Search
Subscribe
Abin da ya kamata matasa su nema

Abin da ya kamata matasa su nema

Ku nemi a mayar da ku mutane, ta hanyar ba ku ilimi mai amfani a duniya da Lahira da kuma sana’a ta hannu. Kudi suna karewa, amma shi ilimi yana tare da ku har abada. Ita kuma sana’a za ta rufa muku asiri ba sai kun je nema wurin wani ba.

Kada ku taho da burinku ku kadai ku samu. Ku nemi yadda za a yi wa jama’arku aiki. Kuma duk inda za ku yi magana, ku yi da yawun jama’arku. Wannan shi ne hakika matakin adalci da nasara ga kowane dan Adam. Ubangiji Allah Ya sa mu dace.

Daga Kwamared Musa Tukur Anka

Shugaban Muryar Talaka, Anka Jihar Zamfara, 08031384371

Muna bukatar ofishin ’yan sanda

Salam jaridar Aminiya. Don Allah ku taimaka ku mika mana sakonmu ga Rundunar ’Yan sandan Najeriya da ta Jihar Kano da DPO na Karamar Hukumar Kabo su taimaka mana da ofishin ’yan sanda a mazabar Masanawa da ke Karamar Hukumar Kabo domin kawo zaman lafiya a yankin baki daya.

Daga Sulaiman Muhammad Masanawa Kabo, Kano 08140881207.

Gaisuwa ga Abba K.Yusuf

Assalam Edita. Ka mika min sakon gaisuwa zuwa ga Abba K. Yusuf, Allah Ya dawo wa Kanawa hakkinsu a kan abin da ya faru a zaben Kano amin.

Daga Mai A.C Kogo Kofar Kudu, 09030466517.

Jinjina ga Gwamna Badaru

Assalam Edita. Ka ba ni dama in mika sakon gaisuwa ga Gwamnan jihata Jigawa Alhaji Badaru Abubakar game da zaben kananan hukumomin jihar da aka yi.

Daga 07061869630.

Tunatarwa ga shugabannin Arewa

Assalam Edita. Don Allah ku mika sakon gaisuwa da yabo da jinjina ga mai girma tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa game da tunatar da shugabanninmu na Arewa kan maganar Masarautar Kano. Tabbas ya kamata a ce manyanmu masu mulki da sarakuna da ’yan siyasa da malaman addini da iyayenmu da duk masu fada-a-ji na Arewa su ja kunnen gwamnatin Jihar Kano a kan ta cire idonta game da duk abin da ya shafi masarautarmu ta Kano mai albarka. Domin mu ci gaba da samun zaman lafiya mai dorewa a Jihar Kano.

Daga Maikudi Ibrahim Zeze, Warure Kano, Mazaunin Ajegunle Legas, 09025253392.

Fatan alheri ga Gwamna Bala Mohammed

Assalam Edita. Ka ba ni dama in yi fatan alheri ga Sanata Bala Mohammed Gwamnan Jihar Bauchi bisa kyawawan manufofinsa ga jihar. Fatarmu Allah Ya dafa masa kuma Allah Ya ba shi mashawarta nagari.

Daga Nasiru Albani Bauchi. 08167155483.

Ina son buga wa Kano Pillars wasa

Ina kira ga Kwamishinan Wasanni na Jihar Kano da mahukuntan Kano Pillasr su yi min gwaji domin in fara wasa a Kulob din. Don na kware a kwallon kafa sosai in kuma an ki za mu shiga kotu. Za mu ga Najeriya ko akwai hukumar kare ’yancin dan Adam ko babu.

Daga Dan wasan Real Socieder, Abba FKD Gwarzo. 09076856233.

An shiga tsaka-mai-wuya

Assalamu alaikum ma’abota wannan jarida tamu mai albarka da fatar kuna lafiya. Gaskiya yankinmu na Arewa an shiga tsaka-mai-wuya komai yana neman dagwalgwalewa duk da Arewa ke da yawancin masu fada- a-ji. Ya kamata su yi amfani da wannan damar da Allah Ya ba su don ganin komai ya daidaita. Allah Ya taimaka, amin.

Daga Abubakar Yusuf Zuba, Abuja. 08032337145.

Muna fatan a daga darajar sarakuna

Salam daga mai kaunar jaridar Aminiya. Allah Ya kawo mana shugaban da zai daga martaban Sarakuna.

Daga Nata’ala Minna, Jihar Neja. 07060607979.

Shawara ga Shugaba Buhari

Ranka ya dade, rijiyoyin mai ka kwace lasisinsu ka bai wa kowace jiha ta kasar nan yadda rabo ya kama ta ji da kanta. Ta haka an rage wa Gwamnatin Tarayya hidimar ba da tallafi kowane wata. Idan aka samu wata goma, rarar da Gwammatin Tarayya ta samu, sai ta bai wa jihohi tallafi su karasa abubuwan da ba su yi ba zuwa karshen shekara.

Daga Aminu Ado, 250 Fagge Kano 08030636621.

Gaisuwa ga makaranta Aminiya

Salam Edita, ina son a mika min sakon gaisuwa ga duk makaranta jaridarmu mai albarka AMINIYA ina muku fatan alherin kuma ina yinku.

Daga Mai 08139039308.

Sakon ta’aziya ga jama’ar Batsari

Editan AMINIYA ina son in kara kira ga jama’a mu ci gaba da addu’a Allah Ya ba mu zaman lafiya a kasarmu amin. Sannan ina ta’aziya ga jama’ar Batsari da ke Karamar Hukumar Batsari wadanda ’yan bindiga suka farmawa har suka kashe wadansu jama’a da ke garin. Allah Ya gafarta musu amin.

