✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da shugabannin duniya suka ce kan harin New Zealand

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka kashe kimanin Musulmi 50 a wani hari da aka kai wasu masallatai biyu a birnin Christchurch da…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka kashe kimanin Musulmi 50 a wani hari da aka kai wasu masallatai biyu a birnin Christchurch da ke kasar New Zealand.

Tuni duniya ta dauka, kasancewar New Zealand kasa ce da aka sani da zaman lafiya da girmama addinan juna.

Firayi Ministar kasar Jacinda Ardern ta samu yabo daga mutanen kasar da kasashen waje saboda yadda ta dauki lamarin. Ta ziyarci Musulmin da abin ya shafa, ta jajanta musu, kuma ta bayar da umarni Majalisar Dokokin kasar ta sauya dokokin amfani da bindiga a kasar.

Babban abin da ya jawo mata yabo shi ne yadda ta sanya hijabi a lokacin da ta zaiyarci Musulmin, kuma sai da aka karanta Alkur’ani a Majalisar Dokokin kasar domin nuna cewa ana tare.

Muna jajanta wa wadanda abin ya rutsa da su – Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya aika da wasikar jaje ga mutanen da abin da ya rutsa da su da kuma iyalan wadanda suka rasu a shafinsa na tiwita, duk da cewa bai ambaci Musulmi a bayanansa ba.

A cewarsa, “An kashe mutum 50 ba gaira ba dalili, sannan aka raunata wadansu. Amurka na tare da New Zealand a duk abin da za mu iya.”

Tun farko Sakataren Watsa Labarai na Fadar White House Sarah Sanders ta fitar da sanarwa, inda take cewa, “Amurka na Allah wadai da harin da aka kai a Cristchurch. Muna jajanta wa mutanen New Zealand da gwamnatin kasar musamman a wannan lokaci da suke ciki,” inji ta.

Wannan ba karamin rashin hankali ba ne – Majalisar Dinkin Duniya

A nata bayanin, Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin da ta bayyana a matsayin rashin hankali da dabbanci, inda ta nuna cewa irin wannan ta’addancin bai da mazauni.

“Mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na kara tabbatar da matsayarta cewa kowane irin ta’addanci yana kawo matsala ga tsaro da zaman lafiyar duniya baki daya.”

Muna tare da mutanen New Zealand – Jamus

Shugabar Jamus, Angelle Merkel ta bayyana rashin dadinta kan wannan harin da aka kai wa masallata, inda ta ce, “Kawai an kai wa mutane hari aka kashe su saboda kiyayya da nuna bambanci a cikin masallaci. Dole mu hada kai wajen yakar irin wannan ta’addancin domin wadanda aka kashe ba komai suke yi face Sallah cikin aminci da lumana.”

Shugaba Erdogan ya la’anci harin

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi Allah wadai da harin, sannan Mataimakin Shugaban Kasar Fuat Oktay tare da Ministan Harkokin Waje Meblut Cabusog sun ziyarci kasar, inda suka halarci jana’izar mamatan.

Shugaba Erdogan ya ce, yadda maharin ya sanar da cewa zai aikata hakan,  ya nuna cewa abu ne da ya aikata tare da shiri kuma ba shi kadai ba ne.

Erdogan ya ce “Idan aka fito tare da bayyana ’yan ta’addan da suke bayansa to hakan zai sanyaya zukatan jama’ar New Zealand.” Kamar yadda TRT ta ruwaito.

Wannan ba karamin abin takaici ba ne – Shugaban Nijar

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Issouhou Mahamadou lokacin da yake bayyana ra’ayinsa a kan harin na new zeland cewa ya yi, “Ina jajanta wa al’umar New Zeland da iyallan wadanda wannan al’amari ya rutsa da su,”  sannan ya ce, “Kisan gillar Chirstchurch wani abin takaici ne da ke kara tunatar da duniya cewa ta’addanci wani abu ne da ba ya da iyaka wanda kuma ya kamata a yake shi a kowane mataki.” Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na tiwita kuma Muryar Amurka ta ruwaito.

Shugaba Trump bai da wata alaka da maharin – Amurka

Fadar Gwamnatin Amurka ta White House, ta yi watsi da duk wani yunkurin da ake yi na alakanta Shugaba Donald Trump da maharin.

Mukaddashin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban, Mick Mulbaney  ya fada wa gidan talbijin na Fod News cewa “Shugaba Trump ba mai irin wannan akida ba ne ta ganin an fifita farar fata,” yana mai cewa “ban san sau nawa za mu yi ta nanata haka ba.”

Ya ce, kamata ya yi a dauki bala’in da ya faru a ranar Juma’a a New Zealand a matsayin yadda ya zo, wato a matsayin “mummunan aiki na shaidanci.”

Dan bindigar da ake zargi da kisan, Brenton Harris Tarrant mai shekara 28 wanda dan asalin kasar Austireliya ne, ya yi wani rubutu mai tsawo, wanda ya fitar jim kadan kafin ya kai harin, inda ya ce, yana kallon Shugaba Trump a matsayin wani “sabon jagoran fito da manufofin fararen fata,” amma ya ce ba ya goyon bayan tsare-tsarensa.