✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da muke fata sabuwar gwamnatin Borno ta yi wa ma’aikata – Bulama Abiso

Aminiya ta samu tattaunawa da sabon Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) reshen Jihar Borno, Kwamared Bulama Abiso dangane da yadda zai fuskanci kalubalen shugabancin…

Aminiya ta samu tattaunawa da sabon Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) reshen Jihar Borno, Kwamared Bulama Abiso dangane da yadda zai fuskanci kalubalen shugabancin kungiyar na tsawon shekara 4 tare da batun aiwatar da sabon tsarin albashi mafi karanci na Naira dubu 30, da kuma bashin ’yan fansho suke bin gwamnati na sama da Naira biliyan 20 da  sauran wasu bukatunsu da  suke so sabuwar gwamnati ta biya musu:

 

Mene ne takaitaccen tarihinka da gwagwarmayar da ka sha a kungiyarku ta kwadago?

Ni dan asalin Jihar Borno ne, kuma na fara aikin koyarwa a makarantun firamare fiye da shekara 20 da suka gabata, kuma na zama Shugaban Kungiyar Malamai (NUT) ta Jihar Borno har karo biyu, kafin in zama Shugaban Kungiyar Kwadago ta Jihar Borno a yanzu.

Me kake fatar gani a matsayinka na Shugaban Kungiyar Kwadago ta Jihar Borno?

Eh, to a gaskiya tsohon shugabanmu da na gaje shi Kwamared Titus Ali Abana ya yi iya kokarinsa ya ga cewa ya hada kawunan daukacin ma’aikatan jihar ta hanyar sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu, tare kuma da bi mana dukkan hakkokinmu a wajen gwamnati. To wannan ya sa muka rungumi ayyukanmu hannu bibiyu, to ni ma abin da zan yi ke nan wato in ci gaba da hada kawunan ma’aikatan jihar da nufin zama tsintsiya madaurinki daya, sannan zan yi iya kokarina wajen gwagwarmayar kwato mana hakkokinmu daga wajen gwamnati wannan shi ne burina.

Wadanne irin hakkokin ma’aikata ne suke wajen gwamnati da ba ta ba ku a baya ba?

Eh, to ka ga akwai karin albashi da akan yi na duk shekara-shekara wanda ake ce wa (Annual Increament) ba a yi ba na shekaru. Akwai kuma kudaden karin girma da su ma an dakatar tun lokacin da aka fara aikin tantance ma’aikata yau kusan shekara biyar ke nan, to muna so a biya cikin gaggawa. Sannan akwai ’yan fansho wadanda ba a biya su garatuti nasu ba, wanda ya taru ya kai wajen Naira biliyan 20, wanda muke ganin shi ma ya kamata a biya shi cikin gaggawa. Baya ga wadannan idan ka zo ta bangaren ma’aikatan kananan hukumomi da malaman makaranta akwai karancin albashi na Naira dubu 18 wanda aka yi kari shekara 8 zuwa 10 da suka wuce, wanda har yanzu wadansu ba su fara cin moriyar wannan kari ba. Kuma har yanzu ba za mu gushe ba za mu ci gaba da gwagwarmayar neman ganin an kawar da wadannan matsaloli da suka addabi ma’aikatan jihar, kafin shudewar wannan gwamnati. Idan kuma bai yiwu ba, to,  muna rokon sabuwar gwamnati da za ta shigo da ta yi wa Allah ta biya wadannan bukatunamu.’

Ka yi bayanin cewa akwai wasu kananan hukumomin da ba su samun albashin Naira dubu 18, kamar za su kai kananan hukumomi nawa ne?

Eh, to kananan hukumomi shida ba su fara samun albashin Naira dubu 18, su ne  Biu da Askira Uba da Hawul da Jere da kuma Birnin Maiduguri, (MMC). To kuma dalilan da gwamnati ta bayar cewa ga abin da ya sa ba a yi wannan kari ba tun wancan lokaci ta ce wai matsala ce ta matsin tattalin arziki da tashin darajar Dala da faduwar darajar man fetur a kasuwar duniya suka haifar da kuma matsalar rashin tsaro da jihar ta fuskanta na yaki da Boko Haram na kusan shekara 10. To amma idan aka lura yanzu an samu maslaha, wato an kama hanyar warwarewa, domin  tattalin arziki ya farfado, sannan darajar Naira ta daidaita, ya kamata a fara biyan ma’aikatan mafi karancin albashi na Naira dubu 18, kafin  a yi maganar sabon mafi karancin albashin na Naira dubu 30.

Ganin akwai ma’aikatan da ba su fara cin gajiyar mafi karancin albashi na Naira dubu 18 a shekara 8 ba, kana ganin za su iya samun sabon albashin Naira dubu 30?

Ya danganta ga sabuwar gwamnatin da za ta karbi ragamar mulkin jihar ce, sannan in za ka iya tunawa batun ya riga ya zama doka babu yadda za a yi a ce ba za a biya wannan sabon albashi ba, mu kyale. Ko wancan ma ai dole ne a biya kuma dole sai gwamnati ta biya kudaden da ba a biya su ba, don mun san cewar wannan dole za a biya don ya riga ya zama doka. Amma ba maganarsa muke yi a yanzu ba, maganar wancan muke yi. Sai an fara gabatar da wancan ga wadanda ba sa samu kuma a biya su basussukan kudaden da ba a ba su ba na albashinsu. To sai mu zo maganar wannan sabon tsari na Naira dubu 30 kuma ya kamata a ce kowa ya samu.