Daga Saminu M. Batsari. 08036773485.

Matasa a kujerar shugabannin majalisun jihohi

Ina taya ’yan uwana matasa murnar samun nasarar zaman shugabannin majalisu a wasu jihohin Najeriya. Da fatan Allah Ya gwada mana mu kai ga samun matashi ya zama Shugaban Najeriya.

Daga Alhaji Bilya Doya Boy Zauro 07067467444, 09016144853.

Kira ga Gwamna Ganduje

A gaskiya bai dace Gwamna Ganduje ya rika takun-saka da Sarki Muhammadu Sunusi ba. Allah Ka ba mu zaman lafiya a kasarmu amin. Ina mika sakon gaisuwa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Daga Maryam A. Dorayi 09034883358.

Kira ga Ahmed Lawan

Assalam Edita, ina kira Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan don Allah a sa kishin kasarmu Najariya.

Daga Ishaka Maidawa Yelwa Shendam Jihar Filato 08064558922.

Wariyar lalura

Maganar gaskiya ya kamata mahukuntan Najeriya ku yi amfani da matakin da dan majalisar nan ya dauka na kawo sauyi ga wadanda ake nuna wa wariyar lalura a Najeriya. Saboda duk yadda ka ga bawa na tafiya da al’amuransa to haka Ubangijinsa Yake son ya gan shi.

Daga Abbakar Lawal Gidan Danmaye Jargaba 08097627776.

Ga Kanawan Dabo

Edita, ka ba ni fili in shaida wa Kanawa cewa, kada su manta Allah ke da zamani kuma shi Ya kawo zamanin da Gwamnatin Jihar kano ta karkasa Masarautar Kano zuwa masarautu 5 masu cin gashin kansu. Babu abin da ya rage yanzu sai a kara gode wa Allah, da addu’ar Allah Ya sa haka ya zama alheri.

Daga Amiru Isah Bakori, 07068147933.   

Kisan gilla a Gwamnatin APC

Zuwa ga APC don Allah ina tunatar wa gwamnati cewa, yaya ake kashe mutane babu tsaro kun yi shiru kun ce PDP ba ta iya ba, to APC kun gaza babu canji. An kashe jama’a a garin Batsari da yawa.

Daga Babangida W K Z. 08023509525.

Kira ga Shugaba Buhari

Ina kira ga Shugaba Buhari, ya samu ya cika alkawarin da ya yi wa iyalan Shehu Shagari na sanya sunansa a wani muhimmin wuri don tunawa da shi.

Daga Sufiyanu Mai Shago Dakwa Abuja 08161788025.

Buhari a kula da mu

Salam Edita. Kokarin da kuke Allah ne kadai zai biya ku, ina yi muku fatan alheri. A madadina da iyalaina muna murna kan rantsar da Baba karo na biyu. Kuma muna kira ya kula da mu talakawa, a samar da tsaro, da lantarki da aikin yi a kau da cin hanci. Allah Ya ba kasarmu zama lafiya.

Daga Ali Muhammad Mustapha Kanon Dabo. 09032518719.

Ganduje kamar Sarki Buhari ne!

Assalamu alaikum Edita. Don Allah ina so ka ba ni dama in jinjina wa Gwamnan Kanawa Dokta Abdullahi Umar Ganduje. A gaskiyar magana rabon da a yi wani jarumi a Arewacin Najeriya tun Sarkin Hadeja, Sarki Buhari, sai Gwamna Ganduje. Gwamna Ganduje yana burge ni kan yadda yake aiki tukuru, babu ruwansa da maganar ’yan adawa. Kanawa babu abin da za ku yi wa Allah sai godiya da ya ba ku jajirtaccen Gwamna.

Daga Daddy Bala Kakabori Hadeja 07065141489.

Ta’aziyya ga gidan  Rediyo Freedom

Edita, don Allah ku mika min sakon ta’aziyyata zuwa ga ’yan uwa da iyalai da  daukacin ma’aikatan gidan Rediyon Freedom na Dutse, bisa rasuwar hazikin ma’aikaci, wato Abdulkarim Bala Darmanawa. Babu shakka wannan babban rashi ne ga al’ummar Musulmi baki daya. Ina fatar Allah Ya gafarta masa, amin.

Daga Isah Sani Mai Arsenal Garkon Alli, Jihar Jigawa.08062332784.

Kira ga Shugaban Kasa da

Gwamnan Kano

Assalam. Don Allah Edita ina son a ba ni dama in yi kira ga Shugaban Kasa da Gwamnan Jihar Kano cewa ramuwar gayya ba shi ne ya kamata su maida hankali a kai ba.

Daga Barau Liman 08062862191.

Garin Waire na fama da  rashin  ruwa

Salam muna kira ga Mai girma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya duba mazabar Waire da ke Karama Hukumar Bichi ita ce mazabar da ba ta da hanya ba wutar lantarki kuma ba ruwan famfo a tausaya mana ya Mai girma Gwamna.

Daga Alhaji Musa Badawa Waire Bichi Kano 08068992280.

Batun tsaro!

Salam matsalar tsaro a Najeriya na kara ta’azzara lura da yadda kullum ake kara kashewa tare da yin garkuwa da mutane, abin sai dai muce Allah Ya sauwake.

 Daga Nasiru Albani Bauchi. 08167155483.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin