Da Dumi Dumi

Abin da ya kai mu wurin Gwamna El-Rufa’i –‘Yan Kannywood

A ranar Talatar da gabata ce wadansu ’yan fim daga  Masana’antar Kannywood, a karkashin Kungiyar Kannywood United Front suka kai ziyara ga Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i a Gidan Gwamnati na Sa Kashim a Kaduna.

Daga cikin ’yan wasan da suka halarci ganawar, akwai Darakta kuma Jarumi, Falalu Dorayi da Nuhu Abdullahi da Fati Shu’uma da tsohuwar jaruma Fati KK, da Ibrahim Maishunku da Jaruma kuma mai shirya fina-finan Hannatu Bashir da Mawaki Malam Ibrahim Yala da sauransu.

Wadannan jarumai sun kai ziyarar ce a karkashin jagoranin Shugaban Kungiyar Kannywood United Front, Dokta Ahmad Sarari.

Da yake zantawa da Aminiya kan dalilin zuwansu wajen Gwamnan, Darakta Falalu Dorayi ya ce sun je wajensa ne domin su taya shi murnar sake zabensa da aka yi, sannan su sake nanata masa bukatun da suke da su a masana’antarsu ta Kannywood ganin yadda yake kaunar fannin.

Falalu Dorayi ya ce, “Zuwanmu yana da alaka ne da yadda yake girmama Kannywood, kuma mu ma muna girmama shi. Shi ya sa bai yi kasa a gwiwa ba, ya karbe mu tare da karrama mu hannu bibbyu.

ADVERTISEMENT

Sannan mun taya shi murnar lashe zabensa da aka yi a karo na biyu domin da mu aka tallata wa jama’ar Kaduna shi, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu,”inji shi.

Falalu Dorayi ya kara da cewa sun yi amfani da ganawar da suka yi wajen isar da bukatar da suke da ita ta ya sanya baki a kan maganar bashin da za a ba su domin karfafa masana’antar, “Mun kuma shigar da batun kokarin da ake yi a kan yadda aka fitar da tsarin bashi domin inganta harkar film a Arewa da Najeriya baki daya, amma kuma sai aka sa tsauraran matakai da mu da ’yan fim na Kudu kowa ke korafi, domin kudin ba za su karbu ba. Shi ya sa a matsayinsa na jagora muka bukaci ya sa baki wajen ganin an sassauta matakan da aka sanya domin kowa ya ci gajiyar bashin. Kuma alhamdulillah ya amshi bukatarmu, ya ce za su duba lamarin bisa la’akari da irin gudunmawar da bangaren masana’antar nishadi ya bayar wajen kafa gwamnatocinsu,” inji shi.

Falalu Dorayi ya ce akwai muhimmin alkawari da Gwamnan ya yi musu wanda zai shafi duk wani da ke da alaka ko ruwa-da- tsaki a Kannywood ta fannin kasuwancin fina-finai, kuma wannan ma ya amince zai yi.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya