Da Dumi Dumi

Abin da ya kamata gwamnati ta yi maimakon hana almajiranci – A. K. Daiyabu

Alhaji Abdulkarim Xaiyabu
Alhaji Abdulkarim Xaiyabu

Aminiya ta kuma tattauna da Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya Alhaji Abdulkarim Daiyabu, inda ya ce fasalin koyarwa a makarantun gwamnati da na allon ya kamata a yi wa gyara ta yadda za su zamo masu koyar da daliban sana’o’in dogaro da kai ba wai a hana makarantun allon ba:

A matsayinka na dan gwagwarmayar tabbatar da adalci me za ka ce kan batun hana almajirai yawo da sunan neman ilimi?

A baya mun sha fada wa gwamnatoci tun daga 1985 da Janar Babangida ya zo gadon mulki cewa tsarin da suke dora kasar nan a kai zai haifar da bala’i da masifa ga kasar nan a gaba, amma sai aka dauka muna adawa ce kawai. Wannan talauci da ake kuka da shi da ake ganin shi ya kawo matsalar tsaro, ba talauci ne na Allah da Annabi ba, a’a talauci ne da ’yan Jari-Hujja, barayin gwamnati suka kirkiro mana shi suka tilasta shi a kanmu. Kuma aka zo aka rusa tarbiyya da da’a daga zukatan mutane aka nuna musu dukiya ita ce komai in ka same ta shi ke nan komai ya yi!

Don haka ba batu ne na almajiranci kadai ba, batu ne na zaluncin da masu mulki suke yi da babakere kan dukiyar kasa daga su sai su da kuma batun rugujewar tarbiyya, saboda haka zalunci ne a dora wa almajiranci matsalar tsaro a kasar nan. In aka duba akasarin masu aikata ta’addancin nan ko dai ba su taba halartar makarantun allo ba, ko bayan makarantun sun halarci na zamani ko kuma ba su halarci ko daya ba. In aka dubi kwamandojin Boko Haram da aka rika kamawa wadansu ko Fatiha ba su iya ba, daga nan za a fahimci cewa ba su ma yi makarantar allon da ake kira da almajiranci ba. Sannan wadanda suke jagorantar Boko Haram akasarinsu ’yan boko ne sun goge a boko har suna da kwarewar sarrafa na’urorin zamani da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da harhada bama-bamai. Sannan kada a manta kafin a samu ’yan ta’adda masu tayar da bama-bamai a Arewa, ai a Kudu aka fara samu, su ma almajiran ne? Don haka in dai gyara gwamnati take so to tun daga makarantun allo zuwa na boko, ta yi musu gyara ta yadda za su zamo masu samar da abin yi ga daliban da suke yayewa, ba kawai su samar da daliban da suka yi karatu babu aikin yi ba.

Ta yaya za a yi wannan gyara ga makarantun boko da na allo?

ADVERTISEMENT

Wato abin da ya kamata a yi shi ne dukkan makarantun boko da na Islamiyya da na allo ko na almajirai da ake kukan suna yawon barace-barace, Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi su fito da wani tsari na koyar da sana’o’in hannu da koyar da su amfani da kananan injuna masu saukin sarrafawa na maza da na mata gwargwadon yawan daliban kowace makaranta ta yadda almajiri ko dalibi yana koyon karatu yana kuma koyon sana’a, ya rika sana’anta abin da ya koya gwamnati ko masu hannu da shuni su rika saye. Yaro yana samun kudin shiga yana biyan bukatun rayuwarsa maimakon yawon bara, kuma yana karatunsa.

Misali kowane mahaifi a yanke masa abin da zai rika bayarwa kan kowane dansa da ke makaranta, wanda ba ya da iko, gwamnatin jiha ko ta karamar hukumar ko masu kudin unguwa su dauke masa. Kuma gwamnati ta samar da masu sayen kayayyakin da almajirai da daliban suka samar su rika sayarwa a Najeriya da makwabtanta a rika ba almajiran da daliban ribar da aka samu.

