✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya kamata manoma su yi don samun kyakkyawar yabanya – Bappah Aliyu

Aminiya: Rahotanni sun ce a baya wannan kamfani ya shiga cikin mawuyacin hali, ko yaya batun yake? Hakika shekara uku kafin zuwan gwamnati mai ci…

Aminiya: Rahotanni sun ce a baya wannan kamfani ya shiga cikin mawuyacin hali, ko yaya batun yake?

Hakika shekara uku kafin zuwan gwamnati mai ci wannan kamfani ya shiga cikin wani  yanayi na ha’ula’i, duk da cewa kamfani ne da ke da dama, amma an bar damar ta kubuce, domin kamfanin zai iya sarrafa takin zamani, amma aka bari ya gagara sarrafawa, sannan injunansa suka lalace. Ma’aikatan kamfanin ba a biyan su albashi hakan ya kashe musu kuzari da karfi da kwarin gwiwar aikin da suke yi. 

Abin da ya faru shi ne akwai tsari na samar da taki karkashin gwamnatin APC a kasa baki daya wanda Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da nufin wadata kasa da abincin cikin gida. Lokacin da aka kaddamar sai aka zabi wasu kamfanonin taki guda 11 aka ce su ne za su samar da takin, amma  kamfanin taki na Jihar Bauchi ba ya cikinsu, daga jin wannan labari sai Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi ya garzaya saboda kyakkyawar alaka da dangantakar da ke tsakaninsa da Shugaban kasa da al’ummar Jihar Bauchi, da ya je ya same shi ya ce za a fara hidimar yin taki a gida, kuma jiharka ta Bauchi tana da irin wannan kamfani, wanda rashin irin wannan tallafawa ya sa kamfanin nan kusan a mace yake, Shugaban kasa ya ce ni ma Bauchi jihata ce ba ni da jihar da ta wuce Katsina da Bauchi a masoya, saboda haka a sa sunan Kamfanin Taki na Jihar Bauchi cikin wannan batu.

Bayan da Gwamna ya dawo, sai ya yi umarni ga Ma’aikatar Ciniki cewa ta shiga cikin wannan aiki, aka yi kwamitoci daban-daban don tabbatar da cewa kamfanin ya sake tsayawa da kafafunsa. Sai suka rubuta yawan kudin da ake bukata kuma ya amince, bayan nan an kusa farawa sai ya gayyace ni ya ce Sarkin Yamma zo, zan kalubalance ka wajen rike mini kamfanin taki. Saboda na san ka da rikon amana sannan kana da hanyoyin kasuwanci kamar yadda muka sadaukar da kai, kai ma ka jingine naka ka zo ka taimaka a samu ci gaban jihar nan. Na ce masa na gode, na jingine dukan abubuwan da nake yi na taho, na zo na duba kamfanin na duba na same shi kamar yadda na fadi tun farko, injunan tun daga na farko har zuwa na karshe kai hatta keken dinke buhu ba wanda yake da kyau, manyan motoci na daukar kaya ba wadda ke aiki.

Haka babbar matsalar da muka samu ita ce wajen da ake yin buhu, inda ake gwadawa da sikeli, wanda injin da yake wajen ba ya aiki, kullum in an tambaye ni nakan so in ba da wani abu na tarihin wurin, wuri ne da idan ka yi wasa takin ba zai samu  inganci ba, don ingancinsa kawai shi ne wanda zai iya ba ka sama da kilo 50 zai kuma iya ba ka kasa da kilo 50 ka ga ai kuma wannan surar tauye mudu ne.


Aminiya: To yaya kuka yi wajen warware matsalolin?

Da muka zo muka duba sai muka yi shawara muka kira Turawan da suka kafa kamfanin a kasar Demark muka ce muna da matsala, muka gabatar musu matsalolin suka ce za su iya magance su amma suna bukatar mu dauki dawainiyarsu kuma mu ba su babbar kujera a jirgi da matsakaiciyar kujera guda daya da kananan kujeru guda biyu, ka ga mutane hudu ne za su zo, suka ce mu samar masu babbar mota da kuma jami’an tsaro da masauki mai kyau. Da muka yi lissafi sai muka ga cewa za mu iya kashe Naira miliyan 14 kan zuwansu kawai, ban da kudin aiki da sauran dawainiya, da muka ji nasu sai muka sake nazari muka ce mu duba ko a cikin kasa za a samu wanda zai yi mana wannan aiki, sai aka ce akwai wani mai suna Malam Abubakar Sikeli a Kano yake, na buga masa waya muka yi magana ya zo mu gana ya ce ba zai iya zuwa ba, na ce dalili ya ce bai ji dadin karon da aka yi da shi a baya ba. Na roke shi na ba shi tabbacin yi masa adalci, bawan Allahn nan ya zo ya duba ya zauna ya yi aikin ya kirkire shi fiye ma da yadda Turawan suka yi shi. Wajen da iska ke shiga da idan waje daya ya toshe sai ya tsaya, ya kara girmansa ya inganta shi ya yi kuma wasu, abin farin ciki shi ne yadda ya koya wa injiniyoyinmu yadda za su rika yi, kuma tunda ya zo duk lokacin da zai yi aikin sai ya kira injiniyoyinmu su yi da su su gani. Haka muka yi aikin muka kammala komai a kan Naira miliyan uku kacal. 

Aminiya: Bara kun ba da takin zamani ga manoman Jihar Bauchi da wasu jihohin makwabta, baya ga tallafin da Gwamnatin Tarayya ta bayar. Ko kawo yanzu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu?

