✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da muke fata bayan gano fetur a yankinmu – Mutanen Bauchi

Tun a 1996 Kamfanin Shell ya fara nemo man fetur a yankin Alkaleri da ke Jihar Bauchi a yankin da ke iyakar Jihar Bauchi da…

Tun a 1996 Kamfanin Shell ya fara nemo man fetur a yankin Alkaleri da ke Jihar Bauchi a yankin da ke iyakar Jihar Bauchi da Jihar Gombe, kuma tonon farko da aka yi kamfanin ya bada sanarwar an samu albarkatun iskar gas da yawa amma bai kai yadda za a yi kasuwancinsa ba.

Tun bayan da aka bayyana sakamakon binciken farko, masana suka ce a ganinsu ba a zurfafa binciken da aka yi ba don masu binciken kamar yadda rahotonsu ya nuna ba su tafi can kasa ba a tonon da suka yi.

Wannan dalilin ya sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a zurfafa binciken aikin da ya kaddamar cikin watan Afrilun bara da nufin fadada binciken.

Kamfanin Man Fetur na Kasa ya kebe wurare shida da aka kyautata zaton za a samu mai, ciki har da Rijiyar Kolmani wanda shi ne aka koma aikin tonowa don nemo mai a cikinta, inda tsawonta bai wuce kilomita 1.7 zuwa nisan kilomita biyu ba, a matsayin wani yunkuri da kamfanin man ya yi wajen tabbatar da cewa an aiwatar da umarnin da Shugaban Kasa ya bayar na kara samo wuraren da za a rika hako mai da iskar gas ba.

Kafin sake komawa neman man, sai da Kamfanin NNPC  da hadin gwiwar wani kamfanin kasar China suka gudanar da aikin fadada bincike don hako mai a yankin da ke cikin jihohin Bauchi da Gombe, inda kamfanin ya samu injin tono mai, mai inganci na zamani wanda zai yi tono mai zurfin kafa  dubu 14 da 500. Kamfanin NNPC ya yi wannan aiki na kwana 60 zuwa 70 kafin ya cimma zurfin da ake bukata, kamfanin ya dauki niyyar fadada tonon zuwa kafa dubu 14 da 500.

Wannan gagarumin aiki da aka yi na zurfafa neman man ya samu cikakkiyar nasara wadda har ta kai ga sanarwar da Kamfanin NNPC ya yi na samun albarkatun man fetur da gas a rijiyar Kolmani a kauyen Barambu a  Karamar Hukumar Alkaleri da ke Jihar Bauchi.

Al’ummar Najeriya sun cika da farin ciki dangane da samun albarkatun man fetur a Arewa a karo na farko, sai dai ga dukkan alamu samun man ya jawo batutuwa na siyasa a tsakanin jihohin Bauchi da Gombe, inda kowace ke ikirarin cewa  albarkatun man a yankinsa suke. Kwanan baya ne aka ruwaito tsohon Gwamnan Jihar Gombe Sanata Muhammad Danjuma Goje yana kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya baki domin inda aka samu man a  Jihar Gombe yake amma Kamfanin NNPC ya ce a Jihar Bauchi yake.

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad a nasa bangaren ya ce babu fada a tsakanin Jihar Bauchi da Jihar Gombe dangane da rijiyar man fetur da aka samu a kan iyakar jihohin biyu.

Ya ce jita-jitar da ake yadawa cewa akwai fada a tsakanin jihohin biyu kan rijiyar man da aka samu a tsakanin Bauchi da Gombe cikin Karamar Hukumar Alkaleri ba gaskiya ba ce.

Ya ce jihohin biyu danjuma ne da danjummai domin daga cikin Jihar Bauchi aka cire Jihar Gombe, “Mu dai a ganinmu komai namu daya ne, ba fada a tsakaninmu kan rijiyar mai domin mu ’yan uwan juna ne wadanda ke yada wannan jita-jita makiya ci gabanmu ne,” inji shi.

Mutanen yankin kuwa sun cika ne da farin ciki yayin da suka ce sun ga manyan injuna na wucewa zuwa yankin da aka samun man fetur din.

Tun bayan sanarwar Kamfanin NNPC, al’ummar Arewa ba su da wani buri illa su ga cewa an fara hakar man fetur din a yankin amma mazauna yankin wadanda suke cike da farin cikin samun arziki a garinsu suna da fata da bukatu da yawa a wajen gwamnati.

A zantawar da suka yi da manema labarai, sun ce suna fata irin abin da ke faruwa a yankin Neja Delta mai arzikin mai na matsalolin muhalli ba za su faru a yankinsu ba, kuma ba su fata masu hakar fetur su yi musu irin barnar da suke a can a yankinsu.

Malam Alhassan Abbas Musa mazaunin yankin mai shekara 55 ya ce sun yi farin ciki da samun mai.

Ya ce, “Ina fata albarkatun man fetur za su amfani Arewa da mutanen Najeriya baki daya.” Sannan ya gode wa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari saboda kokarin da ta yi ba tare da gajiyawa ba don ganin an samu man a yankin Arewa duk da cewa gwamnatocin da suka gabata sun gaza, wasu kuma sun yi watsi da aikin neman man fetur din.

Ya ce fatarsu ita ce idan an fara hakar man gwamnati ta bai wa yaransu ayyukan yi don da yawa daga ciknsu sun gama makaranta ba su da ayyukan yi, “Akwai masu digiri da yawa ba su da aiki, wadansu suna sai da rake, wadansu suna sayar da goro wadansu suna kanana sana’o’i,” inji shi.

Wani mazaunin yankin Alhaji Bakoji Gwaram mai shekara 87 ya ce ya yi auren fari ne lokacin da aka samu mulkin kai kuma tun da Najeriya ta samu ’yanci yake jin labarin cewa akwai man fetur a Alkaleri lokacin yana saurayi amma ba a yi komai a kai ba.

Alhaji Bakoji Gwaram ya ce abu kamar wasa domin haka aka yi ta fada kan wata hanya a yankin ba abin da aka yi don lokacin da aka yi hanyar kawai shi ne lokacin Firayi Minista Abubakar Tafawa Balewa da aka yi hanyar Bauchi zuwa Gombe.

Ya ce amma a wannan karo, “Gwamnati da gaske take yi wajen neman man fetur din, mun ji dadi kuma muna fata yin haka zai kawo ci gaba ga al’ummarmu. Tunda Allah Ya tuna da mu muna maSa godiya da wannan babbar ni’ima,” inji shi.

  Malam Umar Chiromawa, Sarkin Kixan Madobi a Jihar Kano, yayin nishadantar da masu Kirsimeti
Malam Umar Chiromawa, Sarkin Kixan Madobi a Jihar Kano, yayin nishadantar da masu Kirsimeti

Wani matashi mai shekara 36 mai suna Adamu Yalo ya ce suna madalla da wannan ni’ima ta samun man fetur, kuma suna godiya ga Allah

Shi ma Haruna Sarkin Shanu mai shekara 42 ya ce sun yi ta jin batutuwa da dama da ake cewa abububuwa ne da suke samun wadanda suke hakar mai, inda ya ce ya kamata gwamnati ta yi tanadi ga wadanda abin zai shafi gonakinsu a samar musu da mafita da tallafi yadda ba za su shiga wani hali ba, kuma gwamnati ta samar musu da tsaro kafin fara hakar man.

Sarkin Tashar Alkaleri, Bala Mohammed mai shekara 40 ya yi fatar hakar man za ta kawo bunkasar tattalin arziki, ya ce tsoronsu shi ne sun san da zarar an fara tono man  ba za su je gonakinsu ba don haka sai ya shawarci gwamnati ta yi abin sannu a hankali.

Wani dattijo mai shekara 64 Alhaji Dauda Magajin Rafin Doka a Gundumar Pali ya ce abin da suke so shi ne gwamnati ta gyara musu makarantun da suka lalace da asibitoci, a samar musu da kananan sana’o’i yayin da aka fara tonon man fetur din. “Kuma muna fata gwamnati za ta kai yaranmu karatu su karanci fannin man fetur don su dawo su yi aiki a wajen,” inji shi.

Alhaji Maina Alkaleri mai shekara 75 ya ce man da aka samu na ’yan Najeriya ne baki daya. “Muna fata man zai zama sanadiyyar bunkasar tattalin arzikin Najeriya kamar yadda ya zamo a kasar Saudiyya,” inji shi.

Kwamishinan Ciniki da Masana’antu na Jihar Bauchi, Alhaji Mohammed Alhassan Sadik ya ce Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya dauki matakan da suka dace na ganin cewa ire-iren matsalolin da suke faruwa a yankin Neja Delta ba su faru a Jihar Bauchi ba.