Daily Trust Aminiya - Abin da nake nufi da ‘Daga Allah sai Jonathan – Gwamnan Bauc
Subscribe

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed

Abin da nake nufi da ‘Daga Allah sai Jonathan – Gwamnan Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta yi karin haske tare da ba da hakuri kan kalaman da aka ruwaito Gwamnan Jihar, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir yana fadi lokacin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Jihar Bayelsa inda ya ce “Daga Allah sannan sai  Jonathan.”

Kwamishinan Watsa Labarai da Sadarwa, Dokta Ladan Salihu ya ce wani bangare na jawabin aka yanka aka tura don a kawo rudani a tsakanin al’umma, sannan ya ba da hakuri ga duk wanda ya ji cewa wannan jawabi ya saba masa.

“Maganar da ake ta yadawa, a kafofin sadarwa zamani game da bayani da Mai girma Gwamna ya yi a Abuja lokacin da aka kaddamar da Kwamitin Yakin Zaben Jihar Bayelsa, da za a yi wata mai zuwa wanda Gwamnan yake shugabanta. Ya yi magana a lokacin kuma maganar da ya yi sai muka ga ana kokari a ba ta mummunan fassara, wadansu ma har suna neman su muzanta Gwamnan. Kowa ya sani a kullum kafin Mai girma Gwamna ya yi jawabi sai ya yi godiya ga Allah, sannan ya yabi Annabi, kuma ku shaidu ne kan haka.

Ya ce, “Bayan ya sauke wannan nauyi sai Mai girma Gwamna ya yi jinjina bisa akida ta siyasa, akida ta rayuwa da mu’amala na goyon baya da biyayya bisa kyakykyawar mu’amala da yake da ita da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan. Kamar wanda ruwa ya ja ne a kogi sai wanda ya iya iyo ya tsamo shi ya fito da shi, ai magana ce ta Hausa. Da zarar mutumin ya farfado zai ce Allah mun gode maka, daga Allah kuma sai ya gode wa bawan da ya taimake shi. To mene ne laifi idan bawa ya yaba wa wanda ya taimake shi?”

texem
More Stories