Daga farko ina godiya ga Gwamnan Jihar Bauchi domin yana daga cikin gwamnonin da suka ajiye zunzurutun kudi Naira biliyan 1 na sayen takin, don takin ba kyauta aka ba da shi ba, kudin ne ya dauka ya sayi takin hakan ya sa dukan kananan hukumomin Bauchi sun sani cewa kafin ruwan farko sun fara samun takin zamani, mun ba da tirelolin taki sama da 300 a Jihar Bauchi, wannan ya kawo sauyi sabanin yadda abin yake kafin zuwanmu. Domin za a ba da kwangilar sayo taki amma wanda aka ba kwangilar ba ma zai sayo takin cikin lokacin da ake bukata ba, wani lokaci sai gero ya fara tumu ake kawowa, ka ga ya makara, wannan shi ya sa tsadar takin yakan zama Naira dubu takwas zuwa dubu tara. To bayan mun yi wannan manomi ya samu sauki daga yadda ya sayi takin a bara waccan a kan Naira dubu 8 zuwa dubu 9 da 500. Ka ga a nan Gwamna ya samar da sauki ga kananan manoma, bara kuma mun sayar wa Jihar Gombe da taki tan dubu 6, mun kuma samar da takin ga daidaikun ’yan kasuwa kuma ’yan kasuwa daga jihohin Gombe, da Filato da Taraba da Kano da Kaduna, haka wajen Saminaka sun zo sun sayi taki a nan saboda ingancin da takin Jihar Bauchi ke da shi.

Aminiya: Wadanne irin ka’idoji kuke yi da ’yan kasuwa masu sayan taki a wajenku?

Mu ba ma sayar da taki buhu-buhu ba ma sayar da mota guda, abin da muke yi wa kananan ’yan kasuwa shi ne mu ba su dama su zo su yi rajista da mu ko da babban kamfanin takin gwamnati, sai su je su biya kudi a banki mota goma, ka ga Naira miliyan 30 ke nan. Idan kana son kadan sai ka shiga kasuwa ka saya saboda muna da dillalai wadanda muka yi wa rajista don kananan manoma.

Aminiya: Akwai batun da ake  yi cewa sinadaran da Gwamnatin Tarayya ta ba ku wanda kuke yin takin zamanin da shi dan kasar Moroko ne, wanda a duniya baki daya an aminta da ingancinsa, ko hakan shi ne sirrin ingancinsa?

Ba ma sinadarin ba ne, sirrin na jikin yadda kake hada sinadarin ya yi karko, abin da yake faruwa shi ne wannan kamfani za ka ga tudu na datti na daya daga cikin sinadari da a baya ba a kiyaye yadda ake tankade shi, yadda aka kawo shi haka ake sa shi, mu kuma muka ce hakan ba adalci ba ne don in ka sa shi sai ya narke tunda kura ce da yuriya in ka hada su sai su zama ruwa, muka ce a tankade saboda samun sinadarin da in ka sa shi a kasa zai narke domin wanda shi ne wanda kake bukata mai amfani.

Sai kuma wajen awo a kan tauye mudu don an ce ka sa yuriya kaza, kawolin kaza, kowane abu da adadin da ya kamata a sa shi in dai na hada takin ne to a wurin awon sai a rage, maimakon 270 sai a mai da shi 260, ka ga an rage goma, ingancin ya ragu kuma yawan wanda za ka yi ya karu to sauran yaya za ka yi da shi, ai ba daidai ba ne. Mu sai muka tsaya a kan mu yi ingantacce. Ka ga mun samu wadanda suke sayen takin Jihar Bauchi su je su sauya masa buhu, jami’an tsaro sun kama irin wadannan mutane da dama. Akwai kuma wadanda suke bude buhun su rage mudu daya ko biyu ko uku a ciki, su je su dinke buhun su yi algus, akwai kuma masu farke buhun takin namu su gauraya shi da banza-wofi.

Aminiya: Ko wane shiri kuka yi ga daminar bana?

Alhamdulillahi bara duk wanda ya nemi taki ya samu, kuma kafin mu shiga aikin daminar bana gadan-gadan muna da niyyar mu kira taron jama’a mu tambaye su mece ce matsalar da suka samu da takin Jihar Bauchi a bara, kuma ko akwai wani gyara da suke ganin ya kamata mu yi? Za mu zauna ne tsakaninmu da manoma da kuma dillalan taki, in akwai kuskure a fada mana mu gyara, in kuma babu, to wajibi ne mu tsaya mu kara inganta abin da muke da shi.

Wannan shi ne burinmu don a zo a fada mana gaskiya domin shi ne alheri gare mu da kuma manoma. Kuma a yanzu haka wannan shekara da muke ciki muna da shiri mai kyau don muna da taki a kasa. Lokacin da aka ba mu aikin da muka yi bara muka fara samar da yawan takin da aka ba mu daga cikin kamfanoni 11 din da aka ba aikin, kuma bayan mun kammala akwai kamfanonin da ba su iya gamawa ba, aka yago wani abu a cikin nasu aka ba mu, ina tabbatar maka aikin da muka yi daga watan Afrilun  zuwa watan Satumban bara cikin wata shida mun yi aikin da kamfanin nan ya yi a shekara tara. Kuma duk da cewa wasu sinadarai sun kare, yanzu haka mun shirya wa manoman shinkafa da na alkama taki har ma wadansu sun fara saye, mun shirya musu suna zuwa suna saye, kai har masu shirin rancen noman shinkafa na Ancho Borrowers wani daga ciki ya zo ya saya musu. Bisa kudurin da Gwamnatin Tarayya ke da shi na dogaro da kai ta hanyar samar da abinci a cikin kasa ya sa mun shirya tsaf domin fara aikin samar da taki a daminar bana, ban da wanda muke da shi a ajiye. Kuma Alhamdulillahi yanzu noma ya fara samar da kudin shiga ga Najeriya.