba. Ko a manoman akwai marasa karfi, ga ’yan kasuwa da ma’aikata da marasa aiki da sauran raunana da suke cikin kuncin rayuwa suke tsananin bukatar a ceto su.

Lallai Shugaba Buhari da gwamnoni su dubi wannan batu domin talakan Najeriya ya sadaukar da rayuwa da jin dadinsa wajen zabarsu, ya sadaukar da kansa wajen ba su goyon baya duk da kunci da wahalar da ya shiga. Don haka lokaci ya yi da gwamnatocin za su saka masa.

Idan ta kama a gyara tsarin mulki ne don a yi wannan gyara, a yi haka, domin tsarin mulkin nan ba littafin Allah ba ne da za a ce ba za a ci gyaransa ba. A yi masa gyara a rage barnar kudi ga wadansu kalilan musamman wakilan majalisun dokoki, a rage albashi da alawus dinsu da kudaden da ake ba su da sunan ayyukan mazabu. Haka ministoci da sauran mukarraban gwamnati a tarayya da kwamishinoni a jihohi. A tsara duk wanda zai zama dan majalisa akalla ya wakilci mutum miliyan biyu, shi kuma albashi da alawus dinsa kada ya wuce mafi karancin albashi na Naira dubu 30 sau 30. Sannan a tabbatar duk wanda za a zaba ko za a nada ya zamo ba a tuhumarsa da sata ko dan kungiyar asiri ko fajirci.

Shugaba Buhari ya tuna duk aikin da zai yi, saboda mutane ne. Idan talaka yana cikin kunci ba zai ga amfanin kwaltar da aka yi a garinsu ko unguwarsu ba, idan yana fama da jinya ba zai damu da burtsatsen da aka yi a unguwarsu ba. Shugaba Buhari ya amince da karin albashi, to marasa aiki da masu karamin samu ta ina za a waiwaye su? Ba ma’aikata kadai ne mutane a Najeriya ba, ma’aikatan gwamnati ba su wuce kashi biyu da rabi na al’ummar kasar nan ba, sauran kashi 97 da rabi ko dai manoma ne ko ’yan kasuwa ko masu sana’o’in hannu ko masu aiki a kamfanonin ’yan kasuwa da kila karin zai sa su rasa aiki. To wane tanadi aka yi musu ko kuwa an bar su da dabararsu in ma mutuwa za su yi su mutu?

Shugaba Buhari da sauran shugabanni har zuwa kan kansila kuna da babban nauyi da amana a kanku ta kada ku fifita samun kudi daga ayyukan kwangila a kan inganta rayuwar mutanen da za a yi kwangilar dominsu. Sai jama’a suna da rai za su hau kwaltar da kuka gina ko su sha ruwan da kuka samar da sauransu, sai suna da lafiya za su ji dadin duk abin da za ku iya samarwa. Don haka a fifita kula da rayuwa da lafiyar jama’ar kasa!

Alhaji Abdulkarim Daiyabu

Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, kuma tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Harkokin Noma ta Jihar Kano (KACCIMA), za a iya samunsa ta: 08023106666, 08060116666