Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Abin da ya sa aka shirya min tuggu cewa na saci kudi – Sule Lamido

Abin da ya sa aka shirya min tuggu cewa na saci kudi – Sule Lamido

Babu hannun APC a ciki

 

Aminiya ta tattauna da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, inda ya bayyana cewa a siyasance babu dan asali a cikin Jam’iyyar APC mai mulki a yanzu. Ya bayyana mambobinta da taron ’yan ci-ranin siyasa da suka taru a waje daya kamar yadda Fulani ke yawon neman ciyawa. Kuma ya yi bayani daban-daban da suka shafi mabambantan al’amura, ciki har da dalilin da ya sanya PDP ta fadi a zabe a 2015.

A zaben Gwamnan Imo, PDP ta lashe zabe aka karba aka ba APC, me za ka ce?

Asara ai asara ce, ballantana asarar siyasa. Ka kafa jam’iyya, ka yi kamfe, aka yi zabe, ka yi nasara, sannan a kwace.

Kwacewa aka yi?

Dalilina shi ne a wajen hukuncin da aka fada, lauyoyi sun bayyana mana, sun ce hukuncin irin na Buhari ne da Atiku. Lauyoyin sun mana bayanin hujjojin da aka kawo na Buhari aka ba shi zabe, su aka kawo, maimakon a bar mu, sai aka kwace mana. Amma dai akwai maganar shari’a, kuma ni ba masanin shari’a ba ne, amma in dai irin wannan hujjojin ne suka sa aka bar Buhari. Yanzu kusan kowa kansa ya buga kan yaya aka yi haka.

Gwamnatin da ke cin yanzu ta yi kamfe ne a kan PDP na cin hanci da rashawa, akwai yunwa a kasa, babu zaman lafiya. Shekara shida da fara mulkinsu, me za ka ce?

To ai wani lokacin gwamnatin yanzu, kamar mutum ne a ce barinka daya akwai shan inna, wannan lafiyayye ne. Sai lafiyayyen ya rika cewa wannan mara lafiya ne, ai jiki daya ne, ni a wurina koma me APC ta fada ko ma me ta yi, ita kadai ba za ta iya cin zabe ba; zaben farko da aka yi a 1999, kuri’unsu da na sauran jam’iyyu ba su kai na PDP ba. Haka ma zabe na biyu, da na ’Yar’aduwa da na Jonathan, saboda haka Jam’iyyar APC babu dan asali a siyasance, makiyaya ne kawai kamar Fulani masu neman ciyawa. Yawo suke yi daga wata jam’iyya zuwa wata. Ma’ana shi ne gambiza ce, ko daga PDP zuwa APC. Saboda haka babu asali a ciki, babu wani abu da zai nuna kai, kai ne, taro ne na ’yan bariki a bariki. Saboda masu yawon siyasa ne aka sa a waje daya a APC. A ciki akwai ’yan PDP, manya-manyan PDP irin tsofaffin ministoci da gwamnoni da suka sa aka kada PDP suna nan a APC. Ka ga ke nan a cikin APC akwai ’yan uwana a ciki da suka kafa ta. Ko ma me nake ciki yanzu, to ya zan yi, saboda nawa ne suke ja min.

A masatyinka na tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, sai kuma ga batun tuhuma a kotu na ka taba dukiyar jihar, daga ina wannan ya samo asali?

Ka san Jigawa yadda take, ka ga aikin da na yi. Na sa kamfanoni sun min aiki kyauta na kusan Naira miliyan dubu uku, wanda da na ga dama sai in sa ya gota, a biya ni in dauki kudin. In har zan sa wani ya taimaka min, a yi min aiki kyauta, sai kuma in debi kudin Jigawa? Na biyu wannan rigima ce ta yakin gida ya-mu-ya-mu a kan buri da biyan bukata da cewa bari in yi amfani da mukanina in karya wane. Lokacin da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo suka yi rigima da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonatahan, sai ya ce in yi takarar Shugaban Kasa, daga nan ne sai aka fara cewa ni barawo ne, aka fara kama dana da Dala dubu 50 a filin jirgin sama zai yi tafiya zuwa Masar. Yana da ’ya marar lafiya, ya je Masar kamar wata 9 baya na farko an ce ya koma bayan wata uku, an je na biyu da na uku, na hudun ne aka kama shi, dama an tsara za a kama shi. Sai aka kama shi din tare da matarsa da ’yarsa da sauran su biyar. Aka kai shi kotu saboda a mallake ni, ni na san me aka yi, na je wajen masu abin na yi musu magana, kuma na san me suka fada min, zan rubuta a littafina da nake rubutawa. Amma maganar ita ce an yi ne domin a sarrafa ni a ba ni tsoro in bar takara.