Wai ma idan aka hana makarantun ko yawon almajiranci gwamnati tana da makarantun da za ta iya daukar wadannan dimbin almajirai ne? Ko na bokon ba ta iya samar musu da gurbin karatu ba, to ina ga ta hana makarantun almajiranci? Ko kuwa za a hana makarantun ne almajiran su ci gaba da gararamba ba makarantar allon ba ta boko? Gaskiya aiki ne babba gwamnati ta kinkimo wanda za a dauki shekara da shekaru ba a warware shi ba, balle har an bayar da sanarwa a kai. Don haka  gwamnati ta tsaya ta tsara wasu hanyoyi da dabarun inganta irin wadannan makarantu da sauran makarantunta kafin ta fara bayar da wannan sanarwa.

Yanzu fa gwamnati ta yi watsi da nauyin da ke kanta ne na kare rayuwa da dukiya da lafiya da addini da nasaba na al’ummarta, ta koma ’yar Jari-Hujja wadda duk abin da za ta yi in ba za ta samu ribar ruwan kudi ba, ba za ta yi ba, wannan ya sa shugabannin da suka gabata suka yi gwanjon kadarorin kasar nan ga kawunansu kuma suka rufe su ko suka sayar wa baki ’yan kasashen waje, sannan suka daina bayar da tallafi ga kamfanonin ’yan kasuwa da suke samar da aikin yi kamar kamfanoni da masana’antun harhada motoci da na siminti da masaku da sauransu. Yau gwamnati ba ta da jirgin saman kasuwanci ba na ruwa, na kasa ma suna ne, ta yaya za a ce talauci ba zai yi mana katutu ba. ’Yan hukumomin da suke tallafa wa jama’a da suka hada da hukumomin sayen amfanin gona da na sayen gyada da auduga da hukumar kula da farashin kayayyaki da ta sayo kayayyakin bukatun jama’a duk an rusa su, in ka yi noma ya rage naka ko ka yi asara ko ka ci riba babu ruwan gwamnati. Idan kuma tsada za ta kashe mutane su je su yi ta mutuwa babu ruwan gwamnati. To a irin wannan hali babu tashin hankalin da kasa ba za ta shiga ba, shi ya sa muka yi ta yakar masu waccan muguwar akida da ke kashe kasa amma aka kasa ganewa ga shi abin da muke gudu ya tabbata.

Kana nufin gwamnati ta sake kakkafa masana’antu ke nan don samar da aikin yi?

Ko da ba za ta sake kakkafa masana’antu ba ya wajaba ta yi gyara kan wasu abubuwa, na farko ta tsara yadda za a samar da masana’antun da za su dace da bukatun kasar nan kanana da manya. Shugaba Buhari lokacin yana mulkin soja a 1984 ya kafa kwamitin yadda za a tsara tare da tafiyar da masana’antu a kasar nan a karkashin jagorancin Cif Chris Ogunbanjo, ni wakili ne a kwamitin mun zagaya kasar nan muka tsara yadda za a yi masana’antun amma sai aka yi masa juyin mulki, kuma wadanda suka biyo bayansa suka yi watsi da batun. Na biyu tunda an riga an sayar da kamfanin lantarki na kasa, gwamnatin Buhari ta sake kafa wani kamfanin su rika gasa da na ’yan kasuwa wajen rarraba wutar lantarki domin duk kasar da ba ta da wutar lantarki babu inda kamfanoninta za su je. Sannan ta sake kakkafa matatun man fetur, kai ya wajaba a tilasta jihohi a yankuna shida su kakkafa matatun man fetur suna tacewa suna samun riba maimakon yadda ake cutar Najeriya ana daukar danyen manmu ana kaiwa waje a biya kudin dako mai tsada kuma a dawo mana da zallar fetur a rasa sauran nau’o’in man da suka hada da black oil da kananzir da man jirgi da na yin kwalta da na yin sabulai da man shafawa da sauransu.

Sannan albashin manyan jami’an gwamnati da na masu rike da mukaman siyasa a rage shi ya zamo bai wuce ninki 31 na mafi karancin albashi a kasar nan ba. Wato wadannan jami’ai ya zamo misali suna karbar Naira dubu 30 a kullum wato daidai da wanda karamin ma’aikaci zai karba a wata.

Share