Ma’aikatan da yakin Boko Haram ya rutsa da su suka rasu za su kai nawa a kididdigarku?

 Eh, to gaskiya ce wannan yaki na Boko Haram ya shafi ma’aikata sosai amma ya fi shafar ma’aikatan kananan hukumomi da malaman makaranta musamman malaman firamare, duk da cewa ya shafi ma’akatan jiha. Kuma mu ’yan kwadago muna daga cikin wadanda muka tara kudade da kayayyakin masarufi muka mika wa gwamnati don bayar da tamu gudunmawar wajen taimaka wa al’umman jihar. Mun kiyasta ma’aikatan da suka rasa rayukansu za su kai kusan dubu biyu, daga ma’aikatan kananan hukumomi da malaman makaranta da ma’aikata na jiha da ma’aikatan jinya da ungozoma da sauransu. Muna rokon gwamnati mai shigowa ta yi wa Allah ta duba rayuwar iyalan wadannan mamata don tallafa wa rayuwarsu.

Gwamnati ta gina makarantu na zamani amma wadansu na kukan ba isassu kuma kwararrun malaman da za su koyar kasancewarka malamin makaranta me za ka ce kan haka?

Gaskiya abu ne kamar a ce mutum yana jin yunwa kuma gidansa ya rushe kuma wani ya zo ya ce zai gina masa gidan amma kuma yana fama da yunwarsa. Ka ga ba za ka ce masa a’a kada ya gina ba, don shi ma ginin abin so ne, to amma kuma ya kamata a ce an kawar maka da yunwarka kafin a gina maka gidan. To wannan shi ne halin da muka samu kanmu a wannan jiha. Kwarai da gaske gwamnati ta gina makarantu masu kyau da ban sha’awa ga kuma kayayyakin aiki, to amma har yanzu ba a da shirin inganta raywar malamai ta hanyar biya musu bukatunsu na yau da kullum, domin har yanzu muna fama da matsalolin da na  fada tun farko. Kuma idan ba a magance wadannan matsaloli namu ba, to babu wata koyarwar kirki da za a iya samu a wadancan makarantu da aka giggina. Za su iya zama kyal-kyal banza ne kawai, saboda a yanzu haka muna fama da karancin malamai kuma muna fama da kankantar albashi domin a yanzu akwai malaman da suke karbar albashin Naira dubu 10, wadansu kuma  dubu 11. To wadannan matsaloli idan ba a magance su ba to a gaskiya har yanzu dai ana nan a gidan jiya. Kuma wannan shugabanci da Allah Ya ba ni, zan yi amfani da shi wajen mika wa sabuwar gwamnati matsalolin don ta saurare mu kuma ta dube mu da idon rahama ta magance su.

A yanzu nawa ne adadin malaman makarantu a jihar nan?

Wato kafin hawan wannan gwamnatin ta Kashim Shettima muna da adadin malaman makaranta a kananan hukumomi  har dubu 25. Kuma a matakin jiha muna da kamar dubu biyar, ka ga idan aka hada muna da malamai sama da dubu 30 ke nan. Kuma a yanzu yadda nake magana da kai a matakin jiha an samu wadanda suka yi ritaya daga aiki da wadanda suka sauya wajen aiki da ire-irensu, yawan ya ragu daga dubu  biyar zuwa dubu biyu, ka ga muna neman kari ke nan. Kuma a matakan kananan hukumomi wadansu sun bar aiki wadansu sun yi ritaya wadansu kuma sun yi canjin aiki, su ma yawansu ya ragu daga dubu 25 zuwa wajen dubu 20, ke nan muna bukatar karin malamai kusan dubu 10. Wani abu kuma Kwararrun malaman da suka fi dadewa a aiki su ne wadanda aka dauke su a shekarun 1981 zuwa 1985 kuma dukka a wannan lokacin za su yi ritaya. Don haka muna rokon sabuwar gwamnatin da  za ta shigo ta dubi wannan lamarin don yi gyara.

Ko kana da kira ga ’ya’yan kungiyarka?

Wallahi babu abin da zan ce masu tunda suka zabe mu da gagarumin rijaye fa ce Allah Ya saka musu da alheri. Yanzu suna jiran mu aiwatar da abin da suka zabe mu a kai wato mu fara bin hakkokinsu ta yadda za su iya sadaukar da kai wajen aikinsu. Na kuma dauki wannan alkawarin tare da fatar Allah Ya ba mu ikon saukewa. Kuma ina kiransu kan su ba mu cikakken hadin kai da goyon baya, ta yadda za mu gudu tare mu tsira tare. Kuma ina horonsu da su toshe kunnuwansu daga gulmace-gulmace da jita-jita. Idan aka yi haka za mu samu cin nasara a duk inda muka sanya gaba. Ga sabuwar gwamnati mai shigowa ina rokonta ta yi wa Allah ta biya mana wadancan bukatu da muke nema, wato ta magance mana daukacin matsalolinmu, sai a ga ma’aikata sun fi mayar da hankali wajen gudanar da aiki, sannan ba za a ji tsakaninmu da gwamnati ba.