Amma duk da cewa ba na son APC ba na sha’awarta, wannan lamarin babu ruwan APC a ciki.

Amma ana ci gaba da yada fostarka a Intanet na takara, kamar ba ka karaya ba?

Ai dalilin shi ne mai son bata wani, ba zai hana Allah ikon daga bawanaSa ba, shi Allah Ya san zuciyata, kuma Ya san abin da na yi a Jigawa, kuma Ya san ban ci kudin kowa ba, kuma saboda a bata min ake rubutawa, aka ce an kai ni kotu. Kuma me ya rage yanzu? Karshen wulakanci da cin mutunci shi ne a kai ni kotu da ’ya’yana, ai wannan shi ne karshen wulakanci a kai ni kotu da ’ya’yana a ce barayi saboda a firgita ni.

Amma har yanzu kana da sha’awar tsayawa takarar Shugaban Kasa?

Maganar ita ce abin da Allah Ya yi a kan bawanaSa babu mai hanawa. Idan Allah Ya nufa zan mulki Najeriya, duk duniya idan za su hadu babu mai hanawa ko ina kurkuku ne. Obasanjo daga ina aka dauko shi? Ai idan aka ce mutum zai yi amfani da karfinsa ya yi kama-karya ya hana Allah ikonSa, sai ka bar shi da Allah kawai.

Wadansu suna tunanin kamar kin abin ka’idar jam’iyyarku ta PDP na kama-kama ya sa kuka fadi zaben 2015, yaya maganar take?

A lokacin dama akwai tsarin kama-kama din wanda aka biyo, ’Yar’aduwa ya yi shekara biyu, sai muka ce Arewa ta ci gaba. Amma shi tsarin kama-kama tsarin jam’iyya ne, amma da an ci zabe, shugaban ya zama shugaban kowa. To watakila kin bin tsarin na kama-kama ya taimaka wajen kayar da mu a lokacin.

Duk da cewa kai tsayayyen dan PDP ne, amma sai wadanda suka fita daga cikinta suka dawo daga baya suka buge ka a zaben fid-da-gwani da aka yi a zaben baya?

Ai suna da ’yancin zabe ne, su zabi wanda suke so. Ba na jin haushin kowa.

Sun sun ce wai saboda ba ka raba daloli ba ne?

Wannan tunaninsu ne, ba na tunanin za a iya sayen ’yan PDP. ’Yan PDP suna da kimar da ba za a iya sayensu ba, ba sa karbar kudi domin su zabi wani, saboda ’yan PDP ’yan gida daya ne. Amma kawai dai suna da ’yancin zabe.

A cikin shekara 20 da aka yi ana mulkin dimokuradiyya, kun yi shekara 16 me za ka ce?

Yanzu ni zan iya cewa ina cikin bangaren tsofaffi a siyasance domin ba na cikin ’yan zamani masu harkokin Intanet wato ’yan zamanin ICT. Idan za ka kididdige wani abu kamar siyasa ko wani abu, ya kamata ka fara duba yanayin tunanin ko iri daya ne. Misali, idan na fadi wani abu sai a ce manta da shi dan PDP ne, ko dan APC ne.

Amma idan ka duba manyan masu mulkin tun farkon, za ka lura da cewa shin suna da tsari guda daya da suka doge a kai? Suna dagewa a kan tsarin kasar. Idan sun yi fushi, suna kamewa daga fushinsu? Da sauransu, ba mu da wannan.

A wajena, da aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999, akwai farbaga tun bayan zaben 12 ga Yuni. Lokacin ana son a dawo da aminci ne a kasar domin a ci gaba tare wajen bunkasa kasar. Don haka lokacin babban burin shi ne dawo da martabar kasar, ba ma maganar tattalin arziki ba ko sauransu.

Shi ya sa aka hada PDP, inda aka tara mutanen da suka san Najeriya, irin su Adamu Ciroma da Abubakar Rimi da Aled Ekwueme da Bola Ige da sauransu, suka zauna kan nemo yadda za a dawo da martabar Najeriya. A haka ne har aka kai ga nemo Obasanjo daga kurkuku aka ce ya yi takara saboda ana ganin zai kasance na kowa saboda bai kasance mai nuna kabilanci ba.

Don haka an yi amfani da Obasanjo ne domin hada kan Najeriya. Kuma a cikin shekara uku aka gyara komai kuma aka fara kawo ci gaba.

Ganin yadda abubuwa suke tafiya yanzu, ko akwai bambanci tsakanin mulkinku da na APC domin ana ganin kamar ba ku yin adawa yadda ya dace?

Idan aka ce mu yi adawa yanzu, adawa ga wa za mu yi? Adawa ga APC ko ga PDP? Idan aka cire PDP a APC, babu yadda za a yi ta samu mulki. An samu manyan PDP da suka koma APC, don haka gwamnatin akwai ’yan PDP da yawa. Don haka idan ka ce adawa, da wa nake adawa? Da mutanena zan yi adawa?

Me ya sa ba ka koma ba kai ma a wancan lokaci?

Ina godiya da wannan shawarar da ka ba ni, duk da cewa ka makara. Don haka yazu babu adawa ai. Adawa kamata ya yi a ce akwai tsari a shirye, da idan kuka shigo mulki za su yi abin da wancan ba ta yi. Yawancin manyan APC yanzu, duk ’yan PDP ne idan ka cire Tinubu, yanzu kana so in yi adawa ne da mutanena? Kamar barin jiki daya ne, daya ya shanye daya na lafiya, ai duk jiki daya ne.

Kana ganin wannan ne ya sa komai ba ya tafiya ke nan?

Ban sani ba gaskiya.

Amma kana tunanin da gaske PDP ta gaza?

Ka fadi wani abu da APC din take yi da ba daga PDP ba ne, hanyoyin ne, titin jirgi ko tattalin arziki.

Amma dama ita gwamnati ai ci gaba ce?

Da kyau, don haka bai kamata a ce gwamnatin baya ba ta yi komai ba idan har ci gaba ne. Idan aka ce haka, ya nuna cewa ba komai, kamar yanzu ake farawa ke nan.

’Yan Najeriya suna jin haushin gwamanti tun daga farkon har yanzu?

Shi ya sa suke da damar canjawa wadansu bisa amincewarsu su sa wadanda suke so.

Me ke jawo jin haushin amma?

A matsayinmu na ’yan siyasa, mun yi iya kokarinmu, aka canja mu domin ba su gamsu ba. Tunda sun canja mu, ai sai su yi murna. Ai ya kamata a ce ne ’yan Najeriya suna cikin murna yanzu, domin sun samu gwamnatin da suke so.

Kana taimakon APC wajen adawa da jawo hankalinsu?

PDP ai mutane ne ba harfofin ba. Bayan an yi zabe, an kayar da mu, an ce ba mu iya ba, sai kuma in zo in taimaka? Amma da ka ce min ina samun matsala, ka zo ka ba da gudunmawa da sai in zo.

Ana ganin fostarka ta takara a Intanet, a wane bangaren ya kamata dan takara ya fito?

Shi tsarin kama-kama an kawo shi ne domin an samu matsaloli da yawa, sai muke neman yadda za mu kawo maslaha. An kawo tsarin ne domin a ceto Najeriya. Amma idan hakan bai samu ba, sai a nemo wanda ya fi cancanta kawai.