Search
Subscribe
Abin da ya sa aka samu karancin taki a Bauchi – Babban Sakatare

Dokta Musa Bala Lukshi

Abin da ya sa aka samu karancin taki a Bauchi – Babban Sakatare

Yayin da damina ta yi zurfi manoma da dama a Jihar Bauchi na kukan karancin takin zamani don sanya wa amfanin gonarsu. Wakilinmu ya tuntubi Babban Sakatare a Ma’aikatar Gona ta Jihar Bauchi Dokta Musa Bala Lukshi don jin abin da ya jawo karancin takin da yadda za a shawo kan lamarin:

Manoma na kukan karanci takin zamani a Jihar Bauchi a daminar bana, me ya kawo haka?

Kamfanin samar da kayayyakin aikin gona na Jihar Bauchi, wanda shi ne yake sayar da taki da raba wa manoma a jIhar, yau abin da Manajan Kamfanin ya shaida mini shi ne wajen da muke da taki kawai waje daya ne shi ne a Karamar Hukumar Itas Gadau amma sauran kananan hukumomi 20 da muke da su a nan jihar duk takin ya kare. Domin tun ranar Alhamis muka fuskanci cewa za mu rasa taki a kananan hukumominmu gaba daya, saboda haka na kira Manajan Kamfanin namu muka zauna da shi na kuma kira Manajan Kamfanin Taki na Bauchi. Manajan Kamfanin Taki na Bauchi, ya ce halin da suke ciki yanzu shi ne su kansu ba su da takin, saboda takin da suke yi yanzu ba nasu ba ne. Akwai hukuma da Shugaban Kasa, ya saka ta ita ke ba su kayan da suke hada wannan taki, kuma yadda ka’idar take in sun yi takin nan ba su da dama su sayar da shi sai wannan kwamiti na Shugaban Kasa ya ba su izini. Yanzu ba su da wadannan kayayyaki da ake yin taki da su, shi ya sa ba sa yin taki a wurin a yanzu, shi ya sa ba su da taki a kasa balle su sayar mana. Kuma muna da isassun kudin sayen takin amma babu takin, domin Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi ya ba mu kudin taki ya ce in muka sayar in ya kare ba sai mun koma wajensa ba, sai mu dauki kudin da yake hannunmu wanda muka sayar mu sake sayo wani takin da shi. Da a ce akwai a kamfanin taki na Bauchi da ba mu da wata matsala, to amma su ma babu kayan. Saboda haka ne ranar Juma’ar da ta gabata na je na samu Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi na shaida masa halin da muke ciki a jihar ba mu da taki, kuma ga shi yanzu lokaci ne da ake bukatar taki dole manomi ya nemi taki a wannan lokaci. To ya ce mu je mu yi kokari mu nemi taki ko a ina mu sayo mu kawo, shi ne muka tattauna da manajojin biyu don su samo yadda za a sayo takin. Kuma har yanzu muna tattaunawa da Kamfanin Taki na Jihar Bauchi su kuma suna tattaunawa dfa Kwamitin Shugaban Kasa da ke Abuja don samar musu da kayayyakin da za su yi takin zamanin. Idan suka samu wadannan kayayayyaki cikin kwana biyu za su iya wadata duk lungu da sakon Jihar Bauchi da takin. Kuma muna kokari tare da fatan za mu yi nasarar samun kayayyakin da za su yi takin, don hakan zai sawwaka mana wahalar zuwa wajen jihar don sayo takin. Halin da muke ciki ke nan a yanzu muna kira ga manoma su yi hakuri gwamnati tana bakin kokari kuma in Allah Ya so ba za a dauki lokaci ba za a warware wannan matsala.

Yaya kuke yi da masu yin magungunan feshi da sauran kayan noma na jabu?

Bara dai mun yi fama da masu yin magungunan feshi na jabu, ta kai ga sai da muka yi aiki da Hukumar Tabbatar da Ingacin Kayayyaki (Standard Organisation) da Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA), saboda masu kawo magungunan jabu wadanda suke cutar da manomanmu suke cutar da al’umma da kuma jihar baki daya. Sannan duk wanda muka samu yana amfani da magani na bogi, gwamnati ba za ta yi raga masa ba, za mu hada shi da hukuma a yi masa hukunci bisa doka tunda ba mu da wata sana’a sai noma, kuma in muka bar su za su lalata mana wannan sana’a tamu.

 Ko bana ma ma’aikata za su samu tallafin takin kamar yadda aka yi bara?

Eh, to a bara an samu tallafin taki ga ma’aikata da kungiyoyin manoma a jiha, wanda har yanzu muna kkkarin karbo kudaden takin da aka bayar musamman wanda aka ba ma’aikata wanda shi kai-tsasye ne za a cire daga albashinsu. A bana al’amari na iya sauyawa ko kuwa saboda ka san wannan gwsmnati sabuwa ce dole sai ta dudduba. Yanzu haka tana nazari a kai don ta ga shin za ta iya amfani da shi ko za ta iya inganta shi, saboda ga alama wannan gwamnati ta zo da himmar yadda za ta inganta noma a Jihar Bauchi. In ba ta yi na baya ba, za ta fito da abin da ya fi shi don a taimaka wa manoman jihar. Kullum ana kiranmu taro a kan lamarin, don haka mun san ana kokarin yin abin da ya fi kamata ne.

Ko akwai shawara ga manoma?

Shawara ita ce yanzu muna cikin watan Agusta zuwa watan gobe na Satumba yawancin kayayyakin amfanin gonanmu za su fara nuna, abin da yake damunmu shi ne saboda yawancin manoma yanzu ba su da hakuri kasuwa ta farko da ake samun amfannin gona za ka samu yawanci amfanin kudinsa yana da daraja a kasuwar, ganin haka yakans a wadansu manoma su je su samo wani abu da za su sa shi dole koda amfaninsu bai nuna ba, su sa masa wani magani don ya nuna da sauri su samu su kai kasuwa. Don haka muke kira ga manoma su yi hakuri su bar amfanin gonarsu ya bi matakan da ya saba ya gama nuna, don a same shi da kyau da daraja wanda in aka tafi da shi kasuwa ba za a samu wata matsala ba. Musamman ridi da waken suya mutanen sukan je su yi amfani da wasu magungunan feshi, su fesa musu in suka fesa gobe za su iya zuwa su girbe su, jibi su kai kasuwa. Wannan babban kuskure ne kuma cuta ce don wannan magani da suke sawa yana da illa a jikin abincin yana kuma da illa ga mutane, don haka su yi hakuri su bar abinci ko amfanin gona ya nuna. In ya nuna a wannan mataki za a iya barinsa ya zauna shekaru da dama amma in suka yi hanzarin nan abincin ba zai dade ba zai lalace, kuma in ya je gaba ya wuce nan Jihar Bauchi za su dawo mana da shi. Don wannan magani na kashe ciyawa ce busar da ciyawa yake yi saboda haka a yi hakuri a bar wannan amfani ya nuna sosai yadda Allah Ya tsara kafin a kai kasuwa.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin